Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 70 of 227
βUmmi tace Waira ta zauna nanβ
Ta fada da sauri gudun kar yace ta masa laifi. Shi kuma sai ya amsa mata a ransa.
βKin ji nace miki wani abu ne?β
A zahiri kuma sai ya dauke idonsa daga barin kallonta ya cigaba da cin doyarsa, juyawar da yayi sai ya bata damar rama kallon sarkar wuyanta da yayi, sai dai ita a yanzu a fuska take kallonsa kamar wani hoto ko kyaftawa bata yi, ta gefen ido ya ga tana kallonsa kuma kallon ya kasa barinsa ya samu natsuwa har sai da ya dago ya kalleta, abun ka da wanda be iya munafurci ba sai ta kasa dauke idonta taga barin kallon nasa, idonta suka fara blinking babu tsayawa kamar marar gaskiya, can dabara ta zo mata sai ta rumtse idon gaba daya. Samun kansa yayi da murmushi a cikin zuciyarsa ya dauki ruwan dake gabansa ya sha ya ja kujerar baya ya tashi ya bar mata dinning din.
Ummi dakinta ta fara dubawa sai ta tarar har Dr Zainab ta yi bachi, gudun kar ta yi motsi mai karfi ta tasheta ya saka ta shiga a hankali ta bude bathroom ta yi wanka tare da wanke baki sannan ta fito ta dauko kayan bachinta ta saka ta fito tana ta kamshin turare. Dakin Namra ta fara budewa ta leka saita same ta ita kadai tana bachi, daman can ta san Namra ba zata kwana da kowa a dakinta ba, idan har wani zai kwana akan gado daya da ita kara ta kwana akan kujera, ita dai bata son ta motsa ta ji wani a kusa da ita. She has so many rules and regulations na banza da take sakawa kanta just to be unique. Ac dakin Ummi ta rage ta ya janyo mata kofar ta maida ita a yadda take. Sannan ta nufi dakin Nimra abun ka da mai son jama'a sai ta same ta ita da Juwairiyyya suna kwance a gado daya, sai dai da alama Nimra bata shiryawa bachi ba, domin wayarta ta fado kasa hannunta kuma yana lilo a gefen gadon ga wutar dakin a kunne ba kamar Nimra da ta kashe nata ba. Ummi ta karasa ta duka ta dauki wayar sai ta ga missed calls biyu daga heart emoji guda uku, ga kuma wani sako a saman screen din wayar.
(π«ππ'π ππππ ππ πππ ππ πππππ πππ πππππ πππ πππ ππ π π πππππππ, ππππ π πππ πππ ππππ ππππ π πππ πππ ππππππ πππππππ πππππππππ, ππ πππ πππ ππ πππ ππππ ππππππ π π ππππ ππ ππππ ππ πππ π π ππππππ π ππππ πππ, π πππ'π ππππ πππ ππππ πππ πππ ππππ πππ πππ ππππ ππππππ π π ππ π ππππ πππ πππππ π ππππ)
Wani irin tashin hankali da fargaba irin na uwa mai Ζ΄aΖ΄a mata ne ya bayyana a fuskar Ummi, jikinta ya dauki rawa as well as zuciyarta dake bugawa, she can't believe ta ga sakon nan a wayar Ζ΄arta Ζ΄ar ma Nimra wacce zata rantse idan aka saka mata yatsa a baki ba zata ciza ba, a cikin sakon babu abun da ya fi daga mata hankali kamar inda yake cewa ta san kalar karyar da zata yi su hadu? Su hadu a ina? Ina suke haduwa? Why not ya zo gidansu idan sonta yake? Wani ta hadu da shi yake mata wayo haka? The hug and kiss part ma abun tashin hankaline, Nimra zata iya rumgumar wanda ba mijinta ba har ta sumbance shi? Bayan wannan sai kuma me? Ummi ta kalli Nimra dake sharar bachinta hankalin kwance bata san abun da ke faruwa ba. A hankali Ummi ta aje wayar a gefen gadon ta juya ta nufi switch din dakin ta kashe sannan taja kofar a hankali ta fice, gaba daya jikinta yayi sanyi, tunani kala kala ya fara zuwa mata har da wanda be kamata ta yi ba a lokacin, tafiya kawai take tana saukowa basa not knowing downstairs take saukowa har sai da ta ji Waira kira sunanta.
βUmmi ta shanye teaβ
Ta kalli saitin inda take ta sauke wani uban ajiyar zuciyata ta kai hannu ta dafa zuciyarta, tunanin mai kokarin gurbata mata tarbiya Ζ΄a take, kawa ta hadu ita marar tarbiya ko kuma saurayi? Amman idan kawace ya akayi bata san da ita ba a matsayinta na uwarta? Sai a yanzu take gane maganar da hawasa suke cewa mai Ζ΄aΖ΄a mata hannunsa a kirji yake har sai ya aurar da su, idan kuma ya aurar ba ya rufe Ζofa. Ta bawa Yayanta yarda 100% saboda tarbiyar da take ganin ta yi musu hakan ya saka wanin abun bata damuwa ta zafafa bincike kwakwaf akansu ba.
βWaira zo muje ki kwanta dare yayi sosaiβ
Waira ta taso ta nufo inda Ummi take sai Ummi ta rike hannunta suka haura sama, ta shiga da ita dakinta ta bude wardrobe ta dauko mata kayan bachi ta aje mata akan gado.
βShiga ki yi wanka ki yi brush zan jira ki a nanβ
βTohmβ
Ta nufi bandakin, Ummi ta zauna baki gado tana ta tunani kala kala, for how long alakarsu take da wannan mutumen waye ma shi? Mace ne ko kuma namiji, domin a yanzu a wane hali da mata suke neman mata yan'uwansu, maza ma su nemi maza yan'uwansu, miyasa ko da rana Δaya bata gabatar mata da shi a matsayin saurayinta ko wanda take son aure ba? Ita dai saninta a yanzu babu mai zuwa zance gurin Nimra kara ma can da ana zo jefi jefi amman ban da yanzu, balle ta yi zargi wani ne a cikin masu zuwan. Bata son ta munana mata zato hakan ya saka ta fara kokarin yakar zuciyarta ta kawar da abun a ranta. Waira ta yi wanka ta yi brush kamar yadda Ummi ta koya mata idan zata kwanta sannan ta fito ta saka kayan bachin Ummi ta nuna mata turare, sai ta nufi inda turaren yake ta dauka ta fesa a jikinta.
βBaby Waira kin san miyasa mai miki lessons be zo ba yau?β
βAa no aaβ
Ta fada har sau uku a kokarinta na bin umarnin Ummi na amsa mata da baki ba da kai ba.
βBe fada miki komai ba a jiya yace ko ba zai samu zuwa yau ba?β
βNo be fada mataβ
βMiniβ
Ummi ta gyara mata
βMini komai baβ
βTo zo ki kwantaβ
Ta hau ssman gadon ta kwanta gefe nesa da inda Yesmin take kwance, sai Ummi ta bude wani karamin kwando ta dauko safa ta saka mata a kafa.
βKin gani da ace addininmu kike yi sai na ce ki yi addu'a kamin ki kwanta, saboda ki samu tsari wani abu ba zai cutar da ke ba, mutum ko aljani ko wani Ζwaro mai cutarwaβ
Waira dai bata ce komai ba sai sauraren Ummi take, can kuma ta ja blanket ta lulluba, sai Ummi ta kai hannu tana shafa kanta tana ta tunani har bachi yayi gaba da ita, sannan ta tashi ta ja windows din dakin dake bude ta rufe ta kashe musu hasken dakin taja kofar ta fice. Da tunanin abun da ta gani a wayar Nimra ta kwana a ranta, har mafarkin abun sai da ta yi tana ta tunanin yadda zata bullowa abun. Hanne ta shirya abun karyawa da taimakon Ummi, bayab ta gama shiryawa mijinta nasa abun karin domin baya cin na masu aiki, sanin wannan ya saka ta rike wannan al'adar ta yi masa girki da kanta a kullum ko da kuwa ruwan tea ne.
Β Ya baro bangarensa ya dawo bangaren Ummi yayi breakfast tare da yar'uwarsa suna ta hiran baya, kowa da kowa yana falon ana karin safe idon Ummi yana kan Nimra she just can't believe ace Nimra ce aka turawa sakon jiya, ko da yake hausawa sun ce ka yi naka ka barwa Allah sauran, domin tarbiya a yanzu duk yadda ka yi sai idan Allah ya tsare maka kawai. Ita kuma Waira nata idon yana kan Ummi tana tunanin abun da ta gani jiya har yanzu zuciyarta cike da tausayin Ummi, Maleek kuma nasa idon suna kan Waira a sirrance kallon da take yi Ummi ne yake ba shi mamaki, da haka kuma wata ilar ta ja shi ya fara kallace surarta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.