Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 33 of 227
“Lafiya Abiey?”
Ummi ta tambaya tana baro dinning din ta nufo inda yake tsaye. Be amsa mata ba ya kalli Nimra ya ce.
“Nimra ina motarki?”
Kamar saukar aradu haka Nimra ta ji tambaya, wani irin dakan goma goma ta ji zuciyarta na yi, yawu ta hade da karfi numfashinta ya fara rawa.
“Ta... Tana gareji...?”
“Don't lie to me girl ina motarki take?”
Wani karin faduwar gaban ne ya sake samunta. Ummi ma kallonta take domin babu wanda yayi noticing motarta bata gidan sai yanzu.
“Daman motarki bata gida?”
Ummi ta tambaya sai ta kalleta ta daga mata kai.
“Eh tana gareji”
“Daman mun kun saba kai mota gareji da kanku a gidan nan ne? Karki min karya Nimra motarki tana police station din Katsina and they are on their way to arrest you for what you did”
Wani irin gumi ne ya karyo mata bata san lokacin da ta saki wayar hannunta ta fadi kasa ba.....
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
_©Khadeeja Candy_
1️⃣4️⃣
Ta juyo da sauri ta kalli Ummi hawaye na sauko mata da bibiyu.
“Ban aikata komai ba, ban yi komai ba Abiey ka yarda da ni”
Ta sake juyawa ga mahaifinta.
“Ina motarki take?”
Mahmood ya tambaya sai ta kasa furta komai, ta sani idan ta fada laifinta kara girma zai yi, kuma bata son iyayenta su sake kallon Ameer da wani laifin, bata kiyayyarsa ta girmama a zuciyarsu. Ummi ta kalli mijinta.
“Bari na yi magana da ita private”
A take Abiey ya daka mata tsawa.
“No a nan zata amsa mana, ba sai anje wani gurin ba domin police za su su tafi da ita, su ai dole ta fada musu gaskiya idan mu ta boye mana, dole ta fada mana abun da ya kai motarta Kt tare da wasu tarduna nata da suke motar da duk wasu bayananta, tun daga kt aka turowa CP na garin nan abun da ya faru, shi ya turo min komai kuma ya tabbatar min za su zo su tafi dake saboda an ga gawa a cikin motarki”
Ummi ta zaro ido tare da dukan kirji, sai a yanzu ta yarda lamarin babba ne. Gaba daya sai idon kowa ya dawo kanta, not just her body har muryarta da idonta rawa yake duk sanyin falon sai da gumi ya kwankwasa mata kofa, tashin hankali yace baki ga komai ba sai a yanzu, gaba daya sai ta manta da tsoron fadin wanda ta bawa motar, furucin mahaifinta cewa an ga gawa ya fi komai daga mata hankali.
“Ameer na bawa motar Abiey gawar wa aka gani?”
“Wane Ameer din?”
Sai a wannan karon Maleek ya saka bakinsa with confused.
“Ameer abokinka”
Ta amsa kai tsaye, a take Abiey ya sauke mata lafiyayyen mari sai da ta fadi kasa.
“Ta ina kika alakantu da shi? Miye hadinki da shi? Ina kika san shi har zaki dauki motarki ki bawa makiyin ďana? Kin kyauta gashi yanzu an yi miki sakamako kuma zaki girbi abun da kika shuka”
Ummi ta yi saurin shiga tsakiyarsu hawaye na cika idonta, kafafuwanta suka fara juyawa kamar ba za su dauke ta.
“Ga.. Ga.. Ga...ga... ”
So take ta tambaya gawar waye a motar amman ta kasa, saboda tsoro irin amsar da za a bata gashi maganar ma ta gagara fitowa. Mamaki ya hana Mahmood da Maleek cewa komai sai kallonta suke bama kamar Maleek. Abiey ya juya ya fice daga falon cikin wani irin fushi da bacin rai da ya dauki shekaru be ziyarce shi ba. Yana fita Ummi ta duka ta kama Nimra dake kuka.
“Ummi ban yi da wata manufa ba, ya fada min mahaifinshi ya koreshi kuma be san inda zai je ba, na bashi motata da kudi da ATM, amman ban san inda yaje ba, kuma ban aikata hakan da sanin cewar shi ne wanda suka yi fada da Ya Maleek ba, Allah ne shaidata ban sani ba Ummi”
Ummi ta rumgume ta tana kuka. Ummi ta amsa mata ta hayar daga mata kai alamar ta gamsu, sai dai zuciyarta ya samu rauni na rashin jin halin da Ameer yake ciki. Nimra ta dago ta kalli Maleek da ya kasa motsawa daga inda yake tsaye.
“Gawar waye a motar Ya Maleek? Kashe kansa yayi? Ko hadari yayi? Ina Ameer din yake?”
Sanin halin da Ameer yake shi yafi tsaya mata a rai sama da abun da aka zarginta da aikata, ji take idan aka samu gawar wani wanda ba shi ba abun zai zo mata da sauki, amman idan gawarsa shi ta wanne zata ji? Mutuwarsa ko zargin da ake mata?
“Gawar wata yarinya ce”
Maleek ya amsa mata, ita aka amsawa amman Ummi ce ta fi jin sanyi a ranta a take ta lumshe ido ta sauke ajiyar zuciya, kamin ta mike tsaye da sauri ta fice zuwa bangaren Abiey, ko da ta shiga ta same shi yana aikin saka sabon tufafi.
“Da gaske bari zaka yi police su tafi da ita? Abiey zaka iya kashe wutar nan daga nan gida ma ba sai an tafi da ita ba, Nimra macece be kamata a shigo har cikin gidan ubanta a kamata da laifin da bata aikata ba to miye amfanin dukiya da ikon Ubanta?”
Abiey ya juyo fuska a hade kamar garwashi ya kalli Ummi.
“To waya aikata? Miyasa kika goya mata baya ta aikata abun da ta aikata? Akan mi zaki shigar da yata a cikin lamarin rayuwar wani yaron can da bamu da alaka da shi? I warned you Zahra na fada miki ina son farinciki yayana fiye da nawa farinciki, sai dai na lura ke tashin hankali kike so, to ko hankali kowa zai tashi! Akan me zaki yarda ta bashi motarta da kudi saboda ya boya? A tunaninkin kin ni wayo?”
Na girgiza masa kai da sauri.
“Ba da sanina ta aikata ba?”
“Idan zaki hade min Qur'ane ba zan yarda dake ba, kin fi kowa kusanci da Nimra kin san duk wani abu da take in and out. Enough is enough and lemme tell you something har abada ba zan taba amsar Ameeer a matsayin ďanki ba, ba zan taba son ďan makiyina ba, ba kuma zan taba son ďan da kika kaunar ubansa har yanzu ba, idan kika aikata kuskure rayuwar Ameer zaki jefa a hadari domin zai rasa gata ta ko'ina daga nan zaki gane kuskuren neman kusancin da kike da shi...!”
Tsaye ta yi a gurin kamar an dasata, duk wasu kalamai da zasu jefata a damuwa Abiey ya furta mata su akan rashin sani, kasa motsi ta yi har ya gama canja kayan ya saka babbar rigarsa ya fice daga dakin. Sai a lokacin ta samu juyowa tana tafiya kamar bata iya daga kafar, daker ta dawo bangarenta tana tafiya kalaman mijinta na zagaye duniyar tunaninta. Ba su dauka da gaske Abiey zai bar police su shigo har cikin gidansa cikin falonsa su kama yarsa ba sai da aka taba kofar ta yi kara ta sanar musu akwai baki a waje. Kowa ya kasa bude kofar daga Mahmood har Maleek balle kuma Ummi da Nimra ta tashi ta koma kusa da ita ta rike ta tana kuka. Da ido Maleek yayi ma Mahmood alama da yaje ya bude kofar, cikin karfin hali Mahmood ya isa kofar ya bude gabansa sai faduwa yake domin abun ne da basu saba ba, shigowa gidan ma police ba su isa su yi ba sai dan izinin da mahaifinsu ya ba su. Gaba tarda kansa police din yayi a matsayin jami'in tsaro sannan ya nuna masa arrest warrant. Maleek ya nufi kofar ya tsaya yana kallon police din ya ce.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.