Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 110 of 227

Sai a sannan Ameer ya samu gwarin guiwar dagowa ya kalli Daddy idonsa sun rine sun yi ja sosai kamar wani mashayi.

“Da rai na kashe da zan fi farinciki fiye da sanin abun da na san shi ne silar ajalina”

“Me kake nufi?”

“Daddy....”

Sai ya kasa furtawa sai hawaye yake kamar ba shi ba.

“Daddy i know it maganar da Mahafiyar Nimra fa fada i talk to Ammy ta tabbatar min da cewar gaskiya ne, and i confront her too ta kara tabbatar min”

Daddy yayi murmushi.

“Baka jin magana ta Ameer, rashin bin abun da nake fada ya jefa a cikin hali da dama, kuma zai sake jefaka a nan gaba, zuciyarka bata raya maka Jamila tana da alaka da Zahra ba? Shiyasa har ta furta sunanta? Saboda ta san zata goya mata baya su rusa tunaninka”

Ameer ya sake kallonsa da mamaki domin be tana sanin sunan matar da take cewa ita uwarsa ba ce sai a yau a bakin Daddy

“How do you know her name”

“Who?”

“Zahra?”

“Oh... Oh... Because a called her Husband kuma na gargade shi akan ya jawa matarsa kunne, ba zan dauki iskancin da take yi ba, ba zan lamuncin ta saka min tashin hankali a gida ba, and i already told my lawyer, idan ma akan hakan ne kakae wannan kukan da tashin hankali ka daina duk wani abun da za su fada maka karya ne”

“Me yasa za su yi karya?”

“I don't know, maybe suna da wata manufa akan hakan, musamman ma Jamila zata iya shirya wannan saboda na ko yarda na maida ita gidana”

“Daddy you can't hide this anymore, Ammy ta fada min komai ciki har da dalilin fitarta a gidanka, ta fada min dalilinka na boye min cewar mahaifiyata ta mutu”

“Kuma ka gamsu ka karya mahaifinka? Wane irin abu ka sha ne Ameer? Da rana tsaka wani zai kalleka yace kai ba dan Bashir ba ne dansa ne kuma ka yarda?”

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro takardar yarjejeniyar da Zahra ta ba shi ya mikawa Ummi.

“What about this?”

Dauke wuta Daddy yayi for a seconds yana kallon takardar sannan ya mika hannu ya karba, sai da ya gama karantawa tsab sannan yayi murmushi mai sauti dake nuna be amince da abun da ya gani ba.

“Ina tunanin na haifi ďa mai tsananin basira da saurin gane komai, amman yanzu dan wannan abun zai saka ka karaya? Baka san muna a wani zamani da cigaba zai iya sakawa a yi komai ba?”

Ameer ya ciro hoton mahaifinsa ya mikawa Daddy.

“Wannan fa?”

Wannan karon dariya Daddy yayi.

“Karka ba ni kunya mana Ameer, wannan hotonka ne aka canja saboda a karkata hankalinka ka yarda da abun da suka shirya”

Ameer ya girgiza kai.

“Na san kana kokarin boye min komai ne saboda kai ma baka son karbar wannan gaskiyar mai daci, Daddy ina son ka sani, no matter how you try ko da ka yi nasara a yanzu, bayan mutuwarka dole gaskiya zata bayyana, sanin gaskiya ba zai canja komai a zuciyata ba, sai karin kimarka da daraja a idona”

Daddy ya saka hannu ya shafa kan Ameer.

“Karya suke fada maka Ameer idan baka yarda da ni ba, za mu iya yin gwajin jini tsakaninka da su da kuma tsakanina da kai, ta nan ma za a iya tabbatar da komai, kana yawan janyo min abubuwan tashin hankali, amman wannan da ka dauko ya fi ko wane daga min hankali, cuta kake kokarim haifar min da bana tunanin zata warke min da wuri”

“Daddy, ina son ka kalli cikin idona ka ratse min da Allah cewar Zahra karya take, ba mahaifiyata ba ce, ka karya hoton nan da yake hannunka, kuma ka tabbatar min da cewar kai ne ka haife ni ba sadakata aka baka ba”

“Tsaurin idonka ya kai har ka kalli idona ka fada min haka? Ba ka yarda da duk abun da nake nake fada maka ba? Idan da su kake son zama tashi ka tafi, zan iya hakura da rashinka”

Daddy ya fada a tsawace yana mikewa tsaye ya nuna masa kofa.

“Idan har zan fita daga nan, zan tafi ne a inda kai da ita ba zaku sake ganina ba balle jayayya ta hada ku, zan yi fatar mutuwa ne kai tsaye Daddy, na gode da duk wata kyauta da kulawa da ka ba ni, kuma an yi amfani da wannan damar na roki yafiyarka na abun da na aikata maka tun kurciya har kawowa yanzu dan Allah ka yafe min Daddy”

Ya mike tsaye ya nufi kofar da zimmar fice, gaba daya sa jikin Daddy yayi sanyi zuciyarsa ta karaya sai dai har lokacin be shirya fadawa Ameer gaskiya ba, da gaske baya son tashin hankalin Ameer kuma shi ma be shiryar karbar tashin hankalin cewar shi ba mahaifin Ameer ba ne.

“Ameer”

Daf da zai fice Daddy ya kira shi, sai ya tsaya cak sannan ya juyo ya kalleshi.

“Zo nan”

Ame
“Daddy boye min gaskiya zai kara jefani a cikin wani hali ne kawai, miyasa baka fada min sunan mahaifiyata ba even for once? Baka fada min garin da take ba? Baka nuna min yan'uwanta ba? Baka taba bani labarin dalilin rabuwarka da Ammy ba, baka fada min dalilin da ya saka Ammy take kauna har yanzu ba duk kuwa da kasancewar ta rabu da kai, babu ta inda nake kama da kai, bana kama da danginka, baka taba bani labarin mahaifiyata ba, yanzu kuma kai tsaye ka fadi sunanta, me zai kasa ka boye min gaskiya? Why?”

“Saboda ba gaskiya ba ne, Ameer ni mahaifinka ne? Baka da wani uba sai ni...”

“Wata kila zaka fada min gaskiya a lokacin da gaskiyar ba zata amfanin komai ba, sai dai ka tsaya a gaban gawata kama zubar da hawayen nadamar boyen da kake kokarin yi, Daddy kai da kake ďa kamar ni mai saka ka cikin tashin hankali da fitina da faduwar gaba da ciwon kirji, kake tsoron fada min gaskiya saboda karka rasa ni? Ina ga ni da nake da uba kamar kai? Na san gaskiya Ammy ta fada min amman ina tsoron gaskiyar saboda rasa ka Daddy”

Daddy ya fadi zaune kan kujera idon na sauya launi.

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, Ameer don't force me to do this please”

“Amsa kawai nake so daga bakinka gaskiya suka fada ko ba gaskiya ba?”

Daddy ya mike tsaye a daidai lokacin da hawaye suka sauko masa ya nufi gurin windows din dakinsa ya tsaya ya rungume hannayensa ta baya yana kallon harabar gidan.

“A kowane dare da wuninsa, ina rayuwa a cikinsa da fargabar halin da zaka tsinci kanka idan irin wannan labarin ya zo maka, wannan tunanin yana haifar min da tsoro da bakinciki, sai dai ban saka tsammanin zuwan hakan a yanzu ba? Domin ban yi tsammanin na karya daya daga cikin alkawuran da na daukarwa Zahra ba, ta mallaka min kai bayan na mata alkawarin kula da kai fiye da yadda zata iya, na mata alkawarin baka tarbiya da ilmi, na mata alkawarin baka gata da duk wani kalar jindadin duniya, ban kuma yi tunani a akwai inda na gaza ba, sai dai abun da na gagara ganewa a yanzu shi ne, me zai saka ta saka min da wannan? Me zai saka ta daga min da tsohon ciwon da na yi zaton na warke shi? Akan wani dalili zata tambayi ni ajiyar da ce ta kyautarda zuciya daya?”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.