Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 123 of 227

Yayi murmushi.

“That's why you're my favorite Safiyya kin fi kowa fahimtata da kusantar inda nake”

Ta rike hannunsa.

“Ka yi min alkawari zaka canja Yayana?”

“Sure for you only”

Taja hancinta sai ta yi dariya ta mike tsaye.

“Daddy yana kiranka zaku ci abincin dare”

Ya busar da iskar bakinsa.

“Oh... Okay ina zuwa”

Ta masa waving sannan ta fice. After like ten minutes da fitarta ya rufe littafi ya mike tsaye yana gyara rigarsa ya fito daga dakin. Ko da ya shiga bangaren Daddy ya same shi har ya fara cin abincinsa.

“Yunwa nake ji ba zan iya jiranka ba”

Ya kalli dinning din da aka cika da kuloli, ya kalli plate din Daddy dake cin tuwon shimkafa da miyar kubewa sannan yaja kujera ya zauna.

“Yau kam Mommy ta yi min favorite dina kai ma kuma ta yi maka na ka”

Daddy ya fada yana cin tuwo fuska sake kamar babu damuwa a tare da shi, tun a lokacin da abubuwan nan su faru Ameer ya daina ganin kwanciyar hankali da far'a a fuskar mahaifinsa sai yau. Daddy ya dauki plate ya mika masa.

“Ka zuba abun da kake so”

Ameer ya karba ya aje plate din a gabansa ya bude one of expensive warmers da suke gurin ya fara zuba White rice da aka sakawa green beans da carrots da green pepper da yellow, haka yake son a dafa masa farar shimkafa sai a hada masa da miyar hanta zallar hanta, a yankata kanana ta yadda kowane spoon sai ya ci da ita a ciki.

“Dazun mahaifiyarka ta zo, sai dai na hana ta ganinka saboda kar ta takuraka i know baka son ganinta a yanzu”

Daddy ya fada yana kai yankan nama a bakinsa. Sai Ameer ya tari numfashinsa.

“ZAHRA na ganta”

Daddy be damu da kiran sunanta da yayi kai tsaye ba, daman yasan indai Ameer ne komai ma zai iya faruwa.

“Oh really? Ka yi magana da ita?”

“Yeah na fada mata karta sake zuwa gidan nan”

“Saboda gidan nan gidanka ne?”

Ameer ya kalli Daddy.

“Daddy don't joke about this”

“I'm not joking shiyasa da tace zata ganka na hana, amman idan zata zo gurina ko gurin Matata wannan ba huruminka ba ne? Ka fi kowa sanin bana son ana wulakanta mutane”

“Daddy bana son ganin matar nan, da bata min duk wani tsari da tunani na rayuwa”

“I know amman dukan dam'adam ajizi ne Ameer, tana da laifi tabbas kuma ta cancanci duk wani hukunci da zaka yanke mata, amman ni ma ina da nawa laifin, meyasa ban nuna maka haka tun farko ba? Wata kila da duk wannan rudanin be same ka ba”

“Daddy ka yi hakan ne saboda tace ta yafe maka ni, domin ita tana da wasu yayan da suka fi soyuwa a ranta”

“Ameer ko da babu zuwan wannan ranar da ita zata fada maka, ni na san wata rana idan bana raye za'a fada wannan, domin yana rubuce a cikin wasiyar da zan bari, saboda hakki ne da ba nawa ba dole kuma na sauke shi, saboda akwai yan'uwana da suka san da wannan maganar, na tabbatar idan bana raye za a dago maka da wannan maganar, a can ina tunanin kamar idan bana raye abun zai fi zame min kwanciyar hankali, sai dai halin da na ganka ciki a yanzu, ya saka na ji cewar ka san komai a lokacin da nake raye zai fi sauki fiye da bayan raina, domin zafin zai zame maka biyu, amman a yanzu zan iya kula da kai, zan ganka na yi farinciki, domin babu abun da zai canja daga matsayinka na ďana da nake kallonka da shi”

Ya yayinda ya fara cin abincin kamar an masa dole. A lokacin ne Daddy ya aje spoon dinsa ya hade hannayensa yana kallon Ameer.

“Wallahi da za a iya shiga abun da yake zuciya, Ameer da ka kara gode Allah da wannan abun ya bayyana, domin ya kara maka kima da kauna da tausayi a idona, ina jin kaunarka a yanzu fiye da da”

Tsayar da cin abincin yayi ya kalli Daddy.

“Ba dan nasan kudi ba zai siye kudi ba, da na ce kudi matar nan ta baka har ka sauya nan take, wata kila ta siye ka da kalamai ne”

Dariya sosai Daddy yayi.

“Sai kuma gashi kudi baya siyen kudin, ashe wannan ya isa ya fahimtar da kai cewar tunani ne irin na babban mutum mai shekarun da ya isa ya haifeka, kalamai sun yi kadan su siye zuciyata Ameer, ni dai ina da saukin kai da saurin sauka idan na yi fushi ina bude zuciyata na fahimci ciwon wani ba ciwona ni kadai ba, zuwan Mahaifiyarka a gidan nan, ya fahimtar da wasu abubuwan da ada ban fahimta ba, akwai labarai masu matukar tausayi da sosa zuciya a bayan shafin faruwar komai, wata kila da bata ba ni kai ba, da yanzu ban san dadin zama uba ba, ban san zafin rabuwa da kai ba. Ameer bari na fada maka wani abu da ban taba fada maka ba, Mahaifiyarka ta taba ceton rayuwata a lokacin da babu kowa a kusa da ni, da ace bata ceto ni a lokacin ba, da yanzu duk wannan rayuwar ba mu yi ta ba, tana da tsohon cikinka ta gudu daga garin Kano ta tafi wani kauye da yake zaria saboda ta boye cikinka ta haihu a can so that idan ta haihu ba zata bawa Jamila kai ba, baka yi tunanin kauna ta saka ta yin haka ba irin ta uwa da ďa? Zan tafi gurin wani business trip jirgina ya fadi a cikin wani daji da ban san kowa ba, karfen jirgin ya danne ni, mahaifiyarka ita ta taimaka ta fito da ni, ni kadai na tsira a cikin jirgin nan da bata taimaka min ba da ni ma ban rayu ba (Masu makaratu kun tuna lokacin da Zahra ta ceto Mr Bashir a cikin littafin farko CIWON SO?) a lokacin ban samu taimakonta ba saboda ta bar garin tana zubar jini aka kaita asibiti jinina aka saka mata, sai dai tsoron kar ta rasaka ya saka ta sake guduwa daga nan ban san a inda ta koma ba, kudin na na bada a bata ma bata karba ba, ka ga dace kudi ne a gabanta, babu abun da zai hana ta tsaya ta karbi kudin, ban sake ganinta ba sai da Jamila ta aikata abun da ta aikata, sai ya zama nonon Jamila da madara da duk wani nono a duniyar nan baya baka lafiya a ciki, sai nonon Zahra, a dole ta gidan da zama saboda ta samu kusanci da kai”

Ameer ya aje spoon din ya kalli Daddy.

“Daddy abinci ka ce na zo mu ci ba hirar wata ba please”

“Baka yarda da ni ba kenan? You can google it ai tarihi baya boyuwa zaka ga lokacin da hadarin ya faru, Ameer ba ina fada maka wannan ba ne kawai saboda ka sauko daga tudun daka hau, no ina fada gaskiya ne da kuma abun da na fahimta. Da zaka bawa mahaifiyarka dama ka tambaye ta wasu abubuwa wata kila da baka sake yin fushi da ita ba, ni dai na san baka dukan abun da zan iya domin samun farincikinka, shin baka tunanin lokaci yayi da ya kamata ka rama min abun da na yi maka? Ka saka ni cikin farincikin nima? Kai ai kana da sauran lokaci, amman ni na sha ruwa shekaru sun ja, ga kuma ciwo yana yawan kawo ziyara, kar sai bayan bana raye ka ce zaka nuna min kauna, lokacin nan is too late komai ya kare”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.