Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 19 of 227

“Mu tafi gida yanzu?”

Ta daga masa kai, sai ya maida sarewar a cikin walkinsa ya shafa fuskarta da har lokacin hakoranta sun kasa rufuwa.

“Ba sauran fushi?”

Ta daga masa kai ta amsa masa da yarenta.

“Ache kur to”

_Babu sauran fushi yanzu_

“Surt ach tour nianor”

_Haka nake son ji kyakkyawata_

Har wani tsalle take suna takawa yana rike da hannunta, kallo daya yayi ma tufafin jikinsa ya dauke ido domin dattinsu yayi yawa kuma be isa yace mata ta wanke su ba, balle kuma yace ta yi wanka yanzu nan sai su fada, domin ta tsani tsabta ta tsani kwalliya kamar yadda ta tsani mutuwarta.
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*

_Na Khadeeja Candy_

8️⃣

Fitowa yayi bakin gate din gidansu, ya mike hanyar fita daga road din, ko sau daya be juyo ya kalli gidansu ba, not just gidansu even mahaifinsa ya fice masa a rai a yanzu tufafin dake jikinsa ma ji yake kamar ya cire su ya jefar saboda ya same su ne silar mahaifinsa da ya gama yi masa gori ya kwace komai nasa a yanzu.
Ya daukarwa kansa alkawari ko ba zai taba amfani da Atm dinsa ko mota da duk wani abin da ya san ta hanyar mahaifinsa ya same shi ba. Bacin ransa ya ninku akan Maleek zuciyarsa na raya masa komai akan Maleek akai masa, bayan shiga tsakaninsa da friends dinsa yanzu kuma ya shiga tsakaninsa da mahaifinsa.

“Sai na kashe yaron nan”

Ya furta yana jin kamar ace yana gabansa ya saka bindiga ya halshe kansa. Be taba jin tsanar Maleek irin wannan time din ba, duk wani abun dake shiga tsakaninsu be taba kaiwa kololuwa har haka ba sai tsakanin kwanakin nan ba ma kamar yau, da gangan ya daga tsaddadiyar wayar hannunsa kirar Samsung ya buga a kasa ya bita da kafarsa ta ya taka ya rika gurza ta akan titi ba domin komai ba sai dan ya siyata silar mahaifinsa, yana ayyana cewar sai mahaifinsa ya neme shi tun da har ya wulakanta shi har haka, he can't remember when last yayi tafiyar kafa mai nisa irin wannan har ya kai karshen road din be samu abun hawa ba, gashi ya fasa wayar balle ya kira wani daga cikin abokansa su zo su dauke shi duk da yana kallon haka a matsayin wani abun kunya. Unguwace da karamar mota ma abu ne mai wahala ka gani balle kuma napep ko taxi, shi kanshi ya san ya dauko ruwan dafa kanshi, domin tafiya ce zai ci cibi cibi, gashi be san inda zai je ba, garin zai bari? Ko kasar? Ko kuma wani hotel zai kama ya zauna domin vaya son rabar duk wani abu da mahaifinsa ya mallaka balle ya tafi daya daga cikin gidajen mahaifinsa, ko nasa ko ma kamfaninsa, kuma baya son kusantar yan'uwan mahaifinsa gudun kar a kira mahaifinsa a bashi hakuri.

“Hajiya Jamila...”

Ya furta a ransa, he's father Ex-wife, tana matukar nuna masa kauna a duk lokacin da ya rabe ta ko kuma ita ta rabe shi, wannan ya saka duk girman kansa idan yaje Kano sai yaje inda take, kamar yadda take yawan shigowa Abuja ta duba shi.... Sai dai zuciyarsa na raya masa idan yaje can din ma zata iya kiran mahaifinsa ta yi masa magana ko da ya hana ta, shi a yanzu yana son ya tafi inda be san kowa ba kowa be san shi ba, sai dai ya zai yi ya tafi? Ba tare da ya taba kudin da ya same su ta hanyar mahaifinsa ba? Shi ne abun da ya fi tsaya masa a rai, domin tufafin jikinsa ma ya matsu ya cire su balle kuma har ya sake taba wani abun.

Idonsa na akan titi da gidaje amman hankalinsa da tunaninsa ya tafi wata duniyar, sam be ga motar da ta tsaya a gabansa daman hausawa sun ce hankali ke gani ba ido ba, har Nimra ta kusa karaso kusa da shi jikinsa be bashi akwai mai kallonsa, sai dai kamshin turarenta ya dawo da shi daga duniyar da ya tafi ba dan ya tantance mai kalar kamshi ba sai dan turare ya zama wani bangare na rayuwarsa domin shi ne weak point dinsa no matter what happen.

“Hi Buddy”

Ya kalleta with Angry face kamar ita din ce ta yi masa laifi, a take murmushin daya fadada fuskarta ya bace bat kamar walkiya, cike da nuna damuwa ta lake fuskarsa, gushewar murmushinta ya saka shi jin wani iri domin ta zo gurinsa da farincikinta da gwarin guiwa, this is the first time da yaji yana damuwa akan abun da be takama ya damu da shi ba, kuma yana sakewa da abun da be hadade da haduwa da shi ba.

“Miya faru?”

Ya dan sake fuska sai dai ya kasa boye fushinsa, kuma ya kasa kallonta da idonsa dake bayyana bacin ransa karara.

“Alot”

“Zamu iya yin magana akansu?”

Tunani ya tsaya yi, sai ya ji ba zai iya yi mata garda ma ba, ji yake kamar ya dade tare da ita, kamar wata close friend dinsa haka yake jinta.

“Wait ina motarka ya kake tafiya kasa”

“Na bawa Daddy duk wani abu da na mallaka na shi”

Ta saki baki tana masa kallon mamaki.

“Da gani akwai babbar matsala, ina tare da sister if you won't mind ina son ka shiga motar mu tafi gida zai mu yi maganar”

For the first time ya daga ido yayi mata kallo mai kyau, kallon da kawai yayi mata ta fahimci ba zai yarda ya bita gidansu ba, ba ma lallai ne ya shiga motar ba. But bata da yadda zata yi domin tana jin ta damu da shi da rayuwarsa kamar wani wanda ta saba da shi, yanayin yadda kaddara take ta kara hada su ma wani abun ne da ba tsarinta su ba.

“Alfarma zaka min ka shiga motar nan, na san ba ajinka ba ne, kuma ka fi karfin haka but please do this for me”

“Ni zan yi driving...”

Ya fada kai tsaye daman ba shi da wani hope bayan wannan ba shi da wata mafita ko dabara a yanzu sai wannan.

“Fine”

Ta fada tana murmushi tare da daga hannayenta sama, sannan ta daga masa yatsanta daya sama.

“One minute”

Ta nufi da wani irin zumudin da ita ma kanta bata san na minene ba, murna take Ameer zai shiga motarta sai kace wani celebrity. Driver side ta tsaya ta yi knocking Namra ta sauke gilashin, yadda take watsa mata wani kallo sai ka rantse da Allah bata san inda yar'uwarsa Nimra ta fito ba, ba kuma ta yi da gangan ba ne, sai dan ya zama mata hali, ta nan suka banbanta da yar'uwarta, domin Nimra irin yan matan nan da babu ruwansu da girman kai ko nuna isa balle wulakanta wani, tsabanin Namra da take ji da kanta kamar ita kadai ce yar mai kudi a garin Abuja.

“Sauko ki koma baya”

“Ban gane ba”

“Na ce ki sauko ki koma back seat”

“Fine daman ba son driving nake ba, amman zan cen na zauna baya ba zan zauna ba, zan dai zauna a front seat”

“Idan ba zaki zauna a baya ba, then get out of my car, ni zan zauna a front seat”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.