Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 78 of 227
“Assalamu Alaikum”
“Wa'alaikussalam...”
“Who's this?”
“Ameer saurayin Nimra”
Wani deep Ummi ta yi ta nemi guri ta zauna kunnuwanta na sake saka mata sautin muryarsa, wasu zafafan hawaye suka kwankwaso mata kofa.
“Na san be kamata na kira ba, amman ina son mu yi magana ne ta fahimta, ina son ki duba ďakin Nimra ki gani tana nan?”
Ummi ta tashi da sauri ta fita dakinta ta isa kofar dakin Nimra ta tura kofar sai da ga babu kowa a ciki, ta leka bandaki bata ganta ba, a take ta girgiza kai.
“Bata ciki”
“Tana nan tare da ni, ta gudo ta zo inda nake tana son mu gudu ni da ita, saboda tace ba za ku yarda na aureta ba, ita kuma zata iya mutuwa idan kuka rabata da ni, sai dai ba zan iya bari ta aikata hakan ba saboda kuskure ne da zai kara mata tsana a idonku, please ki zo ki tafi da ita zan aiko miki da address inda muke yanzu nan. Ke uwa ce Ummi ban san dadin uwa ba domin na tashi ba tare da na santa ba, tawa uwar ta rasu tun ina jarari saboda haka ban san dadinta ba sai rashinta, amman ke yanyanki sun san dadinki kuma ke ma kin san ďadin yaya, be kamata ki bari Maleek yayi mata wannan dukan ba, da nine mahaifiya ba zai yarda wani yayi min haka ba, balle kuma uwa ta da na tabbatar zata iya hada yakin duniya saboda ta kare ni daga wani ya yi min jina jina a jiki haka, balle kuma Nimra da take mace ce, idan ba ku san alakarta da ni, ku fahimtar da ita cikin hikima da soyayya ba ku yi mata horon da fadan da tunaninta zai gushe har ta bar gidansu ta zo gurina ba, and i want to clean this doubt to you ban taba aikata zina da yarki ba, tsawon lokacin da muka dauka a tare tana boye soyayyata a gareku ba mu aikata abun da kuke tunani ba, i know I'm a bad person but ban taba yarki ba. For now zaki iya zuwa ki tafi da ita kamin mu bar gurin”
Tun da ya fara maganar har ya kai aya Ummi bata ce masa komai ba, sai sauraren muryarsa take wani bakinciki na bude mata sabon feji, hannu ta mika ta taba ginin dake bayanta ta jingina a hankali ta lumshe ido. Can kuma ta bude idon tana ta kallon number da ta yi appearing a truecaller da sunan Ameer. A yau ďanta ya kirata, amman ba kira na sanin cewa ita mahaifiyarsa bace, ba kira nw irin an ďa da uwa ba.
Sakon address inda suke ne ya biyo bayan kiran da yayi mata, ta mike tsaye har lokacin hawaye take, ta kasa tsayar da kuka kuma ta kasa saka hannunta ta share, saukowa ta yi downstairs ta nufi gurin mijinta, tana shiga falon sai ta samu Maleek da Abiey zaune da alama wani abun suke tattaunawa, sai dai shigowarta ya saka sun maida hankalinsu a gurinta.
“Nimra bata gidan nan”
“Kuma..?”
Maleek ya fada da mamakin wani irin hali yar'uwarsa ta daukarwa kanta.
“Ta gudu ta tafi gurin Ameer, ya kira ni a yanzu ya fada min inda zan same ta”
Abiey ya hade wani kwalolon bakincikin da ya tsaya masa a makoshi.
“Ina daf da yafe yarinyar nan...”
“Ba zaka iya ba Abiey, ka fi kowa sanin yadda ake ji idan iyaye suka juya baya, ko ka manta abun da ya faru tsakaninka da Mai Martaba? Ba zaka aikata hakan ga marainiyar da uwarta ta tafi ta bar mana amanarta ba, da ace ta saba aikata maka hakan sai ka ce ka gaji amman bata saba ba, kuskure aka samu ya kamata ka duba mata Abiey, ni bazan iya juyawa yata baya ba”
Ta juya ta fice daga dakin, da gudu ta iso bangarenta tana kuka ta shiga ta dauki hijan dinta ta saka ta dauki makullin motarta ta fito da saurinta ta sauko kasa. Tana fitowa waje sai ta samu Abiey Maleek sun data mota ita kawai suke jira.
AMEER POV.
Ameer ya aje wayar yana matukar jin tausayin halin da ya jefa Nimra, be taba sanin abun da yake aikatawa be kyautu ba sai a yanzu da ya firgita yar mutane ta fita daga hayyacinta. Bama kamar data fito daga bandakin yana kallon fuskarta ya san samun damar kebe kanta ta yi kuka ne kawai ta yi amaimakon wanke fuskar da yace ta yi, yana ta kallonta har Humaira ta zaunar da ita a kujerar da take zaune a dazun, wannan karon tausayine a fuskar Humaira ba kamar dazun ba, bata san abun da ya faru ba, amman yadda ta ga jikin Nimra da kuma kukan da take ya saka jikinta yayi sanyi tana jin tausayinta.
“Zaki iya cin wani abu na kawo miki?”
Humaira ta tambaya, sai Nimra ta girgiza mata kai alamar aa. Humaira ta kalli Ameer dake kallon Nimra.
“Ban san miya faru ba, ban san damuwarta ba, amman ka sani idan kai ka cutar da ita Allah ba zai barka ba”
Ta fada idonta na cika da hawaye, kallonta Ameer yayi yadda take iya fada masa magana ba tare tsoro ko fargabar abun da zai mata ba abun har mamaki yake ba shi, shi kam a rayuwarsa be taba haduwa da tsagera ba irin wannan yarinyar, ba dan ta samu damarsa ba har yaushe zata kalli tsabar idonsa ta fada masa cewar idan shi ya cutar da yarinyar da bata da alaka da ita Allah ba zai barshi ba, sai dai ta ďayan bangaren kalaminta ya sanyaya masa jiki domin duk wani mai imani da tausayi idan ya ga yadda Nimra take zubar da hawaye dole ya tausaya mata, musamman ma shi da ya san silar kukanta da kuma halin da ya jefarta.
“To yar iya na gode sai ki koma gurin aikinki”
Ta watsa matsa harara kasa kasa, tana zaginsa a ranta dan dai ba zata iya fada a fili ba.
‘Bakin Azzalumi macuci, shaidane mai karyar arziki, Allah kadai ya san abun da ya kullawa yarinyar ya yaudare, ita kuma ta fi kyau da kudi ta cutar da kanka, waya sani ma ko ciki yayi mata, dan iska dan kasan wuta... Da wani shegen hanci na shi kamar tattasai, kai kamar ganwon albasa’
Tana tafiya tana zaginsa a ranta, tana ayyana da ace ita ya cuta sai ta karya masa kafa ya zama gurgu.
“Ameer mu tafi yanzu”
“Okay amman akwai wanda nake jiran ya kawo min sako zan dan jira shi minti kadan”
Sai a lokacin ta fara jin ta tsargu sboda babu mayafi a jikinta kuma babu talkami. A da idan zata shigo gurin sai ta saka mask da glass saboda kar wanda ya santa ya ganeta. Dan karamin veil Humairah ta kawo mata tare da gorar ruwa mai sanyi.
“Karbi wannan ki rufe kanki”
Ta kalli Humaira sannan ta mika hannu ta karba, ta lulluba, Humaira ta mika mata gorar ruwa.
“Ba zan iya sha ba, bakina ciwo yake”
Ta nuna mata bakinta dake kumbure.
“Wayyo sannu Allah ya isar miki”
Ameer ya kalli Humaira da sauri ganin tana zakalkalewa.
“Ga wa?”
“Ga wanda ya cuceta mana, daman mace rauni ne da ita wasu mazan suna amfani da haka su cutar da ita, kuma idan mutum ya san be yi cuta ba miye ruwansa da Allah ya isa”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.