Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 140 of 227

Ta zaro ido tana mamaki.

“Daman bayan mutuwa ana sake tashin mutane?”

Ya sake kai mata spoon din abincin a bakinta.

“Kwarai da gaske, a addininku ba a fada muku ana sake tashi ba?”

“Aa a addininmu ba a sake tashi idan an mutu”

“Ba gaskiya ba ne, idan ba a tashi to taya zaka kwatarwar wanda aka zalunta hakkinsa? Ta iya za a saka maka da abun da ka aikata na alheri? Mutanen da suke zaluntar ka ta ina saka musu da abun da suka yi? Ibadar da muke a kullum ko a wata ko a shekara ta ina za mu sakamakonta?”

A nan ya yi nasarar dasa mata wani tunanin, domin a can da bata yi tunanin idan wani ya zalince ka ba za a sake tashinsa a kwatar maka hakkinka.

“Ai tun da can da ke kinsan babu ki, aka hallince ki, to ko kin san zaki mutu kuma dole zaki jira sakamakon abun da kika aikata”

“Mu sau daya muke bauta a shekara”

Ta fada tana sake bude baki ya zuba mata shimkafar da cinta ya zame mata kamar dole.

“Kin ga mu kuma kullum muke ibada, sallah sau biyar a rana, ta wajibi kenan, ban da ta nafila, ga sadaka ga kyautatawa, a cikin ibadu azumi da hajji ne kawai ake yi shekara shekara, shi ma akwai na nafila da zaka iya yi a wata ko a wasu ranaku da aka kebe mana, ga kuma karatun Qur'anen da Annabinmu ya kawo mana”

“Wanene Annabinku? Minene Qur'ane?”

“Karatu mai tsayi sosai, amman dai zaki san komai tun da muna tare a yanzu”

“Ina son na sani, addininku yana da abubuwa da yawa”

“Sosai ma kuwa”

Ya fada yana jan karan hancinta, sai ta yi dariya ta saka hannu biyu ta dauki tea ta sha. Kamin ya dago kanta ta kalli Ameer da ya mike tsaye yana shafa kanta.

“Kin ga a addininmu ba a yarda mace ta bar jikinta a bude ba, ko da kuwa gashin kanta ne, ana son ta bayyana adonta ne kawai ga mijinta”

“Saboda me?”

“Idan kika je siyen minti a shago da wanda aka rufe a cikin leda da wanda aka bari kuda ya taba yayi datti wane zaki zaba?”

“Wanda aka rufe”

“Toh haka mace take, tashi mu tafi”

Ta mike tsaye, sai ya haura sama ya sanarwa Mummy zata tafi, sai gata ta sauko da ledar turare kusan kala hudu ta bawa Waira.

“Ga wannan, kin san mace yar kamshi ce”

A nan ma Waira bata karba ba sai da ta kalli Ameer yayi mata alama da ta karba sannan ta karba ta wuce gaba.

“Allah ya sanya alheri”

Ameer ya bude ido yana murmushi.

“Mummy baki yarda ba kenan”

Kamin Mummy tace wani abu Fiyya ta fito da mayafinta.

“Zan bika mu tafi na ga gidan”

“Wa zai dawo da ke?”

“Yeah daman ina son naje da motata kuma gashi na zo da motar Ummi, so kija min motata zan shiga ta Ummi sai muje ki ga gidan, in ya so direba sai ya dawo da ita”

“Okay”

“Yeeeee Mummy sai na dawo”

Fiyya ta yi gaba abunta. Sai da Ameer ya shiga dakinsa ya dauko key din motar sannan ya fito ya bata key din shi kuma ya shiga motar Ummi. Waira ta juya ta kalli dan karamin akwaitin dake back seat ta kalli Ameer da ke juya kan motar ta ce.

“Sukenan kayan da zaka dauka daman?”

“Eh ai ba tufafi zan dauka ba, wasu abubuwan da nake son amfani da su zan dauka, idan mun je gida zan yi Order sabon tufafin da duk wani abu da zan yi amfanin da shi sai a kai min a can”

“Okay kana da kudi shiyasa amman kana aiki ko?”

“Aa bana aiki, ni zan zaman banza ne, shiyasa nake son zama a gurin Ummi saboda na samu kudin”

Ya fada yana murmushi da yafi kama da dariya saboda fitar sautin murmushin.

“Ummi zata baka mai yawa kuwa bata da rowa, tana da yawan kyauta”

“Haka addininmu ya koyar da mu....”

Muhimmanci kyauta da sadaka yayi ta fada mata, da kuma falalarsa har suka isa gidan Ummi. Kamin su shiga gidan gabanta ya soma faduwa tunawa da Maleek da ta yi. Horn yayi aka bude masa gate ya shiga ya faka a compound din gidan, Fiyya ta faka a gefensa tana karewa harabar gidan kallo daga cikin motar da take zaune. Maleek na zaune a one of set din kujerun da suke Entrance din rike da waya hannu, yana sanye da kananan kaya mug a center table. Kallo daya ya yi ma motarsu ya dauke ido be sake kallon inda suke ba, har iso gurin Ameer ya bude ma Waira kofar falon ta shiga tana matsar hannu kasa kasa take satar kallon Maleek har ta shiga, sannan shi ma ya shiga. Fiyya ta iso gurin tana kallon Maleek da be san ma da wanzuwarta a duniya ba, kallonsa kawai take har ta isa bakin kofar falon, kyaun nan nasa mai daukar hankali da kuma kamshin turarensa mai jan hankali ya hana ta wuce ba tare da mika masa gaisuwa ba.

“Sannu ina wuni”

Ya dago ya kalleta daga sama har kasa ba tare da amsa ba, ya maida kansa kasa ya cigaba da abun da yake. Ta dan bude ido.

“Shi kuma haka yake?”

Ta fada murya kasa kasa sannan ta tura kofar falon ta shiga da sallama Ummi ta dago tana amsa mata fuskarta da annashuwa.

“Lale marhabun da zuwa”

Ameer ya kalli Waira dake nunawa Ummi perfume din da Mummy ta bata ya ce.

“Waira kin san ma'anar Sallamu Alaikum da kuma Wa'alaikassalam?”

“Aa me yake nufi?”

“Peace be upon you, Wa'alaikussalam kuma peace be upon you too”

“To meyasa ake cewa haka?”

Ameer be amsa mata ba ya kalli Ummi ya ce.

“Ummi duk tsawon zaman da ta yi a gidan nan ne bata san komai akan addinin musulunci ba? Baki zaunar da ita kin fada mata matsayi da martaba ta addinin musulunci ba, da irin aminci da natsuwar da yake da shi?”

Kalmar Ummi da Ameer ya kira Ummi da ita tafi komai yi mata dadi, ba yau ne karon farko da ya taba kiran sunan ba, sai dai a yau ne ya fara kiran sunan cikin girmama sa karamci, ya kirata kai tsaye kamar yadda sauran yayanta suke kiranta sai kuma ya dora da bayanin abun da ya kara mata kaunarsa wato son addinin da kokarin ganin Waira ta koya.

“Ni uwace ina da abubuwa da yawa a gabana, shiyasa ban maida hankali akan haka ba”

“Cika uwa yana nufin kula da yaya har ta bangaren addininsu, nauyin Waira yana kanki a yanzu kamar yadda kika fada”

“Yana kam mu gaba daya”

Ta gyara masa zancensa na karshen, sannan ta kalli Fiyya ta ce.

“Ya Mamanki take?”

“Lafiya kalau, tace a gaisheki”

“Ina amsawa, Ameer na gyara maka dakinka da kaina, amman ban sani ba ko akwai abun da ba zai burgeka ba, zaka iya min magana a gyara”

“Bari na duba”

“Waira wuce ki kaishi dakin dake kusa da nawa”

Waira ta wuce gaba Ameer ya bi bayanta Fiyya ma ta rufa musu baya. Sun dauki lokaci a dakin yana duba abubuwa, be dauka sabon furniture Ummi zata zuba masa ba, amman ga mamakinsa sai ya ga har tawul da bathrobe duk sabin Ummi ta aje masa, hakan kuma ba karamin faranta ransa yayi ba. Ya sauko yana magana da Fiyya yayinda aka bar Waira a dakin tana kara duba wasu abubuwan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.