Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 204 of 227
Hawaye ya sauko mata tana son rayuwa cikin iyalinta amman ta san ba lallai be ciwon ya barta ba. Maleek ya saka yatsansa ya share mata hawaye
“Karki karaya Ummi kar ciwon nan ya saka ki kawo mutuwa a ranki, na ga masu irin ciwonki da yawa sun warke bayan samu kulawa mai kyau shiyasa nake son ki amince a fita dake gurin manyan likitocin da wannan ne bangarensu, wasu kuma ana saka ran su rasu da wuri sai gashi Allah ya tsawaita rayuwarsu, kawai abun da ake so shan magani da kuma bin ka'idodin da likita zai fada”
Ta kalleshi tana murmushi.
“Toh Maleek na amince idan haka zai faranta ranku, amman ni ma yanzu ku faranta min rai ku yi aure please kuma ku zauna lafiya da junanku”
“Zaman lafiya Ummi tun jiya na fada miki babu abun da zai sake faruwa, kuma ba aure ba har haihuwarmu sai kin gani da yardar Allah”
Ya sumbaci goshinta ya rumgume yana jin kamar ya fashe da kuka sai dai karfin zuciya na kasancewarsa namiji ba zai bar shi ya aikata haka ba. Ya dauki minti talatin a tare da ita sannan ya mike tsaye
“Bari na je na duba Nuwaira maybe ma ta dawo yau idan na ga jikin nata da sauki saboda mu samu saukin zirga zirga, sai mu ji da Ameer kawai”
“Abincinta yana kitchen na so ni zan tafi na wuce mata da shi, sai na ji ba zan iya ba, kuma ka wuce tare da Safiyya ka sauke ta gida”
“Okay”
Ya fice daga dakin, tunaninsa be bashi ko'ina ba sai dakin Namra dan haka ya nufi dakin ya kwankwasa sannan ya tura, sai ya same ta tsaye yana nade kaya Fiyya kuma na zaune kanta babu dankwali ita da Namra duk dariya suke da alama wani abun dariya suke magana.
“Good Morning”
Namra ta gaishe shi, Fiyya ma ta dora da nata ya amsa musu fuka a sake sannan ya ce.
“Namra ki kula da Ummi bata jindadi yau, zan tafi asibiti duba Nuwaira maybe na dawo tare da ita, sai mu wuce asibiti da Ummi”
“Okay, yanzu Fiyya ke fada min wai an har tsoronka suke?”
Ya kalli Fiyya sai ta noce kai be dauka tana da yawan magana haka ba, ita ma kuma bata dauka Namra zata masa magana ba.
“So dariyata ce kuke yi kenan?”
“No labarin wata friend dinta ce take ba ni”
“Taso muje Ummi tace na sauke ki gida”
Fiyya ta dauki hijabinta ta saka ta mike tsaye.
“Muna hira zaka dauke min ita”
“Okay ta zauna idan kun gama hiran sai ki kaita gida ai kina da mota”
Yana fadar hakan yayi baya ya fito ya janyo mata kofar dakin, yana sauko stairs ya hadu da Abiey cikin shirinsa da kuma hanzarinsa.
“Ka dawo? Umminka ta fada min cewar jiya zaka kwana asibiti tare da Ameer na jidadi haka”
Maleek yayi murmushi.
“Abiey an tashi lfy”
“Lafiya kalau, ya masu jikin Amarya da kuma Ameer”
Maleek sake yin murmushi.
“Abiey ba auren gaske ba ne fa, kuma ban je ba yanzu zan je na dubata”
“Toh baka fatan ya zama na gaske? Ni ai ban ki ace gobe ma a daura muku auren ba, ko dan Umminka”
“Abiey mu yi yaya da Ameer? Yana son Nuwaira sosai?”
Abiey ya tako kusa da shi ya dafashi.
“Kaddara ta riga fata, na tabbatar kana sonta fiye da yadda yake sonta, kuma na tabbatar kai kafi dacewa da ita, amman dai wannan wani abu ne da za a bata dama ta zaba idan ta zabe ka haka muke fata, kasan bahaushe yace so so ne amman son kai ya fi, ina son abun da ďana yake so, saboda ina son farincikinka Maleek”
“What if ta zabe Ameer?”
Abiey yayi dariya duk kuwa da kasancewar ba shi a cikin yanayin farinciki a yanzu saboda ciwon Ummi.
“Idan kuma ta zabe ka ba mu isa mu cilasta mata auren Ameer ba, dan kawai yana sonta”
“Yeah na yi wannan alkawarin ni ma ko da kuwa ba a Ameer ba, duk wanda take so shi za a aura mata, but for now ni na ja jiki already na yi magana da Ameer jiya na fada masa ba zan iya jayyaya da dan'uwana akan mace ba, duba abun da ya faru ya so kashe kansa saboda kawai ya ji cewar an daura aurena da ita, da ya mutu ya Ummi zata ji, kuma ni ma hakan ba zai min dadi ba, zan iya rasa Nuwaira ko kuma shi ya rasa ta amman ba zan sake samun dan'uwa ba”
“Ka yi tunani mai kyau Maleek shiyasa a kullum nake alfahari da kai, kuma bana shakkar nuna ka a ko'ina, ko yau na mutu na san ban bar mugun baya ba, zaka kula da kanenka kuma zaka yi abun da ya kamata, Allah ya zaba maka abun da ya fi zama alheri a rayuwarka Maleek”
“Ameen Abiey Thank you, about Ummi kuma na ga jikinta yayi tsanani yau fiye da ko yaushe and na yi magana da ita tace min ta yarda zata je asibitin a dubata”
“Already mun fara magana da Dr akan ciwonta saboda kai na ga abubuwa da yawa a gabanka kuma ga matsalolin da suka tunkaromu a yanzu, saurin da nake yanzu ma daukarta zan mu muje asibitin idan ka kare abun da kake sai ka same mu”
“Okay sai na zo”
Ya nufi kitchen ya dauki kwandon da aka aje da kayan abinci da kuma flask, Abiey kuma ya nufi upstairs. Tafiyar minti goma sha biyar ta ya iso Asibitin Skylines, duk yadda ya so ya fara isa dakin da Nuwaira take hakan be faru ba a dole sai da ya fara zuwa office dinsa ya duba wasu abubuwa sannan ya fito ya nufi inda take. A hankali ya tura kofar dakin ya shiga tana ganinsa ta sauko daga kan gadon da sauri ta nufo kofa kamar zata zo ta tarbe shi.
“Ina zaki je?”
“Bana son nan, na farka ni kadai a dakin kuma a waje ban san kowa ba”
Tana maganar idonta na cika da kwalla.
“Toh cinye ki za'ayi? Muka shiga garinku ma muka fito lafiya balle kuma nan? Muje ki zauna”
Kamar tace masa a a sai kuma ta ji ba zata iya musa like always dan haka ta koma ta zauna tana taba hannun nata gurin da aka saka mata drip. Zaunawa yayi a saman gadon yana kallonta
“Kina jin wani abu yanzu?”
Ta girgiza kai.
“Fever din ya sauka?”
Ta daga kai. Be sake ce mata komai ba ya mike tsaye ya bude abincin ya fara zuba mata, sai da ya gama hada mata tea sannan ya juyo ya kalleta.
“Kin wanke baki?”
Ta girgiza kai.
“Aa na dauka gida zamu tafi sai na wanke a can ina son na ga Ummi”
“Sai na tabbatar saukin jikinki tukuna, Ummi ma asibiti zata tafi”
“Waye ba lafiya? Ita”
“Eh kanta zata kai tare da Abiey daga nan ma can zan je, Ameer ma yana asibiti ya samu accident jiya amman da sauki sosai musamnan ma yau na ga sauki a tare da shi”
A take hankalinta ya tashi jin cewar mutumen da ta sani yayi hatsari, kuma Ummi ma tana asibiti.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.