Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 148 of 227
“Ka manta waya da sarewa a can, bari na dauko sai maka”
“Oh haka fa”
“Toh idan kin dauko ki bar talkamin a waje karki shigo da su”
Ummi ta fada sai ta amsa mata da kai sannan ta juya ta wuce daga falon, hankali na gurin abun da take son daukowa dan haka bata lura da Maleek dake gefen entrance din ba ta hauka abun da a dan karamin stairs dake gurin ta nufi Garden, dukawa tai ta dauki wayar Ameer da sarewa sai da ta gwada busa sarewar sannan ta juyo tana murmushi sai jin ta yi ta bugi mutum, tana daga kai ta yi arba da Maleek yana kallonta fuska babu annuri, kamar bakin hadari ta dan yi baya kadan gabanta na faduwa.
“Wato ke saboda kin cika har kin batse, har ke da kanki kike bude hannu ki rumgume Ameer ko?”
Ta sauke idonta tana mamakin yadda yake damuwa da abun da ba laifi ba ne a gurinta, idan ma addini ya hana ita ai ba addinin take ba, shi kuma Ameer da yake yi be yi complain ba sai shi dan kawai ya tsaneta. Ta yi gefe kamar zata kauce sai ya sha gabanta
“Ina magana kina tafiya? Ina zaki je? Kin raina hankalin mutane ko?”
Yanzu kuma tsoron magana take kar ta karawa kanta laifi a gurinta, dan haka ta yi shiru ta marairaice fuska tana shafa sarewar dake hannunta. Bakinciki fa fushi zuciya na irin wanda ya kasa controlling kansa ya saka shi fisge sarewar ya kefar kusa da pool. Ta bude ido ta saki baki tana mamaki.
“Ta Ameer ce fa?”
“Ameer din miye tsakaninki da shi, ban gargade ki akan tana jikinki da yake ba?”
Cikin bacin rai da ya fi kama da shagwaba ta yi kokarin bashi amsar abun da ya tambaya
“Amman kai ai....ai... Kana taba ni har a nan ma, kuma kana shafawa min jiya ba har kiss ka yi min ba, amman idan Ameer ya taba ni sai ka yi fada saboda mu baka son mu”
Ta juya tana kara bata fuska ta nufi inda sarewar take. With shock ya bita da kallo kamar wani sakare ya san ko rantsuwa yayi ba zai yi kaffaraba Ameer ne ya saka mata ta fadi haka, domin shi dai be san yayi mata haka ba, Allah ma ya kiyaye ya ji me a jikinta? Shi ko so zai yi idan ma Allah ya kaddara masa son a mace zai yi babbar mace mai amsa sunan mace ba ita ba. Shi da rika hannun mace ma aiki ne a gurinsa zata masa kazafin ya taba ta. Takawa yayi ya isa inda take tana goge sarewar a jikin kayan bachinta.
“Indai Ameer ya saka miki fadin haka, to be samu sa'a ba, domin ni kowa ya san ba halina ba ne, ko da halina ne ba zan yi ke ba, Allah na tuba balle kuma ba abun da na saba yi ba ne, babu wanda zaki fadawa haka ya yarda”
Watsa masa wani kallo mai kama da harara.
“Ni ba wanda ya tsara min, ai ka yi ne na gani, har ina bachi ka fara taba ni ka dauka bachi na mai nauyi ne sai gashi na farka kuma yi min kiss a front head ya fita”
Rage ido yayi yana kallonta, this time around ya gane dai mafarki ta yi wata kila rakiyar da yayi mata da dare ta shiga dakinta bayan shiga bachi ya dauketa ta yi mafarki sai ta dauka kamar a zahiri ne hakan ya faru.
“Ko ma dai minene na fada miki karki sake hada jikinki da na Ameer, karki kuskura ki sake because wannan lokacin ba wasa nake ba, kuma sai na fadawa Ummi abun da na ga kin yi”
Yana kaiwa karshe ya saka hannunsa ha hankadata sai ta tafi suuuuu tana kara zuwa cikin Swimming pool, tare da fada da wayar da sarewar tana kokawa da ruwan domin bata taba fadawa a ruwa haka ba, ban da zuwa gidan Ummi ma da ta waye take wanka akai akai, bata san ta ga ruwa ko ruwa ya ga jikinta ba, dan haka bata hada hanya da ruwa ta iya hawan tsaunuka da bishiyoyi amman ban da shiga ruwa saboda rashin son wanka. Ya juya zai yi tafiyarsa sai ya ga tana yin kasa yadda take fisge fisge ma kadai ya isa ya saka shi gane bata iya swim ba, ga muryar da ta bude domin neman ceto idan ta je magana sai ruwan ya wuce mata.
“Fito mana kina wani abu kamar baki iya ruwa ba, I'm not like Ameer balle ki raina min hankali little girl like you...”
Yana fadar haka, kamar ya ce mata kara, sai ruwan ya hadeta gaba daya ta yi kasa. Ba tare da tsayawa tunanin komai ba, without any thinking ya yayi tsalle ya fada ruwan domin cetonta...
TEAM MALEEK.
TEAM AMEER
ko da yake Maleek ya ce me zai yi da ita. Amman dai ni dai ina hango wani abu a zuciyar Maleek Allah yasa ku ma kuna hangowa 🤣
[7/22, 10:47 PM] My S Line: 60
Da sauri ya fito da ita daga cikin ruwan a aje abakin gabar yana kallonta. Kamar wanda dabara ta bacewa haka gurfana a gurin yana kallonta not knowing what to do, halin da ya ganta a ciki ya mugun rikita shi yadda take ta tari tana bude baki ya saka masa tausayinta, idonta har rine da ja alamar ruwa ya shiga cikin idon. Gashin kanta ya jike shakaf. Cikin karfi hali ta mike tsaye tana ta tarin sai yayi saurin mikewa tsaye shi ma yana kallonta, a lokacin ne kuka ya zo mata, domin a yanzu ta tabbatar Maleek makiyinya ne nakarshe da baya bukatar ganin rayuwarta ko da wasa.
“I'm sorry ban san cewa baki iya ruwa ba... Da ba zan miki haka ba”
Ta kalleshi idonta na rawa ta raba gefensa zata wuce.
“Karki shiga falon a haka mana, bari na sama miki wani abu”
Ya fada yana dauke idonsa daga barin kallon jikinta, domin ruwan da ta shiga ya saka kayan bachi kama jikinta abun ka da silk material, bata saurareshi ba ta cira kafa ta fara takawa tana fadin.
“Idan baka son ganina a gidanku zan iya tafiya wani gurin amman ba sai ka kashe ni ba”
“Ban yi domin na kashe ki ba, kawai dai raina ya bace ne”
Ya biyo bayanta sai dai yayi iya kokarin da zai yi ya hana idonsa kallon abun da ba halalinsa ba, har suka fito daga Garden din, sai da ta kusa isa kofar falon sannan gabansa ya koma faduwa saboda abun da Ummi zata ce bayan ta ja masa kunne akan dauke idonsa daga ganin alakar Waira da Ameer.
“Waira can you please tell Ummi ruwa kika fada na je dauko ki?”
Yana kokarin cire rigarsa ya fadi haka, sai ta juyo ta kalleshi a kokarin na mamakin yadda yake son boye abun da yayi ashe ya san ba abu ne mai kyau ba kenan kokarin kasheta. Sai dai ta manta da duk wani tunani da take a lokacin da ta yi arba da kirjinsa dake dauke da tarin kwarzantaka da kirar cikaken namiji matashi mai jini a jiki kamar shi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.