Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 99 of 227

Daddy ya nufi hanyar stairs kamar zai haura sai kuma ya fasa ya juyo ya nufi kofar fita, can kuma ya sake juyowa ya kalli Ameer dake kallonsa.

“Kar na sake jin maganar nan a bakinka, i will deal with her, domin wannan ba maganar da za kyale ba ce, akan me zaka ta kalli dana da hankalinta ta ce ďanta saboda kawai wani selfish interest nata, ba zan bar wannan ba”

“Okay”

Kawai Ameer ya fada sannan Daddy ya fice yana kokarin danne tashin hankalinsa. Sai da yayi nisa da fita sannan Ameer ya lura da counter sa data fadi kasa ya nufeta ya dauka ya bi bayan Daddy. Yana shiga part dinsa hullar kansa ce abar da ya fara cirea ya jefar a kasa, sannan ya daga wayarsa ya kira Hajiya Jamila da rabon da ya kirata tun da a lokacin da Ameer ya bata.

“Salamu alaikum”

Daddy be tsaya amsa mata sallama ba, bayan ta amsa kiran sai akwai ya kora mata da bayanin dalilin kiransa.

“Na ja masa kunne, amman na san ba ya jin magana zai iya kiranki ya tambaye wani abu akan wata mata ta ganshi tace shi danta ne, karki amsa masa?”

“Miya faru baka min bayanin komai ba, akwai ka fara da ba ni umarni? Sannan kuma ka saka hankalina tashi da jin wadannan kalaman naka”

Daker Daddy ya samu ya natsuwar fada mata abun da Ameer ya fada masa in brief.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Allah yasa ba Zahra ba ce, daman tana garin Abuja da zama?”

“Ba ni da wannan labarin, ko a lokacin Ameer ya samu matsala da abokinsa ban bibiya akan dole sai na san ko waye ko kuma dan waye ba, amman taya zata hadu da yaro a hanya ta fada masa wannan? Ameer ya girma a hannun tun yana karami har ya girma, karatunsa cinsa da shansa duk a hannuna yake, da dukiyata yake yadda yake so, shi yake kula min da wani bangare na kawancina, ina son Ameer shi yake maye min gurbin ďa namiji da Allah be bani ba, yadda nake son Ameer ko kaina bana so haka, taya zan yarda a raba ni da ďana, Ameer ďana ne that's”

“Mr Bashir kenan, ka ji kwatankwacin abun da na ji, a lokacin da ka raba ni da Ameer, kuma ka tsinke igiyar auren dake tsakaninmu”

Turo kofar dakin da Ameer yayi ya shigo yayi daidai ta lokacin da Daddy yake bawa Hajiya Jamila amsa.

“Ke aje wannan maganar a gafe, wacan da ne, wannan kuma yanzu ne babu wanda ya isa ya sauya yadda komai yake tafiya a yanzu, ba zan lamunta da wannan ba”

Daddy ya juyo yana ganin Ameer ne sai yayi saurin sauya maganar.

“Gidane na riga na siya an mallaka min, so zancen a maida kudi yanzu ba taso ba, sun san suna son gidan suka bari na siya? Akan me za su nemi daga ma kansu hankali har su daga min, su yi hakuri su bar ni na mutu a gida dan Allah...”

Ya yanke wayar Ameer kallonsa akwai yake domin be saba ganinsa a cikin irin wannan yanayin ba, yana waya yana fada.

“Ka bar carbinka a falon Mummy”

Ameer ya matso kusa da shi ya mika masa, Daddy ya karba tare da mika jikinsa ya rumgume ďanta.

“Allah ya maka albarka, ina matukar kaunarka Ameer, Allah ya kara shirya min kai”

“Ni ma ina kaunarka Daddy, Allah ya baka lafiya”

Ya sake shi yana sauke ajiyar zuciya, Ameer ya juya ya fice yana jin rashin natsuwa da halin da ya tararda mahaifinsa, da kuma wayar da yake.

“Dole na canja maka friends da guraren da kake zama,”

Ya fada bayan Ameer ya fice daga dakin yaja masa kofar. Hannu ya saka ya dafe kirjinsa tunawa kawai da yayi cewar Ameer ba dansa ba ne, sai ya ji duniyar da jindadin dake cikinta ya juye masa zuwa bakinciki da ciwon kirji a take.

“Kin zaki bukata miyasa kika ba ni? Rayuwata kawai matar nan take son ta ruguza kuma ta zubar min da mutunci, ba ta tunanin halin da Ameer zai shiga? Ta sani ta yi haka ko kuma kuskure ne? Ita din ce ma ko wata? Allah ka amshi rayuwata kamin ranar Da Ameer zai san ba ni na haife shi ba, ba zan bar hakan ma ta faru ba...”

Ya zauna gefen gadon yana jin kirjinsa na masa mugun ciwo.

WAIRA POV.

Sai da aka gama darasin sannan Malamin ya ciro katon lollipop ya mika mata, ba tare da tsayawa tunani komai ba ta karba, ta bude ta fara sha tana dariya kamar ba ita ce ta gama kuka ba. Tsareta yayi sai da ta shanye sannan yayi mata sallama ya tafi, ita kuma ya dauki jakar karatunta da dayan hannunta yayinda dayan hannun ke rike da zomon da daukarsa da yawo da shi ya zame mata kamar ibada. Sai da ta fara aje jakarta ta bude kofar falon sannan ta dauka ta shiga tunawa Ummi bata cikin gidan sai ya saka jin babu dadi a take yanayinta ya sauya. Saman ta hau ta shiga dakinta ta aje jakar a inda ta saba ajewa sannan ta sauko kasa ta aje zomonta akan kujera ta nufi hanyar Kitchen ta duba idan Hanne na ciki ta hada mata tea idan kuma bata nan sai ta hada da kanta. Tana leka Kitchen din ta hango Maleek tsaye rike da gorar ruwa sai ta tsaya jikin kofar. Da ido ya tambaye ta lafiya sai ta turo baki a shagwabe ta fara magana idonta har wani ruwa ruwan kwalla suke yana ce mata tak zata fara amayar masa da hawayenta

“Zan sha tea, ko cake ko a soya min arish ina jin yunwa”

Be ce mata komai ba, ya aje gorar ruwan ya nufi inda mug suke ya dauka ya hada mata tea iya yadda ya fahimci Ummi na hada mata, ya aje ba tare da yace mata ta zo ta dauka ba. Ita ma kuma kamar ta san ba zai ce ta zo ta dauka din ba sai ta nufi inda mug din yake ta saka hannu biyu ta dauka, ta fito Kitchen din ta dawo falo ta zauna tana son tea din zafi da tiririn da yake ba zai bari ba haka ta rumgume mug din tana kallon tea. Maleek ya fito daga kitchen din yana amsa wayar Abokinsa Abdull, yanayin yadda yake amsawar sai yayi mata kamar da Shuraim yake waya da sauri ta aje tea hannunta ta nufi inda yake tsaye rike da kujerar dinning ta tsaya tana kallonsa.

“Sulem? Sulem?”

Ya girgiza mata kaiwa, sai zuciyata ta raya mata me zata yi idan ba kuka ba, a sake ta fara aikin hawaye.

“Ba Suleem ba ne”

Ya fada bayan ya gama amsa wayar.

“Kirashi, ki kara shi”

“Ya za'ayi na kira shi? Ni ban da number shi, miye hadi da shi ma?”

“Akwai”

“Babu”

Ya juyo ta dawo hau kan kujera ta kwanta ya takure kanta. He just don't know why ya kasa dauke idonsa daga barin kallonta, and yana jin wani abu kamar ba dadi a takurawa kanta da kwantawa kan kujerar da ta yi, sai dai ba zai yi magana ba ko da kuwa zata shekara a haka. Bata dago ba sai da Jabir ya shigo shigo falon tana ganinsa ta tashi zaune da sauri kamar daman shigowarsa take jira.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.