Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 147 of 227
“Ranka ya dade idan an amsa wayar sai magana ma ta gagara? Ana rayuwa aka? Shekara ana tare amman kai da Maleek duk kun guje mu? Kun bata tsakaninku kuma kun guje mana”
Ya zauna sannan ya dan yamutsa fuska a zatonsa Dawood ya kira shi ne saboda yayi masa maganar dawowa da yayi da zama a gidansu Maleek.
“Ka yi waya da Maleek?”
“Aa Wallahi yanzu dai nake son idan na gama da kai na kira shi, ya kake?”
Ya daga kai yana kallon itatuwan gurin kamar su za su sama masa amsar da zai bawa Dawood.
“Lafiya kalau, idan na fito zan kira ka sai mu hadu”
“Okay”
Dawood ya amsa ya kashe wayar, domin ya fahimci abokinsa be cikin mood din yin wayar a yanzu, daman Maleek ne sai yace halinsa na son dogon zance a waya, amman Ameer ba haka yake ba. Ya aje wayar gefe ya bude box dinsa ya ciro sarewar ya kafa a bakinsa ya fara busar yana rufe ido ya bude saboda dadin busar da yake ji da kuma daukewar masa damuwa da kewa. Ba shi kadai ba kusan duk wanda ya ji busar dole ne ta dauki hankalinsa, hakan ya saka Mahmood kara gyara kwanciyarsa sakancewar yau babu aiki, busar sai ta masa kamar kara gyara masa bachin ake. Maleek kuma da windows dinsa suke bude ya aje karatun qu'anen da yake ya nufi window ya tsaya yana kallon abokinsa na baya kuma dan'uwansa a yanzu.
Can cikin bachi Waira ta ji busar sai ta bude ido, zumbur ta tashi zaune, ta sauko da kafafuwanta ta saka talkaminta na teddy ta nufi window ta daga curtains din ta leka Garden din dake kasan windows din ko wane daki na gidan, ta kara matsawa ta bude window gaba daya jin busar da ta yi da kyau ya saka yin murmushi, sai ta juyo da gudu ta nufi kofar dakin ta bude ta sauka sauka tana gudu har ta isa gurin kofar falon ta bude ta fita bata tsaya jira talkamin falon ta canja a na fita harabar gidan ba ta nufi Garden tana gudu da hakki har wani murmushin nishadi take. Ameer na ganinta sai ya sauke sarewar yana kallonta can kuma ya tuna da ni abun da yafi zama masa wajibi idan yana tare da ita wato murmushi ya fadada fuskarsa da shi. Sai dai hakan be hanata fahimtar damuwarsa ba, daman tun jiya ta lura da canji da ta gani a tattare da shi wunin ranar. Bata ganshi ba lokacin da ta tafi makaranta sai dai ta dawo ta tararda yanayinsa a haka ta yi tambayarsa ya ce mata ba komai, shi kuma yayi hakan ne saboda baya son tattaunawa akan matsalar. Yau kuma ta ga haka a tattare da shi, sai dai ta fi dora abun a mazaunin ko baya son zaman gidan ne ko kuma gidan ne baya masa dadi.
“Ameer tashi tsaye”
Ba zai iya musa mata ba duk da kasancewarta karama akan shi, dan haka ya mike tsaye.
“Aje abun busar a can”
Ta nuna masa inda box din yake, sai ya aje sarewar. Takawa ta yi ta matsa inda yake ta ware hannayenta ta rumgume shi, so take ta san abun da yake damunsa, shi kuma sai ya ji kamar ya samu shoulder to cry dan haka yayi mata maraba a kirjinsa ya rumgume kamkam a kirjinsa ya rufe ido, her skin is so soft and smooth. Sun yi minti biyar a haka sannan ta sake shi ta daga kai ta kalleshi.
“Ummi ta yi magana da Grandma dinka ko ba haka ba?”
Yayi murmushi tare da ja saboda hancinta.
“Sannu aljana na manta kina duba”
“Minene duba?”
“Wani abu ne da Allah ya hana saboda ba shi da kyau, amman ke kika yi”
“Saboda me aka hana?”
Ya rika hannunta ya zaunar da ita ya fara karanta mata dalilin hanin da kuma illar aikatawa da tarin zunubi da ake samu idan an yi. Haka suka kwashe rabin safiyar a gurin har sai da Ummi ta aiko mai aikinta Hanne kiransu, sannan suka fito Waira na fada masa yadda take iya saffara kowane kalar itace ta hau, har tana fadar ba dan Ummi ta aiko kiransa ba da sai ta hau itacen ta nuna masa.
Tare suka shigo falon yana rike da hannunta ya san haramun ne but he don't mind ya aikata hakan a gaba kowa, domin dan boko ne da ba dan zuwan Waira ba wani abu da ya shafi addini be dame shi ba balle har ya tattauna kuma ba dan be sani ba, sai dai be damu da wannan bangarenba, but one he doesn't want to miss is pray, baya wasa da sallah da duk wani abun da ya shafeta.
Maleek na zaune a kujerar dake fuskarta kofar fita da shiga falon Ameer ya shigo, wani stupid thing is idonsa sun kasa daukewa daga barin kallon hannun Waira dake cikin na Ameer ko fuskarsu be kalla ba idonsa yana kan hannayensu, Waira kam ta ma manta da wani Maleek baya son tana taba maza hankalinta ya tafi gurin abincin da ta tarar Ummi na zubawa Mahmood. Cikin karfin hali Ummi take murmushin a lokacin da ta sauke idonta akan danta Ameer, tana tsananin sonsa da son farincikinsa burinta kawai ta kyautata masa.
“Ameer ka tashi Waira ta jaka waje ko?”
“No ni na tafi da kaina, ta tarar da ni a can ne, Good Morning”
Sai a lokacin ya saki hannun Waira, sakin hannun da yayi ne yayi hankalo da Ummi ta lura cewar yana rike da hannunta suka shigo kenan! Ummi ta zagaya ta ja masa kujerar da take son ya zauna, sai ya zauna yana mata godiya.
“Thank you”
Sannan ya kalli Maleek da gayya ya ce
“Good Morning Maleek”
Ba dan Ummi tana gurin ba, Maleek ba zai amsawa Ameer ba, ba kuma dan komai ba sai dan ganinsa da yayi tare da Waira wani tukukin bakin ciki ke turnikeshi. Amsawar ma da kai yayi masa sannan ya kalli Waira yana jin kamar ya kamata ya fara dukata har sai hannayen da ta rumgume Ameer da su karye. Mahmoud kam da kansa ya mikawa Ameer gaisuwa sannan ya shiga gaba da cin abincinsa. A take Ummi ta fara zuba masa abun da Hanne ta girka, daman Maleek da Mahmood tuni a kusa gamawa da shi. Da wata fuska mai kamar munafurci Waira ta gaishe da Maleek kai tsaye ya sauke kansa kasa yayi mata banza, Mahmood kuma ya dago ya amsa yana tsokanarta.
“Sai yanzu kika gan mu? Ko idonki be gani dazun ne?”
“Yana gani mana, ai na jira kowa ya gama ne”
Maleek yaja kujerarsa baya ya mike tsaye ya fice daga falon zuwa waje domin baya jin shiga daki, kuma baya son zama a inda idanuwansa za su ga abun takaici da haushi. Waira ta ja kujera zata zauna Ummi ta dakatar da ita.
“Kin yi brush? Kuma shoes din da kike yawo da shi a falo, da shi kika fita? Kuma still kika sake dawowa da shi? Wannan wane kalar kazanta ne Waira? Tashi ki cire shoe's din can waje”
Ta wara ido, ita kam ba ma ta talkamin da Ummi ta yi mata magana take ba, tunawa ta yi da Ameer ya bar sarewarsa da wayarsa a inda suka zauna dazun..
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.