Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 100 of 227

“Waira bachi kike yi?”

Ta girgiza kai, sai ya sakar mata murmushi.

“Miye na sad face? Ko fada ka yi mata?”

Ya karasa yana kallon Maleek, Maleek be ji zai iya amsa masa dan haka ya maida kansa kan wayarsa dake hannunsa.

“Ta so muje ki raka ni gari”

Ta mike tsaye da sauri ta nufi inda yake.

“Ba a fita da ita, idan ka ga ta fita sai idan makaranta zata je, Ummi bata son a fita da ita”

“Idan ta zo ka ce mata ni na fita da ita ba wani bako ba”

Jabir ya kama hannunta ya juya da ita zata fice, har Maleek ya unkuro kamar ya yace baki sha tea ba Waira sai kuma wata zuciyar ta hana shi, but he don't know why kawai baya jin natsuwa da fitar da Jabir zai yi da ita.
[6/24, 4:30 PM] My S Line: 41

MALEEK POV.

Gaban windows din falon ya isa ya faga curtains din yana kallon Jabir da ya budewa Waira gabam gaba ya shiga ya zauna tana share hawaye, ya rufe mata sannan ya zagaya ya shiga mazaunin tuki ya murza key din motar. Sai da Maleek ya ga fitarsu sannan ya saki curtains din ya nufi hanyar dakinsa. Ya san karya ya fada cewar Ummi bata bari a fita da Waira kuma ba zai iya fadar dalilinsa na yin karyar ba, shi dai be tana gwada fita da ita ba, haka ma Mahmood da Namra, Ummi kuma ba fita take irin haka nan ba, wani lokacin ko da zata fita Waira tana makaranta ko ana mata lessons, ko tana bachi, sai dai a yadda ya lura Ummi bata damuwa da rashin fitarta dan haka ya fahimci cewar bata son a fita da ita ba dan ta fada masa ba. Ya tura kofar dakinsa ya shiga, abu daya ya fado masa a rai wato bude jakar da ya dauko a dakin Ummi domin sanin me ke ciki, daman irin wannan lokacin yake so, da babu kowa a gidan babu mai takura masa.

Sai dai be natsu da hakan ba har sai da sakawa kofar key, sannan ya nufi closet dinsa ya dauko jakar. Be takurawa kansa sai ya bude key din ba sai ya saka reza ya yanka saman jakar, ya san he most explain idan yaje maida mata jakarta, but for now yana son sanin me ke cikin jakar da har Ummi ta saka shi a cikin akwai ta dora masa kaya kuma ta rufe a wardrobe dinta. Ya bi duk takardunta ya duba be ga abun da yake nema ba, domin be ga wani abu daya shafi ciwonta ba, shi kuma zuciyarsa ta kasa natsuwa da zancen da Waira ta yi musu cewar tana da ciwo da zai kasheta. Saman jakar ya yanka ya bude saboda zip din yayi tauri, takardar ya tarar ya fara cin karo da su as he expected daman ya san Ummi ba zata yi ma kudin wannan mugun boyon ba, domin ba su barawo a gidan. Cikin wani yanayi na kamar nadamar ya saka hannu ya dauko takardun ya fara dubawa, each and every paper da file da ya ci karo da su na rashin lafiyartar ne, stage din da ciwonta yake da kuma dokokin da likitoci suka bata. Tashin hankali ba a sa maka rana inji bahaushe, Maleek ya mike tsaye da sauri yana duba takardar cikin matukar tashin hankali da rudani.

“Ummi.... How.... How....”

Ya furta murzar na karkarwa har hakoransa na son haduwa da juna, taya Ummi zata boye babba abu kamar wannan? Abiey ya sani? Kowa ya sani? Maybe shi saboda ba shi da kusanci da ita ne ya saka be sani ba.

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”

Zuciyarsa ta kusanto masa da abun da bakinsa zai furta kwakwalwarsa ta samu natsuwa. And now ya fahimci gaskiya Waira take fada cewar ita da Ummi duk suna jiran mutuwa ne, babu abun da ya fi ba shi mamaki kamar boye ciwon da Ummi ta yi miye manufar yin haka? Ya sake daukar wata takardar yana dubawa, sai da yayi gaske sannan zuciyarsa ta raya masa gaskiya yake gani ba karya ba, and the most painful part is ya sa there is currently no cure for multiple myeloma, but treatment is available, ga wanda cancer dinsa ta kai stage 3. Ya lumshe idonsa da suka ki bashi hadin kai, hakan kuma be hana hawayensa saukowa ba duk kuwa da irin kokarin da yayi na hana kansa kuka.

“Me zai saka ki boye wannan babban almari Ummi? Why?”

Damuwarsa a yanzu is tana shan maganin? Tana ganin likita akai akai? Karar wayarsa ne ya katse masa tunanin da yake, sai da ya share hawayensa sannan ya bude idon ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayar. Kanensa ne Mahmood mai kira, and yes he need someone to talk to, hakan ya saka shi  picking calls din.

“Maleek na ga motarka a waje, please come out ina Garden akwai abun da nake son mu yi magana da kai”

“Okay”

Ya maida wayar aljihunsa ya riko takardar da yake son nunawa dan'uwansa ya nufi kofar dakin ya bude, fitowarsa ta yi daidai da hawan Ummi stairs din, kallonta yayi ita ma ta kalleshi sai ta dauke kai ta nufi dakinta ta bude ta shiga. Be yi kasa a guiwa ba ya bi abun da zuciyarsa ta raya masa na bin bayan Ummi ta tura kofar dakin ya shiga sai ta jiyo rike da mayafinta ta kalleshi. Rauni, tausayi, da losing hope su ta gani shimfide a fuskar danta a lokacin da ya tunkaro inda take rike da takardun da bata gama tantance na miye ba domin fararen takardu ne da bakin rubutu a jiki ba file ba balle ta yi saurin ganewa.

Wani yanayi da ta dade tana sakashi a  mafarkinta, ta dade tana jira zuwansa, take ta fatan ganin zuwan ajalinta. Shi ya sameta a lokaci da ranar da bata yi tsammani ba, wata hug daga ďanta Maleek, a lokacin da ya karasa kusa da ita sai ya rumgumeta ya lumshe ido jikinsa na rawa, irin na wanda be taba rumgumar mace ba, duk gurin da wata kofa ta gashi take a jikinsa sai da ya ji ana tsikara masa allura, hawaye ne masu tsananin zafi suke sauko masa. Zuwan abun da baka yi tsammani a lokacin ba, da kuma tunanin dalili shi ya hana Ummi yin wani kwarran motsi, sai ta tsaya a gurin kamar ice.

“Ummi dan me zaki boye mai muhimmanci haka?”

Ta lumshe sai hawaye suka kwankwaso mata kofa, ta daga hannayenta ta rumgume danta, a tunaninta yana magana ne akan Maleek.

“Miye hujjarki na boyewa? Mu kika boyewa ko har da Abiey? Ko kuma ni ne kawai ban sani ba saboda ba ni da kusanci da ke?”

Ya dago daga jikinta sai ta zauna gefen gado tana hawaye, shi kuma ya zube kasan guiwowyinsa rike da takardun, cikin fargaba da wani yanayi mai kama da firgici ta mika hannu ta karbi takardun tana dubawa sai gabanta ya fadi, tashin hankalinta da damuwa suka karu, abubuwa biyu za su zo ma iyalinta a lokaci daya.

“Ina ka samu wannan Maleek”

“A cikin jakarki, zuciyata ta kasa samun natsuwa tun daga lokacin da Waira ta furta cewar kina ciwo kuma zaki mutu, tun a ranar babu ranar da bana bincike a dakinki, kawai so nake na samu natsuwa ashe wani karin tashin hankalin ne zan tarar, for how long zaki yi ta boye mana wannan Ummi?”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.