Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 76 of 227

“Ya ji wata yar iskar yarinya yaushe kika san Ameer din ma, da zaki fada min haka? Okay idan har Abiey zai yarda ki aureshi ko Ummi sai ki aureshi din, amman idan suka nuna basa so, ba zaki aureshi ba, ki rubuta wannan ki aje”

Ya mike tsaye ya juya.

“Saboda baka san me ye so ba Ya Maleek, aure zamu yi ba zaman banza ba”

A fusace ya juyo ya daka mata tsawa.

“Yanzu me kuke yi? Ke ce baki san waye Ameer ba Nimra amman ni na san Ameer in and out, na san abun da zai iya da wanda ba zai iya ba, da ace sonki yake da gaske, da ya sauke gabar da yake da ni dan shi ne ba shi da gaskiya, amman a halin yanzu Ameer ya bata da duka friends din mu saboda ni, idan na zauna a guri Ameer ba zai sake zamansa ba, idan na gaisa da wani Ameer ba zai sake magana da shi ba, taya zaki kalli idona ki fada min cewar Ameer da gaske yake son ki? idan ban soyayya ba ai na san hankali da tunani, don't you think yana amfani da ke ne kawai saboda ya bata min rai? Ameer baya yafiya, Ameer baya aje burinsa saboda wani, ba ya kashe kansa saboda wani ya rayu, ya sani duk ranar da na san yana soyayya da kanwata zan yi bakinciki wannan ma kadai abun farinciki a gurinsa, and i know one thing for sure Nimra, Ameer ba zai ajeki a gidansa for more than one year ba tare da ya taba ki ba, ko dan kasancewar ki kanwata zai aikata miki komai, and bari na fada miki wani abun da baki sani ba, Ameer yana da mistress ya ajeta a wani gidan na dabam you're not the only one wannan kadai be isheki abun kunya...?”

“Ameer ba shi da kowa sai ni, kuma ni Ameer ba taba min komai ba, saboda so na yake da aure, baka fahimce ba ne Ya Maleek, ka bude zuciyarka ka zuba mata tausayi da soyayya, ka zahilci so...”

Da mugun mamaki Maleek yake kallon.

“Ina fada miki gabas kina fada min yamma? Saboda an kyale ki?”

Baya son saka hannunsa dan haka ya nufi gurin Laptop dinta take ya fisgo carjar ya nufi Nimra da ita ya fara dukanta kamar an aiko shi, tun yana dukanta tana ihu har ta kai muryarta bata iya fita Ummi kuma ta saka fitowa ta ceceta sai nata kukam take a dakinta tana sauraren muryar Nimra. Waira ce ta hau sama ta tsaya bakin kofar ďakin Nimra tana buga kofar da karfi, ba dan ta san abun da yake faruwa ba, domin shigowar kenan bayan ta ga ji da zama a motar da Maleek ya barta. Kamar wanda aka cewa ka yi ta dukanta har sai bacin ranka ya fita haka Maleek ya rika zunawa Nimra wayar carjar laptop din a jiki ido a rufe har kafarsa ya saka ya shureta, abun da be taba ba, ya kan doke su amman acan baya lokacin da suke shige masa hanci da kududdufi sai dai ba kamar irin dukan da yayi mata a yau ba.

“Do you know what? Da ina tunanin idan Abiey da Ummi suka amince zan goya miki baya ki aureshi, but yanzu na yanke hukunci ba zaki aureshi ba, sai kuma na ga yadda zaki yi, ki mutum na gani”

Ya karashe tare da kwafa sannan ya juya ya nufi kofar ďakin ya bude, sai yayi arba da Waira, ita ma ta yi arba da shi da bulalar wayar dake hannunsa, hannunsa dake rike da bulalar ta fara kallo sannan ta kalli fuskarsa dake hade kamar bakin hadari, a zatonta ya gama dukan Nimra ne ya fito ita ma yayi mata nata, sai ta kwala kara iya karfinta har sai da ya dafe kunnensa ya kauce daga gurin ya sauka kasa da sauri zuwa ya nufi bangaren mahaifinsa yana jin kansa na mugun sarawa, domin tana da ƙyaƙyar muryar irin wannan mai shiga har can cikin amon kunne. Ummi ta fito da sauri tana share hawayenta ganin Waira tsaye a kofar ďakin Nimra ya saka ta karaso da sauri, ganin Ummi ya saka Waira ta yi shiru domin a yanzu ta gama fahimtar babu lafiya a gidan, ganin Ummi ma tana kuka.

“Lafiya? Waya taba ki?”

“Ya Maleek ya dauki bulala zai daki Waira”

Ummi ta rika hannunta taja ta suka nufi ďakinta, hakan ya bata damar rumgume Ummi ta sauraren dalilinta na kuka.

NIMRA POV.

Maleek na fita daga dakin ta ji ihun Waira da kuma Isowar Ummi taja hannunta suka bar gurin ta san, Ummi ta ajeta a gefe kenan, ba dan haka ba da yanzu ta iso da gudunta a lokacin fa Maleek yake dukanta ta tare mata dukan har ma ta yi fada da Maleek din, amman gashi bata zo ba, sai da Waira ta yi ihu, furucin da Maleek yayi mata da kuma bacin ran da ta gani a fuskar mahaifinta, ya matukar daga hankalinta ya kuma tabbatar mata da cewar ba za su taba yarda ta auri Ameer ba, ita kuma a yanzu tana jin ta shiryawa mutuwa akansa, bata taba so ba sai akan Ameer wani namiji be taba shiga zuciyarta ta juyawa yadda yake so ba sai Ameer, dabam wanda be saba ba idan ya samu ba shi ma so da sauki, iyakar gaskiyarta tana nufin mutuwa idan har aka rabata da love of her life, bata ta inda zata rayu ba idan har iyayenta suka zabi raba soyayyar da Ameer. Daker ta tashi ta tsaye ta nufi inda ta nefar da key din mota da wayarta ta dauka idonta daya a rufe saboda dukan da Maleek yayi mata ya same ta a dayar idonta ne, bakinta na a kumbure yake har lokacin yana jinin naushin da Abiey ya kai mata a baki, bata ko iya taka kafarta da kyau sai dingishi take, ko'ina na jikinta tsami yake duk inda Maleek ya same ta da bulalar ya kumbura mata jiki, yayi mata ja. Idonta har ya canja kala saboda kuka har wani jiri take gani. Sai da ta fara lekowa ta ga babu kowa a saman sannan ta sauko nufo downstairs tana tafiya dake tana sauri ta sauka, kanta babu ďankwali balle ayi maganar mayafi, haka ta sauko falon ta nufi kofa ta fita babu talkami da faduwar gaba ta fito falon ta nufi gurin motar da Ummi ta bar mata tana hawa tun bayan da Ameer ya ci uban tata motar. Ta bude ta shiga ta yi mata key kamin ta yi reverse kamar zuciyarta zata fado ta ji, masu gadi na ganin ta kunna mota sai suka fara kokarin bude mata gate, kamin ta iso har sun gama budewar ta nan ta samu sa'ar ficewa da sauri tana wani irin gudu. Fita ta yi daga unguwar amman hankalinta be kwanta ba har sai da ta ganta a bakin gate din gidan Ameer, tana faka motar bata tsaya kashewa ba ta bude ta fito ba dan tana da tabbacin Ameer yana cikin gidan ba ta nufi kofar falonsa ta tura kofar tana budewa sai ta fadi cikin falon saboda babu kuzari a jikinta kanta ma kamar zai tsage gida biyu take jinsa saboda ciwon da yake. Ameer dake rike da gorar ruwa da waya a kunne yayi saurin yanke wayar ya aje ruwan ya nufota.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.