Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 227
“Who's that stupid guy?”
“Wani sakarene da zan koya masa hankali soon”
“In that case kai ma ka yi bincika wani abin da ya fi tsana, so that ya dandana dacin da ka ji, sai dai ban ci ka wuce iya yadda yayi maka ba, zaka iya bincikar abin da baya so sai ka yi masa shi ka ga na zuza kenan”
Ta fada da murmushi a fuskarta sannan ta nufi motarta.
“Kar na yi latti bye, sai wata rana idan Allah ya sake hada mu but next time karka yarda mu hadu na ganka da bacin ran nan kuma karka ce min baka rama ba”
Kallonta kawai Ameer yake cike da burgewa har ta shige motarta ta barshi a gurin tsaye.
“You're right yarinya, na fi kowa sanin abin da ya fi tsana kanki na ja kin kawo shawara, nice to meet you”
Ya fada da murmushi a fuskarsa kamar ba shi ne ya gama fushi a yanzu ba.
______________
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
_Na Khadeeja Candy_
5️⃣
“Ko wace dakika da mintuna idan suka wuce basa dawowa, rashin dawowar yana nufin rasa abubuwa da dama ciki har da lokaci idan baka yi amfani da shi a lokacin da ya dace ba, kyaunku ba zai tabbatar har a bada ba, ku yi aure a lokacin da maza suke ganinku suna yaba surarku har suna sha'awar aurenku, idan lokaci ya wuce za ku neme su ku rasa a lokacin ido zai rufe wata kila ku fadawa wanda be dace da aurenku ba, ba ni da buri a yanzu kamar ganin aurenku”
Ta sauke hannunta daga fuskar Nimra tana murmushi.
“Zamu yi aure Ummi, ni kin riga da kin san inda da wanda nake so kuma da zarar ya dawo daga Umra zan masa magana ya turo, sai dai ki yi ma Namra wa'azi ta rika sauraren masu zuwa gurinta, domin ita ce mai girman kai”
Namra dake ta danne danne da complete ta dago a fusace tana kallon kanwarta, wato Husainarta.
“Okay haka kike zama gurin Ummi kina min munafurci ko? Kina ruwanki da rayuwata? Maybe I'm not ready now ko kuma dukan masu zuwan basu min ba”
Ummi ta lankwasa kai tana kallon yarta.
“Na fa san halinki Namra, taya za a ce duk samarin dake nuna suna sonki babu wanda yayi miki?”
“Ummi I'm serious gaba dayansu ni ba su min ba”
“Ba ki sake jiki da su taya za'ayi ki san wadanda suka miki? Da wandanda basa miki?”
Cewar Nimra, domin ita ce mai far'a da saurin sabo ga son mutane, yadda take friendly da kowa sai ka dauka tana kaunar duk namijin da ta yi arba da shi ne.
“Nimra this is my life, can you please mind your own business? Ni fa ba irinki ba ce kowa far'a kowa dariya har wanda be kamata ace yana sonka ba ya zo yana maka maganar soyayya”
“Ummi See? Kin ga abun da nake fada miki ko? Fadin rai ba zai bar ta ta kula samari ba”
Namra ta dauki fillon kujera ta jefawa Nimra, Hajiya Zahra ta yi saurin saka hannunta ta tare.
“Gaskiyar da ba ki so, dole mu fada miki, kuma karki yarda na sake jin bakinki ya furta cewar baya son kowa?”
Miyewa ta yi sauye bayan fadar haka ta nufi wata karamar kofa dake falon ta bude ta fita tsakar gidan da ko'ina yake tsab, matsawa ta yi kusa da flowers ta mika hannunta tana taba su a hankali, babu ranar da bata tunanin ďanta, babu ranar da zata zauna ta yi hira da yaranta akan rayuwarsu bata tuna da ďanta, damuwarshi ta haifar mata da damuwa da yawa, ta haifar masa da rashin kuzarin iya rike kanta a duk lokacin da ta tuna kamar yadda hawaye suka fara wanke fuskarta, ta kasa cire kanta a damuwa ta kasa daina tunaninsa duk da kasancewar likita ya gargadeta da ta cire damuwa a ranta saboda hawan jinin da take fama da shi. A tsorace ta juyo jin muryar Mahmood yana kiranta. Kamar hoto ya tsaya yana kallonta ganin hawaye a idonta.
“Ummi lafiya?”
Ta taba fuskarta sai ta ji hawayen sa bata san lokacin da suka sauko mata ba, murmushi ta yi ta share hawayen.
“Lafiya kalau, yanzu ka dawo?”
“Eh ni ma dauko Abiey, amman Ummi ba lafiya ba kalli fa kuka kike yi”
“Tunani kawai nake yi, makomar yayana idan bana raye that's...”
Ta karasa wasu hawayen na sauko mata.
“Haba Ummi ki daina kawo wannan abun a ranki please, ba zai taba faruwa ba tare zamu rayuwa In Shaa Allah”
Ya rumgume yana jin wani emotional, he can't imagine his life without her, ta ya za su iya rayuwa.
“Ummi ba zamu iya rayuwa ba idan babu ke, babu wanda zai rayu babu uwa a kusa da shi kuma ya more rayuwa, there's no love like a mother love for her child”
Kalaman da Mahmood yayi sai ya kara sakata cikin damuwa, ta kara tausayin ďanta, su da suka san dadinta suke fadar haka ina ga wanda be sani ba.
Lumshe ido ta yi wasu hawayen masu zafi suna sauko mata, su da suka rayu da ita kenan suka san dadinta ina ga wanda ya rayu shi kadai be san dadinta ba.
‘Ko waye mahaifiyarsa a yanzu?’
Ta tambaye kanta, kamin ta dago fuskarta ta share hawayen ta nufi kofar fita daga gurin tana sauke kanta kasa domin bata son yaranta da suke falo su lura da kukanta. dakinta ta shiga ta ci kukanta iya wanda ya isheta sannan ta wanke fuskarta ta shafa hoda da kwalli saboda ta bata da fuskar kukan amman ina ya kasa boyuwa a idon mijinta, domin a duk lokacin da ta shiga bangarensa idonta yake fara kallo ta nan yake iya karantar damuwarta.
“Zahra kukan me kika yi?”
Ya tsayar da shirya kulolin abincin da take kuma ta kasa hada ido da shi.
“Na tashi ne bana jindadin jikina”
“Amman ba zan fita ba haka na barki ba, wani abun ya faru ne? Ko yarane suka bata miki rai?”
Ta kalleshi tare da girgiza masa kai.
“No, ina tunanin ďana ne, na kasa manta ciwon har yanzu, ban san ranar da zan warke ba”
Kamar daukewar wutar nepa haka Abiey yayi shiru be sake cewa komai ba, har ta gama zuba abincin ta aje masa a maimakon ya ci sai ya mike tsaye ba tare da ya kalli abincin ba ya fice daga falon na shi ya shige dakinsa, binsa ta yi da kallo hawaye na sauko mata, haka suke yawan samun sabani a duk lokacin da zata nuna masa kauna ko tausayin ďanta da baya tare da ita, wannan dalilin ya saka ta boye abin a ranta ta daina maganarsa ko son sanin halin da yake ciki, balle har ta tambaye shi, yana raye baya raye a halin yanzu duk bata sani ba.
“Lokuta da dama bana iya tunani mai kyau, na kan aikata abun da yake zuwa ya zame min na bakinciki da nadama, ni kawai bana iya aikata komai a daidai”
Ta furta tana girgiza kai kuka take sosai irin kukan nan marar sauti.
AMEER POV.
A gurin da suka saba shakatawa suke zaune, sai dai a yau a waje suke zaune ba VIP ba kamar yadda suka saba, saboda Ameer da ya riga su zuwa ya kama guri a harabar da wasu suke zama ya zauna, a ka'ida idan ya zauna a guri, siye gurin yake irin siyewar da ko awa nawa zai yi ba za a shigo ko a zaunar da wani costumer ba, sai idan ya bar gurin ko da kuwa zuwansa ne na farko a guri, Ameer na jin wata kalar isa da kasaita kamar wani Sarki da shi kadai ya ke da ikon yin yadda yake so a ciki jama'a, sai dai a mamakinsu yau yana zaune cikin mutane and nishadin dake fuskarsa sai ka yi zaton irin samarin nan ne da ba su dauki duniya da zafi ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.