Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 137 of 227
“Ta so mu je”
Ya nufo inda take yana zaunawa sai ta mike tsaye tana kallon kofa.
“Ya Maleek zai iya dukaba”
Juyawa yayi ya kalli kofar a zatonsa ko ta ga Maleek din ne tsaye a gurin, juyowar da zai yi sai yayi arba da Ummi ta fito ta wata kofa da a ina take fitar da mutum ba. Waira ta nufe ta da sauri tana kuka.
“Ummi Ya Maleek zai iya dukana yau ba zai bar ni ba”
“Babu abun da zai miki kwantar da hankalinki, na yi masa magana”
“Baki san me ya faru ba”
Waira zata fada Ummi ta tare numfashinta tana saka hannu ta dago kanta.
“Na sani je gurin mota ki jira Ameer”
“Toh ba zai doke ni ba?”
“Babu mai ikon dukanki a cikinsu je ki jira shi”
Waira ta saki hannu Ummi ta juya ta kalli Ameer dake kallonta sannan ta fice daga falon tana share hawayenta. Ummi ta matso kusa da Ameer dake tsaye yana kallonta ta ce.
“Ba dan ni ba, wata kila ni ba ni da wannan kimar da zaka min alfarma, amman ina rokonka saboda ita Waira dan Allah ku daina rigima kamar kananan yara a kanta kuna daga mata hankali, Waira kamar amana take a gurinmu dan Allah ka kula da ita, bata da gata sai mu bata da dangi bata da kowa sai mu, idan bata ji sanyi a gurinmu ba a gurin waye zata ji?”
“Karki damu da wannan, na san Maleek ya kitsa karya da gaskiya ya fada miki, wata kila ma na fiki son kula da ita a yanzu, ke kina daukarta a ƴa ne, ni kuma ina kallonta a wani natsayi na dabam ne, ni ba zan gidanki dan na daga miki hankali ko iyalinki ba, idan ma baku da bukatata zan iya tafiya...”
Ummi ta kara matsowa kusa da shi tana girgiza masa kai da sauri.
“Aa nan din ma gidanku ne, sai dai ka yi kora ba wai a koreka ba, kawai ina damuwa da Waira ne ka yi hakuri”
Ba ce mata komai ba ya juya ya fice daga falon, windows ta nufa tana leken motarta, ta saka hannu ta rike curtains din idonta na bin motar da kallo har sai da har ya bar gurin da idonta suke iya gani. Fitar Ameer da minti biyar Maleek ya shigo falon ta kofar da Ummi ta fito dazun, wato kofar dake sada mutum da part din Abiey.
“Ya fa tafi da ita”
Ummi ta saki curtains din ta juyo ta kalleshi.
“Miye damuwarka da hakan ne Maleek?”
“Amman dai kin san abun da ya faru da Nimra”
“Abun da ya faru da Nimra kamar ya? Fyade yayi mata? Soyayya ce kawai shi ma kuma na tabbatar da ace ya san haka zai faru da ba zai aikata ba, kuma ita ma hanyar mutuwarta ce a haka, ko da ba Ameer ba dole wani zai yi sanadiyar bugawar zuciyarta”
“Idan kuma fansa ya zo dauka fa, zai iya amfani da Waira sabo...”
Wani irin kallo Ummi ta watsa masa da ya saka shi kasa karasa maganar.
“Fansa? Ka taba ganin ďan da ke daukar fansa a gurin uwar ta dauki cikinsa ta yi nakudarsa ta haife shi? Ka taba gani? Me yasa zuciyarka bata raya alheri akan ďa?”
Maleek ya gyara tsayuwarsa a yanzu ya san duk wani abu da zai fadawa Ummi ba lallai ne ta fahimta ba, amman shi a baibai yake kallon abin domin ya fi kowa sanin waye Ameer, ba kamar ita da a yanzu take saninsa ba. Ummi ta nuna shi da yatsa.
“Ka cire idonka akan Ameer, ka kawar da kanka ga barin kallon alakar dake shiga tsakaninsa da Waira, ina son farincikin kowa a cikinku, kuma ina iya karantar abun da ke idon Ameer, na da yakini da tabbacin ba zai taba cutar da Waira ba, Ameer ya canja a yanzu sanin da kai masa a ad ba shi ba ne, dan Allah kar ka bari shaidan yayi tasiri a zuciyarka ya dasa maka kiyayyar dan'uwanka”
“Ni bana kiyayya da Ameer, kawai ina fadar halinsa ne, kuma ke nake tausayi idan Ameer ya aikata abun da baki yi tsammani ba zaki fi kowa shiga damuwa da bakinciki”
“Ba zai aikata ba ina baka wannan tabbacin, ka saka ranka a inuwa domin a yanzu zai dawo da zama a gidan nan ne, dole ne ka dauke idonka daga alakarsa da Waira wata kila alakar da kake tsammani ba itace a gabansa ba”
Ya hade yawu har ta yi kamar zata wuce sai kuma ta dawo ta kalleshi
“And bari na maka wani gargadi wannan ya zama karo na karshe da zaka aibatanta Ameer a gaban mahaifinka, kalaman da ba su dace ba, kokarin nuna yana son bata tarbiya wasu, duk bana so, uwa bata son a aibata ďanta, zaman a gidan nan ina son na ba shi farincikin da ya rasa ne, na kusanto da shi a kusa da ni, idan baka taimaka min na samu haka ba, to karka yi kokarin bata min rai”
Tana gama fadar haka ta nufi hanyar stairs, Maleek ya runtse idonsa sosai har sai da ta haye sama, sannan ya bude idon, ya san ba zata fahimci abun da yake kokarin nuna mata ba, shi dai kawai yana tsoron kar Ameer ya lalata rayuwar Waira ne, hakan zai kara jefa Ummi a damuwa, amman tun da bata gani zai dauke ido akansu kamar yadda ta fada, daman can ma miyasa ya kula? Me yasa ma ya tsaya magana da Ameer din? Why ya shiga part din Abiey a fusace yana fada akan Ameer ya sumbanci Waira? Ya rike hannunta? Miye damuwarsa ma da haka. Daga gurin ne ya daukarwa kansa alkawarin ko Ameer zai kwantar da Waira a gabansa ya yanka ta da wuka ba zai nuna ya gani ba ma balle har yayi magana, ko da Ameer zai nemi yin lalata da Waira a gabansa idonsa ba zai ce uffan ba. Bayan ya daukarwa kansa alkawarin ne ya nufi kitchen a fushin zuciya da bacin rai da be san na minene ba, ya bude fridge ya dauko ruwa ya nufi gurin da aka aje cups ya daga container din ya dauko glass cup ya aje ya zuba ruwan ya dauka ya sha, ya sake zuba wasu ya sha har sau uku still zuciyarsa bata sauka a daga hawan da ta yi ba.
“You should act mature mana Maleek ina ruwanka a ciki? Ido zan saka musu ai kamar yadda ta nema ni na san Ameer sai ya saka ki zubar da hawaye Ummi”
Ya daki gorar ruwan da karfi har sai da ta fadi kasa, magana yake da kansa cikin wani irin fushi da zafi rai da fushin zuciya marar misaltuwa.
AMEER POV.
Yana tukin yana kallon Waira dake gefensa tana share kwalla, be ce mata komai ba tun da suka shigo motar ita ma bata ce masa ba ko inda yake bata kalla ba, gashi ta dan bata fuska alamar fushi take, fushin da be san na minene ba. Rage wutar motar yayi ya faka gefen titi ya kashe motar yayi relaxing akan kujera yana kallon dayan gefen titin. Hakan ya saka ta juyo ta kalleshi sai ta ga ba ita yake kallo ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.