Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 80 of 227
“Kar wanda ya bari ta sake fita a gidan nan”
Waira na ganin zai saukowa ta yi saurin guduwa ta boya bayan kujera jikinta na rawa gani take kamar ita aka yi ma jina jina a jiki, a zatonta Abiey ne yayi ma Nimra wannan dukan daya canja mata kammanin. Tsoron kar ya hukuntata da laifin data aikata a dazun ya saka ta fashe da kuka tana rufe bakinta, dazun ma ba karamin fada yayi mata ba balle kuma yanzu da ya doki yarsa ita ma zai iya dukanta. Namra ta rika Ummi ta karasa shigowa falon ta zaunar da ita saman kujera.
“Ummi are you okay? Please kar ki saka abun da Nimra ta aikata a ranki”
Ummi ta juyo ta kalli Mahmood dake maganar tana kallonta cike da kulawa. Ta lumshe ido ta bude so take ta cika rokon da ďanta yayi mata na ganin ta bawa Nimra kariya.
“Je ka fito min da Nimra”
“Amman Ummi ba zaki hakura har zuwa anjima ba?”
Ta girgiza masa kai. Sai ya mike tsaye ya nufi upstairs ya tura kofar dakin Nimra ya shiga, kwance ya same ta a kasa tana kuka kamar ranta zai fita.
“Ta so Ummi tana kiranki ita ma kin saka ta kuka idan haka shi ne burinki, sakamakon da zaki yi mata kenan”
Nimra ta dago ta kalli Mahmood ta koma ta kwanta ita kadai ta san abun da take ji a zuciyarta, ganin ba zata tashi ba ya saka ya iso gurin ya rika hannunta yana janta da karfi domin shi ma a yanzu haushinta yake ji, sanin zata wahala ya saka ta fara rarrafe tana bin bayansa daker da sauko downstairs din, sai dai wani abu mai kama da kunya da jin nauyi ya hanata karasa inda Ummi take zaune, Maleek ya gurin dinning tsaye ya rumgume hannayensa yana harararta kamar zai cire.
“ƴa ta taso mana”
Ummi ta fada kamar ba komai tana kallon Nimra, kalaman da Ameer yayi mata a dazun ya dawo mata da tunanin rayuwarta ta baya, a yanzu tana iya fahimtar halin da Nimra take ciki. Bacin rai ya saka Maleek da Mahmood bari falon, sai Namra ce ta tashi ta riko hannun yar'uwarta tana kuka ta kawo ta gurin Ummi, Ummi ta rika kanta ta kwantar a kan cinyarta.
“Ya isa haka, wannan kuka ya isa Nimra ki kwantar da hankalinki ki saka ranki a inuwa, komai zai wuce kin ji? Karki sake kokarin guduwa ki bar ni saboda wani, kina tunanin uwa zata rayu idan babu yayanta a kusa? Ke kika da saurayi kika kasa jurewa balle ni da na haife ki? Kamin ki aikata wani abu ki rika tunawa da Umminki, kuma kin ga da acw guduwa abun kirki ne da wannan saurayin na ki be barki kin dawo ba, bude baki ki yi ta Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, ki yi sallah ki fadawa Allah damuwarki ki roki sasauci da zabi na alheri, Abiey zai sauko amman dole ne a yanzu sai yayi fushi sosai kin ji”
A hankali ta daga kai tana jin kaunar Ummi a ranta da kuma tausayin kanta.
“Kalli yadda kika saka ni kuka ni da yar'uwarki, karki sake yin haka kin ji? Ke musulma mai tarbiya, na yardar ba ki watsar da tarbiyar da na baki ba, tun da har baki bashi mutuncin ba, yadda kika oya yakar zuciyarki ta hana ki aikata zina, ya kamata ki yake ta ta hana ki batawa iyayenki rai, domin bacin ran iyaye yana tare da fushin Allah, idan kika bata mana rai ko da kin gudu kin tafi wani gurin ke da ahi ba zaku taba ganin haske ba, amman idan kika bi komai a hankali sai a samu maslaha”
Ummi tana fadar tana shafa kanta, kamin ta kalli Namra ta ce.
“Je ki kira Maleek ya zo ya bata magani”
Namra ta share hawayenta ta mike tsaye ta fice daga falon zuwa gurin nemansa a wajen bangaren Ummi. Ummi ta kalli gefen kujerar da Waira ta boya ta ce.
“Baby Waira Yata fito mana me kike yi ma buya? Wa kike tsoro”
“Abiey...”
Ta fada daga can inda take boye.
“Abiey ya tafi bangarensa Umminki ce kadai a nan sai yar'uwarki Nimra fito”
Ta fara lekowa ta karewa falon kallo ta ga babu kowa sai Ummi da Nimra sannan ta fito da sauri ta nufi gurin Ummi ta zauna a kasa dayan side din da Nimra take zaune tana kallon Nimra da idonta yake rufe tana zubar da hawaye.
“Kalli wacce ta rasa iyaye da yan'uwa da abokai da gari, ta rasa abinci da masu jin kalar yarenta ta bata mutu ba ta rayu tare da mu, sai ke ce zaki mutu dan kin rasa saurayi? Karki bari shaidan ya sharin zuciya su rinjaye ki Nimra”
Nimra ta bude ido ta kalli Waira take leken fuskarta, murmushi karfin hali Nimra ta yi mata sai Waira ta saka hannu ta fara share mata hawayenta, ta mika hannunta ta kama hannun Nimra ta rike ba dan komai ba sai dan ta san abun da yake faruwa, ta kwanatar da kanta a jikin Ummi kamar yadda na Nimra yake kwance. Ummi ta girgiza kai tunanin Ameer da kalamansa sun hanata sukuni, furucinsa na cewar saboda be san dadin uwa ba shi ke nuna be san muhimmancinta ba ya matukar tsaya mata a rai. Me aka fada masa? Uwarsa ta mutu? Shigowar Maleek ya saka ta share hawayenta ta kalleshi sa'insar da sukayi a dazun da Ameer take ta gani a idonta.
“Treatment zaka mata ka bata maganin da ya kamata”
“Ban taba mata treatment ba”
“Ka fara daga yau, kuma ban ce ka fada mata ko da kalma matar dadi ba balle har hannunka ya sake kaiwa a jikinta, Namra rikata ku tafi dakinta ki hada mata ruwa ta gasa jikinta zan hada mata wani abun ci a yanzu”
Ummi ta karasa tana kallon Namra wacce ta amsa mata da kai ta rika yar'uwarta suka mike tsaye. Waira ta bude ido da sauri tana kallon Nimra.
“Ta sanshi i know him... Waira ta san shi ta gane shi ta san shi”
Haka take ta fada da sauri tana nuna Nimra, daga Ummi har Maleek dake tsaye ba su fahimci abun da take nufi ba, Ummi kuma bata da lokacin tsayawa ta fahimceta a yanzu balle har ta gyara mata abun da take furtawa. Da ido Maleek ya harare a tunaninsa zata fara ba bada labarin abun da ya faru a school dinsu ne a yau, sai ta yi tsit kamar bata gurin.
“Bari na je na siyo magani”
Maleek ya fada sannan ya juya ya koma ta kofar falon da ya shigo. Waira ta bi Nimra da kallo har sai da suka haye sama gaba daya sannan ta dauke idonta ta dawo da su gurin Ummi.
“Ummi...”
Ummi ta kalleta wasu hawayen suna tarar mata a ido.
“Ummi miyasa Ummi ba zata bari Nimra ta aure shi ba”
“Saboda wani abubuwa da yawa tashi ki je ki cire uniform dinki”
Ta tashi ta nufi upstarts, sai kuma ta juyo.
“Ummi... Meyasa Ummi ba zata fadawa Abiey tana son mijin Nimra ba?”
Ummi bata bi ta kan maganar ba, domin tana cikin damuwa a yanzu.
“Na ce ki tafi ki canja uniform dinki”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.