Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 130 of 227
“Da hannu yafi dadi mu bama ci da spoon”
Maganar Waira ta fado, masa sai ya aje spoon din a muhallinsa ya zari tissue ya saka ya dauki cake din yana ci. Sai da ya ci kusan rabi sannan ya rufe mata saura ya saka mata a jakarta ya aje jakar gefe ya kwanta jikin kujerar yana sauke ajiyar zuciya, duk wata magana da Waira ta yi masa sai da ta dawo masa a lokacin, ta fada masa kusan abun da mahaifinsa Mr Bashir ya fada masa amman be fahimta ba sai a yanzu. Bude motar yayi ya fito nufi cikin asibitin, ya isa Emergency ya nufi dakin da aka ya barta sai ya tarar wasu ne ba ita ba. Nurses din dake gurin ya tambaya ta fada masa cewar an canja mata daki. Wani ta saka yayi masa jagora har dakin da aka maidata, Mutumen na nuna masa dakin ya juya yayi tafiyarsa. Ameer ya kalli room number din dakin sannan ya murda kofar ya shiga, first abun da ya fara arba da shi is Humairah tana tsaye gurin kan tsohuwar idonta yayi ja har ya kumbura, kana ganinta kasan ba kadan ta yi kuka ba. Tsayawa yayi yana kallonta da mamaki ita ma kallon mamaki take masa, Mamarta kuma ta mike tsaye tana kallonsa domin ta gane shi ne mai gidan yarta Humairah ta rike fuskarsa tun a ganin farko da ta yi masa, shi kam ba dan ganin Humairah ba da ba zai iya shaidar fuskokinsu ba daga ita uwar har kakar.
“Me kik.... Kakarki ce?”
Ta daga masa kai.
“Kai ka kadeta?”
“It wasn't intentionally, zan wuce ne ita kuma zata je karbo sadaka”
Ya karasa gurin gadon.
“Ya jikinta?”
“Da sauki amman har yanzu bata dawo hayyacinta ba”
“Ba zata dawo hayyacinta da wuri ba, tana bukatar lokaci”
“Ina wuni ranka ya dade”
Mahaifiyarta ta gaishe shi kamar zata risina.
“Lafiya kalau”
Ya amsa yana jin wani iri. Sannan ya kalli Humairah ya ce.
“Za'ayi muku komai a nan, zan tafi gida yanzu anjima kadan za a kawo muku abinci tare da kudi ku siye wani abun, kuma idan akwai abun da kuke bukata ki sanar da ni”
“Okay”
Da ok kawai ta amsa mahaifiyarta ta dora da godiya da addu'a, shi kuma ya juya ya fice bayan yayi ma tsohuwar fatar samun sauki. A lokacin da yake kokarin bude motarsa ya shiga ya ji muryar Humairah bayansa.
“How are you Ameer?”
Ya juyo ya kalleta.
“I'm fine”
“Ban ga haka a fuskarka ba”
“I will be fine”
Ta rumgume hannayenta.
“Ka yi magana da ita?”
“No maybe tonight idan zan kai jakar Waira”
“Who's Waira?”
Ya daga kansa yana kallon harabar gurin.
“Wata yarinya ce mai kyau fuska da kyakkyawar zuciya, ta iya kyautata lafazi, gata da jan hankali, abar tausayi ce kuma abar so, abar kulawa full-option ta hada komai, and someone has never been in her heart”
“I'm sorry Ameer. It since like ka yi saurin warkewa daga abun da ka yi ma Nimra. With due respect Ameer baka canja ba”
Ya matso kusa da ita.
“I canja Humairah kuma zan canja, shiyasa nake son na kyautatawa mata i won't break her heart, ba zan bari wani ya cutar da ita ba, she's the kind of girl I'm looking for, not just her zan kyautatawa kowa gwargwadon ikona, domin na fahimci ni ma alfarma nake ci”
Ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani abu marar dadi ya tsaya mata a makoshi.
“Who's knows who my family is? Wace kalar rayuwa suke? Su waye su? Mutanen kirki ne ko na banza wace kalar rayuwa mahaifina yayi ban zani ba, kamar yadda Waira ma bata san waye mahaifinta ba, banbancinta da ni, ni ina da Daddy da Ummi a yanzu, ita kuma bata da kowa”
“if you want to change you should start from within.... Ina fata kuma ina kyautata zaton mahaifinka mutumen kirki ne wish you all the best”
Ta karasa tana murmushin karfin hali.
“Thank you”
Ya amsa sannan ya saka key din ya bude motar ya shiga. Tana tsaye a gurin har ya bar asibitin. A hanya ya tsaya yayi sallah sannan ya kama hanyar gida. Yana isa ya cire jakar Waira ya saka a wata motar ya mikawa mai kula da motocin gidan key motar da ya dawo da ita.
“Ka wanke ta da kyau akwai jini a ciki, na kade wata mata ne muka kaita asibiti”
Jiki na rawa mutumen ya saka hannu biyu ya karba, yana mamakin yadda Ameer yake masa bayanin abun da ya faru, abun da be saba ba, ko da mutum zai bude ya gani a motar ba zai fada masa ga abun da ya aikata ba, shi a gidan babu mai jindadinsa dukansu suna zaune ne kawai saboda Mr Bashir yana kyautata musu kuma yana musu albashi mai tsoka. Ya shiga cikin falon cikin wani yanayi mai wuyar fassara, Mummy dake tsaye rike da remote ta kalleshi.
“Ameer ka dawo”
Ya kalleta, a lokacin da yake ďan iskan gari bata isa ta yi magana ya amsa mata ba sai ya ga dama, har ganin yake kamar sa'ido take masa tana masa munafurci a gurin Daddy, amman yanzu wannan duk ta kau.
“Eh”
Ya wuce sai kuma ya juya.
“Na kade wata mata by mistake amman na kaita asibiti, please ina son ki saka masu aikin gidan nan su zuba mata abinci, zan yi ma musa text din inda take da kudin da za a bata sai yaje ya kai musu”
“Subhanallahi amman dai baka ji ciwo ba ko?”
Ya amsa mata da kai.
“Matar da sauki?”
“Da sauki ina tunanin karaya ce”
“Allah ya sauwake, ya tsare gaba please Ameer ya kamata ka rika kula idan kana tuki, kuma ka rika sassautawa zuciyarka”
Sai da yayi kamar ya tsaya yi mata bayanin ba da gangan ya kade ya ba, it's not his fault sai kuma ya juya kawai ya nufi stairs.
[7/17, 6:21 PM] My S Line: 53
Around 9:11pm Waira tana zaune kan carpet tare da pen dinta, liffatinta na lessons na gabanta ta dora jakar a kan kujera. Baby rabbit dinta ta dora kan littafin tana zanawa kamar an sakata.
Namra na zaune kam 3 seater tana lasar wayarta. Maleek kuma na zaune a dayan side din falon rike da mug hannunsa daya kuma rike da wayarsa, sai ko kadan hankalinsa ba shi a gurin wayar ya tafi gurin abokiyar fadansa Waira dake zane, ba ya iya hangen zanen da take, but he found himself looking at her, ko wane motsi da nata yana kan idonsa. If ba dan kar na yi karya ba da sai na ce har yadda yake fita da shigar numfashinta yana kallon yake yana kan idonsa. If wani zai tambaye me yasa yake kallonta ba zai iya fada ba, maybe ko dan ita ce mace ta farko data fara bude masa ido har yake son kallonta ko zama kusa da yan'uwanta, zai kuma fi yarda idan aka ce saboda kyaunta ne domin tana da kyau daidai yadda ko ita ta tsara kanta iyakar abun da zata yi kenan. Everything about her is unique her hair, dress, her talk the shagwaba part and even her talk yana jin fadi muryarta when she's talking about something. Yana ganin Ummi ta fito daga kitchen sai yayi saurin dauke idonsa daga barin kallonta ya maida dubansa kan wayarsa. Ummi ta dire mata copy tea
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.