Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 196 of 227
MALEEK POV.
Sai da rana ta fara haskowa sannan Maleek ya kwanata a inda Nuwaira ta tashi ita kuma ta fito waje ta zauna tana shan ranar tana taba wuyanta har lokacin ciwo yake mata, tun kamin aje ko'ina ta fara missing din gidan Ummi.
Juyawa ta yi a hankali ta kalli Maleek dake bachi sai tausayinsa da kaunarsa suka kama ta wanu be taba gwada kare lafiyarta kamar shi ba, gwadawar da zai jefa rayuwarsa a cikin hatsari saboda ita, be damu da rashin kyau dakin va ya kwana a haka, kuma ta taya ta gyara dakin be nuna mata kyama ba, wani abun da yake burgeta da shi be taba gwada taba jikinta ba sai a lokcin da ya ceto a ruwan swimming pool sai kuma ajiya a kokarinsa na kareta daga danginta. Taba ta da ake da dare ma tana zaton shi ne a yanzu ta gane ba shi ne ba, sakamakon mafarkin da ta yi jiya.
Murmushi ne yayi ma kansa muhalli a fuskarta a yayinda idanuwanta suka kallon fuskar Maleek da be san tana yi ba domin bachi yake yi mai nauyi na ranko bachin da be samu yi ba da dare. Jin alamar takun tafiyar mutane ya saka ta dawi da dubanta gurin hanyar shigowa sashenta, tawaga ce daya ta sarki tare da wasu manyan mutanen da ta san su a fadar sarkin.
Da sauri ta mike tsaye gabanta na faduwa wata zuciyar na raya mata taje ta tashi Maleek ta dayan bangaren kuma tana jin tsoron ko Maleek din suka zo cutarwa. Kamin su karaso gurin Maleek ya farka da sauri kamar wanda aka sanarna a mafarki ya fito waje da sauri ya tsaya kusa da Nuwaira.
“Su waye?”
“Daga fadar Sarki suke, ban sani ba ko wani abun za su yi maka”
“Ko kuma ke ba, kar su ce za su dauke ki ko su cutar da ke”
“Idan ni ce abun da sauki, kai ne da ba zan so su cutar ba”
Mutanen ba su yarda sun karaso kusa da inda suke tsaye ba suka ja daga suka tsaya, daya daga cikin zaratan jaruman fadar masu hidima wa Sarkin Garin ya matsa gaba kadan ya fara magana da Nuwaira da yarensu.
“Sarki ne ya aiko tawaga ya ce a taho tare da ke da bakonki yana son ganinku a fada”
Nuwaira ta juya kadan ta kalli Maleek dake gefenta.
“Sarki yana son ganinmu”
“Fada masa zamu tafi bari na dauko wayata”
“Ya Maleek idan kuma cutar da kai zasu yi fa?”
“Babu abun da za su yi min, duk abun da kika ga ya same ni to daman can an rubuta zai same ni ne, amman babu wanda ya isa yayi min wani abu sai da amincewar Ubangijina, ni kuma na yarda da shi ba zai taba bari a cutar da ni ba, ki amsa musu kawai zamu zo”
Yana maganar tana hawaye ganin take ya kasa fahimtar manufar, bayan kuma ta san waye Sarkinsu kuma ta san su waye jama'ar garin, ko da ka kyautata musu idan kai ba dan garin ba ne za su iya cuta maka balle kuma ace ka munana musu ka karya dokokinsu.
“Idan ina ganin hawaye a idonki kina karya min guiwa ne kawai, ba zan ma dauki wayar ba mu tafi”
“Ya Maleek”
Ya aika mata da wani irin sihirtaccen kallo cikin kwayar idonta da ya hana ta karasa kiran sunansa ma balle kuma ta dora da abun da take da kudurin fada. Shi ya fara takawa ganin haka ya saka dole ta cira kafa suka fara nufar mutanen a tare, tawaga jama'ar Sarkin suka yi musu wasu a gabansu wasu baya wasu dama wasu hagu, jama'ar garin da suka fara hada hadar safiya suka fito sai kallonsu suke, wasu kuma daga cikin gida suke fitowa suna kallonsu, ita dai gabanta sai faduwa yake, Maleek kuma ya dagewa zuciyarsa duk wani tsoro ko fargaba ya bar shi a cikin zuciyarsa bakinsa na ta karanta addu'ah har suka isa fadar.
A zahiri ya san Sarautar domin shi ma jikan Sarki ne, hakan ya saka shi yin ladabi ya cire talkaminsa tun kamin su shiga fadar, sannan yayi bismillah ya nasa kafarsa cikin katuwar fadar da aka kawata da fatar farar daminsa, kujerar kuma aka yi da fatar zaki aka dora kan Zakin saman kan kujerar dama da hagu na kujerar kuma kanun manyan macizai ne daga inda Sarki zai dora kafarsa kuma kunamu ne da ka tsafe aka hade su guri daya aka busar da su aka yi ma Sarkin gurin dora kafa. Babu annuri babu far'a babu sakewa da walwala a fuskar Sarkin da ya kwana biyu har tsufa ya fara cin karfinsa, sandar sarauta ce a hannunsa wasu zaratan jarumai suna tsaye dama da hagu suna masa fita, kujeru da aka jesa a fadar suna cike da masu rike da Sarautu a garin, daya bayan daya Nuwaira ta bisu da kallo har idonta ya sauka a kujerar da ake aje mata ta tsafi abun da ta yi arba da shi ya bata mamaki matuka Eid ne zaune a kujerar shi ma fuskarsa a hade take babu alamar ya taba dariya babu imani da tausayi a idonsa Maleek kawai yake yi ma mugun kallo na fitina. Sai da suka iso tsakiyar fadar sannan suka tsaya mutanen da suka yi musu rakiya kuma suka matsa daga gefe aka bar Maleek da Nuwaira tsaye suna fuskantar Sarki.
Cikin halshensu Sarkin ya fara magana da Nuwaira.
“Kin karya dokar da muka saka miki, kika gudu kika bar garin Garuk, bayan kuma kin san hukuncin da muka shai'anta miki idan har kafarki ta bar garin Garuk me yasa kika gudu”
“Saboda na tsorata a wacan lokacin, kuma ban shirya karbar hukunci akan laifin da ban aikata ba, ba ni na kashe mutumen da kuka zargina da kashewa ba, haka kuma ban shirya karbar Sarautar da kuke cilasta dole sai kun ba ni ba”
“Kin gudu kin tafi a gurin mutanen da suka fi mu tsafi da iya sarrafa aljanu saboda su baki kariya daga garemu, kin watsar da al'adarki da addininki kika dauki ta su. hakan be wadatar da ke ba har sai da kika gayyato daya daga cikinsu zuwa cikin garinmu, ya karya mana dokoki ya ci mutumci yayi fada da jininmu akan wani dalili”
“Ku kuka kira ni, Eid kuka aika har cikin gidan da nake rayuwa tare da mutanen da na dauka a matsayin dangina, gashi nan be fada muku ba?”
“Mun tura shi ne kawai saboda shi kadai ne yake iya sarrafa kansa ya shiga cikin gidan da kike, babu kalar tsafin da ba mu aika miki ba, amman ya kasa samunki saboda kina cikin gidan da tsafinsu ya dara na mu, daga lokacin da kika gudu na kira taro na sanar da duk wanda ya kamata ya sani ya dauke mu kwana hudu kamin mun hanke shawarar abun da zamu yi, daga karshe muka cin ma matsaya akan kasheki, amman Eid ya tsaya kai da fata wajen ganin kin rayu, babu kalar azabar da ba mu yi masa ba a lokacin da yake ziyartarki a haka ya jure, muna daf da yafe ki ya bukaci a dawo da ke ko da ba za a baki Sarautar ba, sanadin guduwar da kika yi ya saka mun sauya sarautar tsafinmu ta shekara da shekaru, a dole muka yi mata garanbawul daga karshe aka cin ma matsayar baiwa Eid Sarautar, hakan ya kara masa kima da daraja a idonmu, shiyasa har ya roki mu dawo dake a cikin garinmu kuma muka saurareshi”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.