Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 84 of 227

‘Waya koya miki, hawa itace? For how long kike hawan itace’

Wani salon iskanci da rainin wayo na kin son magana irin na Maleek, duk a cikin ransa yake mata wadannan tambayoyin kamar ance masa zata iya karanta abun da yake ransa ne. Ganin wannan ba zata fitar da shi ba ya saka shi tambayarta abun da ya saka ya biyota a gurin, domin tun a dazun da ta yi maganar abun yake cinsa.

“Waya fada miki Ummi zata mutu?”

Ta yi kasa da kanta kamar ba ita yake magana ba.

“Uh.. Hmm”

“Waira na sani, ta gani”

Cikin yanayin na jinin sarauta ya taka ta karasa inda take tsaye, sai ta yi baya ta jingina da wayar dake gurin.

“Waya fada miki? Ta ya kika san Ummi zata mutu?”

A take idonta ya cika da hawaye.

“Ummin tana da ciwo ciwon mai kashe Ummin ne, ciwon na mutuwa ne”

“Wane lalar ciwo ne?”

“Ban sani ba, amman bata fadawa kowa ba Ummin tana jiran mutuwa, Waira ma tana jiran mutuwa”

“Waye zai kashe ku? What kind of nonsense is this?”

“Ba karya ba ce, na gani da gaske Ummin tana da ciwo, kuma Ummin tana son ta ga Ameer”

Ta share hawayenta, maganarta ta masa wani iri ya kasa yarda gaskiya take fada ko akasin haka, amman da karya take ba zata fadi haka a gaban Ummin ba dazun har tana kuka. Sai da yayi kamar ya tambaya waya bata zomon dake hannunta sai kuma ya juya ya fice daga gurin, da kuzarinsa ya dawo part din Ummi yana kokarin hawa Stairs din Jabir da Mahmood suka sauko, kai tsaye dakin Ummi ya nufa, sai da ya suke ajiyar zuciya sannan ya kai hannu ta tura kofar ďakin ya saka kafarsa sai duk ya ji wani iri domin ba zai iya tuna lokacin da yake da kurciya ya shiga ďakin mahaifiyarsa ba, ko ciwo take sai dai ya gaisheta a falo ko bangaren mahaifinsa idan sun hadu. kamshin turaren jikina kamshin dakinta, jimke hannayensa ya fara yi thinking of ta ina zai fara, kamar wanda aka kama yana sata haka jikinsa ya fara rawa tun kamin yayi abun da be saba ba wato bincike...
[6/17, 10:50 PM] My S Line: 35

THREE DAYS LATER...

Nimra ce kwance a cinyar Dr Zainab, kallo daya zaka yi mata ka san damuwa da kuncin zuciya sun saka ta a gaba, domin ta rame sosai kamar ba ita ba, kwana biyu bata iya cin komai sai ruwa su ma kuma idan Ummi ta matsa mata ne, gaba daya ta dauki damuwa ta saka a ranta, bata fita daga dakin kullum tana ciki idan an kawo mata abinci yadda aka aje shi haka za a dauko shi. Duk wani kokari da yar'uwarta Namra ta yi na ganin ta dauke mata hankali daga damuwa abun sai ya ci tura domin ba kadan soyayyar Ameer ya kama ta, tana taba jin som namiji kamar yadda take son Ameer ba, bata san yadda zata cire soyayyarsa a ranta ba ko da kau shekaru dari aka raba mata nan gaba, wani irin sonshi take irin son da take jin zata iya kai karar Abiey da Ummin a gurin wadanda za su barsu su ji maganarsu abarta ta auri Ameer.

“Nimra rayuwa ta yi haka? Dubi yadda kika maida kanki? Ni dai wannan zuwan be min dadi ba sam na ji abubuwa kuma na ga abubuwan da ban jidadinsu ba”

“Mommy yanzu babu yadda zaki yi ki lallaba Abiey ya bar ni na auri Ameer? Wallahi ina son Ameer, daman na san haka zata faru shiyasa na ce zan fada miki wata magana tun a farkon zuwanki na so na fada miki abun a sirrance saboda ki san yadda zaki shawo kan Abiey sai gashi komai ya lalace ya zo ta inda ba mu zato ba”

“Nimra abun da iyeye basa so hakuri ake yi, karka zafafa kace kana so, abubuwa da yawa ba alheri ba ne a garemu, ki yi wannan nazarin kuma ki yarda da hukuncin Allah”

“Mommy ba zaki gane abun da nake nufi ba, Mommy Soyayya akwai ciwo idan kana son mutum zaka ji zaka iya aikata komai saboda ka same shi, idan kuma aka ce mutumen ya barka ko an raba ku sai ka ji kamar ka kashe kanka ka saboda bakinciki”

Dr Zainab ta yi dariya.

“Nimra kenan, ku da kuke yaya kuka san soyayya balle kuma mu da muke iyayenku? Babu alakar soyayyar da ban gani ba tsakanin Mahaifinki da Zahra, idan an bude miki sirrin yadda aka yi sanadin samuwarki zaki sha mamaki, amman da iyayenki suka yi hakuri daga baya sai komai ya zo musu da sauki fiye da yadda suka sha wahala a baya, Mahaifinki ya zo Zahra irin son na tabbatar ace be aureta abu ne mai wahala yayi aure, abu ne mai wahala alaka mai karfi ta sake shiga tsakanina da shi, saboda yana ganin ni na hana shi samun Zahra wacan lokacin, babu kalar haukar da Abiey be yi ba akan Zahra, shiyasa shekaranjiya da na gansu suna sa'insa sai abun ya bani kuma kuma yayi min ciwo, domin tun da ya aureta be taba kirana ko ita ta kawo min kararsa ba, ban ce basa samun sabani ba, amman basa bari a gane balle har ace wani ya shigo yana musu sasanci, Abiey baya son fushin Zahra ko kadan, idan tana son abu yakan fita kaunarsa amman wannan karon abun da na ji kuma na gani ya bani mamaki, sai dai ta wani bangaren yana da gaskiya domin ina hango abun da zai biyo baya, idan na yi tunani ta wani bangare ina ganin cewar gaskiya yake fada, kuma dole a daga masa kafa idan ya nunawa ďan makiyinsa kiyayya, musamman ma ta yadda abun ya bayyana, da ace ba ta wannan hanyar abubuwan suka biyo ba wata kila da an samu sauki, sai dai yadda abubuwan suka zo ne dole su fusata shi”

Nimra ta daga daga jikin Dr Zainab ta kalleta.

“Ban gane abun da kike nufi ba Mommy wani abun nw ya faru?”

Gudun kar aji mutuwar sarki a bakinta ya saka ta kawar da maganar gefe ta hanyar yin murmushi.

“Bari na tashi na duba aikin da ake kar abar Namra ita kadai da aiki, ko zaki zo muje?”

“Aa, Namra ta jidadi zata auri wanda take so an barta zata yi soyayya ta wanda take kauna ba kamar ni ba”

Ta fada tana jin wani sabon kuka na sakata gaba. Dr Zainab ta ce.

“Shi ma sai an bincike halinsa da zuri'arsa idan ya cancanta sai a aura mata idan kuma be cancanta ba sai a bata damar kawo wani kamar yadda aka baki ke ma a yanzu”

“Ni zan kawo ba Mommy, bani da kowa sai Ameer idan ba shi ba sai dai na mutu ban yi aure ba”

“Aa Allah dai ya saukewa”

Shi ne kadai abun da ta fada ta fice daga dakin. Kasa ta sauko tana jin yadda falon ya dauki kamshi ana ga shiryawa bakon Namra abubuwan dadin, ita ma ta zage dantse ana ta aikin da ita saboda bakon nata ne kuma wanda take matukar jin da shi, ko ba komai kokarin zuwan da yake cikin kwana uku abun a yaba ne, kuma hakan ya nuna da gaske sonta yake da aure ba iya chat da waya abun ya tsaya ba, domin tun haduwarsu a Instagram sau biyu kawai suka taba ganin juna a fili, shi ma kuma zuwan gaggawa yake a Abuja sai ta fita su hadu a wani gurin su gaisa, sai da ta sada shi da Ummi sun gaisa sau biyu, ita ma ta gaisa da yan'uwansa sosai har live video yayi ta gaisa da iyayensa, sun santa ta san su. Yanzu kuma ta sanar masa iyayenta suna son ganinsa sai ya zabi ya yanke duk wani abun da yake ya gabatar da kansa a matsayin mai son yarsu. Sati ta bashi shi kuma ya rage ya zabi kwana biyu, saboda damar da yake ta jira kenan na neman aurenta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.