Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 14 of 227

Wannan karon ma Hajiya Zahra ce take maganar cikin fushi tana jin kamar ace wanda ya aikatawa ďanta haka yana a gabanta.
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*

_Na Khadeeja Candy_

6️⃣

WAIRA POV.

Tun daga lokacin da sarki yayi mata gargadi sai ta rika ware kanta dabam, daman can bata da abokan wasa sai dai tana dan shiga cikin mutane a yanzu kuma ko fita gida bata yi sai dole, Eid din ma da take sakewa da shi sai ta daina, sai dai hakan be saka ya kyale ta hakan be canja komai daga alakarsu idan bata fita ba shi zai zo ya same ta har cikin gidan, wani lokacin zai mata hira ranar da aljanun kwarai suke kanta sai ta amsa masa su yi ta hira yana bata labaran duniyar da ta sha banban da tata, wani lokacin kuma har ya gama abun da zai yi ya tafi ba zata ce masa komai ba. Sai dai tana jidadin idan yana labarta yadda wasu abubuwan suke a wasu garuruwan kuma yana fahimtar hakan a fuskarta domin ya fi kowa sanin halinta, abun da zai faranta mata ko ya bakanta mata rai.

Karar jirgin saman da ya ji ya saka shi riko hannunta ya fito da ita daga cikin dakin da take ya nuna mata jirgin saman, ba a yau ta fara ganinsa ko jin kararsa ba, sai dai yau ne rana ya farko da ya taba labarta mata cewar mutane ne a ciki, kuma tsuntsun yana daukar mutane da yawa har da kayansu, kana ya misalta mata yadda girmansa yake a kasa, ta bude baki sosai tana fiddo idonta waje.

“Kuma mutum ne yake tukawa?”

Ta tambaya tana saka hannunta ta tare ranar dake haska fuskarta.

“Mutum ke tukawa, yana da sauri fiye da tsuntsu”

Ta dawo da dubanta gurin fuskarsa tana murmushi.

“A ina yake sauka?”

Shi ma ya sauko da kansa kasa yana kallonta domin yayi mata tsawo sosai.

“A can garuruwansu, sun tanadar masa muhalli mai girma sosai wandanda za su hau sai an tantance su suke hawa, kuma sai sun biya kudi”

Ta sake juyawa tana kallon inda jirgin ya bi amman ko alamarsa babu.

“Me suke bautawa su? Miyasa komai na su ya banbanta da mu?”

“Saboda sun yarda sun karbi sauyin da duniya ta zo da shi, wanda mu muka kasa haka, na nesa da mu suna da addininai kala kala na kusa kuma na san ana kiransu Musulmai”

Ya amsa mata yana kallonta irin kallon nan dake tafiya da ruhin mai yinsa.

“Ina ma ace an baki damar fita wajen gari, da na bawa idanuwanki abinci, na zaga dake duniya ki ga wata rayuwar data banbanta da taki sai dai an iyakance miki iya cikin garin nan, fitarki a garin nan zai saka ki manta hanya dawowa, hakan kuma na nufi rasa rayuwarki gaba daya”

Ta sauke kanta kasa ta fara tafiya.

“Miyasa rayuwarsu take burgeka?”

“Rayuwarsu tana da kyau, wani abu na su yana burgewa ke ma da zaki leka ki gwada zama a cikinsu da kin jidadin rayuwar”

Bata sake ce masa komai ba har suka isa gurin da dade bata zauna ba saboda gargadin da Sarki yayi mata, zaunawa ta yi a gurin shi kuma ya tsaya yana kallon itatuwan da suka kawata gurin ga ruwan dake gudana gwanin sha'awa.

“Wasu kan kawata cikin gidajensu da irin wannan ruwan”

Ta yamutsa fuska.

“Saboda su yi wanka?”

Ya amsa da kai yana murmushi, a take ta ji ta tsani mutanen domin mutane masu yawan wanka ko son tsabta basa burgeta.

“Bana son zama a cikinsu”

Zaunawa yayi a gurin yana kallon ruwan da take kallo.

“Akwai wanda na taba haduwa da shi, a rana zai yi wanka kamar sau biyar ko sau goma saboda tsabta”

“Kuma baya jin wahala?”

“Baya ji kuma baya gajiya”

Ya juyo ya kalleta sai ya kama hannunta ya rike.

“Waira baki taba jin marmarin wani abu da kika rasa ba?”

Da manyan idanuwanta ta kalleshi tana kokarin fahimta tambayarsa, sai ya saka yatsansa ya daki hancinta.

“Taya mutum zai yi marmarin wani abu da da be san da wanzuwarsa ba?”

Ya kallonta yake wannan karon kallon tausayi yake mata, ta tashi babu iyaye kuma tana rayuwa ita kadai kuma tace bata jin marmarin wani da ta rasa ba.

“Baki marmarin zama da iyaye?”

Ta kyalkyale da dariya irin dariyar nan ta yaran da ba su gama sanin ciwon kansu ba.

“Mi zai saka na yi marmarinsu? Bayan ban rayu da su ba? Abun da ka taba kasancewa da shi shi kake marmari ai”

“Zaman da kike ke kadai be taba sakawa kin ji marmarin iyaye da yan'uwa a kusa da ke ba?”

“Ina da yan'uwa ai”

“Su waye?”

Ta saka hannunta cikin gashin kanta ta ciro karamin beranta ta dora a hannu ta nuna masa.

“Gashi tare da zakaru, ina jindadin rayuwata ni”

Ya kawar da kansa.

“Wannan ba jindadin rayuwa ba ne, Waira kin tashi babu iyaye kin ware kanki dabam kina rayuwa tare da abubuwan da ake kebewa, a haka kuma jiran ake ki shekara ashirin a baki sarautar da idan kika haihu zaki mutu ki bar abun da kika haifa, to ina jindadin rayuwa a nan?”

Hannu ta saka ta raba gashin kanta biyu ta saka beran a tsakiya sannan ta mike tsaye ta doshin gurin iccen abaya, Eid na kallonta har ta haye sama tana tsinko ayabar tana jefowa kasa sai da ta gama sannan ta kwanta a saman itacen tana cin wata. Eid na ganin haka ya tashi ya karasa gurin ya daga kansa sama yana kallonta.

“Zo mu tafi gida”

Ta girgiza masa kai alamar aa, yana jin haka ya san ba yanzu zata tafi gidan ba, sai ya juya yayi tafiyarsa, tashi ta yi zaune sai da ta daina hangoshi sannan ta share hawayen da suka cika mata ido. A yau kam Eid ya saka ta marmarin da tunanin abun da bata taba ba, su waye iyayenta wace kalar kulawa za su bata duk bata sani ba, ta ware kanta daga yan'uwanta saboda ta fi jindadin rayuwarta a inda take rayuwa a yanzu. Saukowa ta yi daga kan itacen ta nufi gabar da ruwa ke gudana ta rika bi tana kallon ruwan har ta isa inda mahadarsu take, sai ta taka wani tsauni ta tsaya akai tana hango wani gari da ba ta taba sanin akwai a gurin ba, domin yawonta be tana kawo ta a nan ba, hangaga ta hangame baki tana dariya domin yanayin iskar gurin ma a dabam take.

‘Wannan ba jindadin rayuwa ba ne, Waira kin tashi babu iyaye kin ware kanki dabam kina rayuwa tare da abubuwan da ake kebewa, a haka kuma jiran ake ki shekara ashirin a baki sarautar da idan kika haihu zaki mutu ki bar abun da kika haifa, to ina jindadin rayuwa a nan?’

Maganar Eid ta dawo mata, a ciki babu abun da ya fi tsorata kamar cewar zata haihu ta mutu, kamar yadda mahaifiyarta ta mutu bayan haihuwarta, a duniya babu abun da take tsoro kamar mutuwa, ta zauna a gurin ta sako kafafuwanta kasa tana kallon yadda dacin ya wadatu da ni'imar Allah da albarkarsa.

AMEER POV.

Ya dago yana yi ma sakatarensa wani mugun kallo irin na kaskantaccin mutane.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.