Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 29 of 227

“Ke aljanna ce?”

Bata san me ya fada ba, hasalima bata taba jin yaren ba bakon yare ne a gurinta, kamar yadda fuskarsa take bakuwa a gurinta, baya baya ta yi ta lafe a jikin dutsen tana kallonsa. He thought bata jin hausa domin yanayinta ya nuna haka.

“Who are you?”

A karo na farko ta ji yaruka kala biyu da ba irin nata ba, kamar yadda tufafinsa ma suka banbanta da nata, yanzu kam ta tabbatar ba Eid ba ne, sai dai kuma bata da tabbacin ba turoshi aka yi a gurinta ba, idan kuma turo shi aka yi to me yake jira da ita be kamata ba?

“Some time I'm such a fool wanda be ji Hausa ba ta ina zai ji turanci?”

Ya fada yana jin zuciyarsa na tashi da alama wani aman yana kusa domin yawun bakinsa sai tsinkewa suke suna cika masa baki. Dauke ido yayi daga barin kallonta ya dauki Box din sarewarsa ya saka sarewar ya fara tafiya yana yamutsa fuska ya kasa daina ganin beran nan na dazu da dattin dake jikinta.

“Daman hakan aljanu suke da kazanta?”

Ya tambayi kanshi kamin ya duka ya fara kwara amai kamar marar lafiya, sai da ya gama ya nufi motar Nimra ya bude ya dauko ruwa ya wanke bakinsa da fuskarsa sannan zauna a bayan motar yana sauke ajiyar zuciya.

*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*

_©Khadeeja Candy_

Na yi mistake din page, na saka 12 Instead of 11 so wannan shi ne na 12 wacan kuma 11.

1️⃣2️⃣

Can kuma ya dago kanshi ya fito daga cikin motar,  ya nufi wasu itacen ya tsaya a gurin yana tunanin makomarsa, gida zai koma ya duba jikin mahaifinsa? Ko kuma a nan zai zauna inda be san kowa ba kuma ba shi da komai, and the most annoying part is duk wani abu da yayi amfani da shi na Nimra ne kanwar makiyinsa, tunanin mafita ya saka shi fara tafiya ya koma yar karamar hanyar nan da ya fito, ashe kaddara ke kiransa domin yana tsaka da leke hallitar nan ta da a bayan ya bar gurin ta fito tana dingishi ta nufi gurin shimfidarsa, wani biscuits din ta dauka ta taba ganin irin na dazun ne, kala ce kawai ta banbanta yasa ta jefar ta nufi inda ya aje Gel din da yayi wanka da shi ta dauka tana ta kallon gorar a rayuwarta bayan gorar zuba ruwa irin wanda ake da ice sai kuma ta kwarya bata san wata gorar ruwa ba, hakan ya saka ta daga ta sama tana kallo kamin ta sauke ta fara kwankwasawa can kuma ta kara kunne ta tana saurare, hakan be gamsar da ita ba sai da ta saka dayan hannunta tana shafa gorar, gurin da ta ga an yi hanyar da gel din zai fito ta kai bakinta tana tsotsowa abu ne da saba gani ba, hakan ya saka bata san dannawa ake sabulun ya fito ba, sai kufan da ya rage kawai ta samu a bakinta, abun ka da mutumen daji sai ta hade tana sauraren yadda dandanonsa yake. Jin babu dadi sai wani makaki da kumfa ya saka ta jefar ta nufi gurin ruwan da yayi wanka ta saka hannayenta biyu ta fara debar ruwan tana sha, a take cikinta ya kulle yan hanjin cikin suka murde ya fara mata ciwo. Tun da take a rayuwarta bata taba jin azabar yunwa irin wannan karon ba, a take ta fashe da kuka ta fadi a gurin ta dafe cikinta. Yana daga kafarsa ya kara matsawa gurin da take domin ita bata san ma yana kallonta sai ya ji abu ya dan taba masa kafa dauke kafar da yayi yana dubawa sai ga maciji, wani tsalle ya kara dakawa ya yi baya da sauri.

“Kai....”

Ya furta da mugun karfi wanda hakan yayi sanadiyar zaburar Waira da sauri ta tashi zaune tana kallon inda yake tsaye, babu abun da ya zo a zuciyarsa sai ita, a tunaninsa ita ta turo masa macijin har wani bangare na zuciyarsa na raya masa ita ma din macijiya ce. Da sauri Waira ta fito daga gurin idonta kamar za su fado tsabar kallon tsoron da take masa, ganin yayi baya sosai ya saka ta tsaya tana kallon abun da yake yi ma gudu, maciji ne ba wani babba sosai ba sai dai baki ne dake neman shigewa cikin ciyayin dake gurin, tsoron kwari irin maciji ko bera da wasu kananan abubuwan daji ba ba nata ba ne, domin duk wanda ya saba hawa itacen fruits baya tsoron maciji, musamnan icen ayaba, mango da kuma guava. Da dingishi ta nufi inda macijin ya bi tana lekonsa, ganin be yi nisa ba ya saka ta yi hanzarin bin bayansa, Ameer ya zaro ido yana takowa ya leketa. Dukawa ta yi ta saka hannunta ta cafki macijin da yake kokarin tashi tsaye sai ta rikoshi da hannunta ta mike tsaye.

“Bura'uba, yau na ga bala'i ganin ido”

Furucin da yayi ya saka ta juyo da sauri ta kalli inda yake tsaye, a take zuciyarta ta hau bugawa da sauri kamar zata fado, ta fi tsoronsa fiye da macijin dake hannunta, kamar gwalanniya haka take jin yarensa, a tsorace ta sake macijin da take da zimmar sakawa dutse ta kashe, be sauka a hannunta ba sai da ya cijeta.

“Ashashashash.... Atak Atak gil rièèk bisk...”

Bata san lokacin da ta yi furucin ba, tana yarfar da hannu tana ihu, fuskar mamaki Ameer yayi na jin yaren dake fita bakinta domin shi be taba jin yaren ba.

“Zaki yi kyau da gadi, yadda kike da rashin tsoron nan”

Ya fada sannan ya yayi baya baya yana kallon yadda ta fadi a gurin tana ihu gumi na karyo mata kamar wance aka watsawa ruwa, hannayensa ya daga masa.

“No offense...”

Ya furta tare da juyawa yayi tafiyarsa domin be ga mahadinshi da ita ba balle yace zai taimaka mata, ta ina ma zai iya taimakon wanda be sani ba? Ko mutuwa zai aka ce sai ya taba ta zai rayu be jin zai iya taba sai dai ya mutu din, balle ita ce zai ceto.

“Ahhhhhhh Ashhhh”

Ya dan tsaya yana jin karar da take, zuciyarsa na raya masa maybe ma hadin kai ne so ake ya taba ba, idan ba haka ba miyasa ta je ta taba macijin bayan bata da magani, a dayan bangaren zuciyarsa kuma na raya masa be kamata ya tafi ya barta a gurin a haka ba.

“To me zan mata?”

Ya tambayi kamshi kamar wanda zuciyar take tsaye a gabansa, yana shinshina rigarsa wani karni yake ji duk da kasancewar Waira bata matsa kusa da shi ba, be ma taba ta ba. Yadda zai fita daga dajin ne abun da ya fara zuwa a masa a rai, ya san tafiyar da yayi a motar kamin ya iso a nan a tafiya mai nisa da mota ma balle kuma yace zai tafi kasa, ina ma zai iya? Idan kuma ya dauki motar nan ai ba shi da zuciya ma, to ya zai yi? Gashi ba shi da waya balle ya kira wani, idan ma ya kira waye zai zo? A KT yake fa ba Katsina ba!

“Ya ilahi?”

Cikin daga murya ya fadi haka yana runtse idonsa ya bude, kamar ya kashe kansa haka ya rika ji saboda takaici, a dayan bangaren kuma Waira ta cika dajin da ihun da take yi gwanin tausayi. Sanin dole motar zai dauka ya fita da ita dajin ya saka ransa ya kara ba ci. Kamar ana kiransa haka ya rika ji har ya karasa nesa da inda Waira take kwance tana mulmula da kasa ta rike hannu har wani shidewa take kamar zata mutu. Daker ya cira kafarsa ya dan kara matsawa, sai kuma ya daga kai ya kara karewa gurin kallo, daji da za a iya samun abubuwa masu cutarwa kamar yadda zai yi wahala wani ya shigo gurin balle ya kawo musu dauki.
Ya dawo da dubansa gurinta har yanzu mamakin inda ta fito yake, kalar tufafinta da kazantar dake jikinta, akwai gari kusa da dajin ne ko kuma dai wani ya kawo ta a gurin ko kuma gudowa ta yi? Yana ta jera ma kansa tambayoyin da ba shi da amsar su, a zuwa yanzu kam zuciyarsa ta fara raya masa cewar ba aljana ba ce. Cikin wani yanayi mai kama da bata san tana yi ba ta mika masa hannunta mai ciwon tana jin kamar ya taba azabar ciwon da take ji a yanzu ta bace lokaci daya. Tsaye yayi yana kallonta ya san zafin cizon maciji ba karamin abu ba ne ko da kuwa be taba cizonsa ba ya ji labarin azabar da ake ji, tun tana mika masa hannu har hannu ya fadi idanuwanta suka fara rufewa tana numfashi daker gashinta ya tara gumi, hawayen idonta sun wanke fuskarta sai suka hadu da datti dake jikinta suka yi mata jurwaye.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.