Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 103 of 227
“Me kika sani game da ita?”
“Ameer”
Ta kira sannanshi a a hankali, sai ya amsa yana duban agogon hannunsa.
“A ina kake?”
“Ina kan hanya”
“Tuki kake?”
“Aa”
Ya amsa tare da bude motar ya fito.
“A tsaye kake”
“Eh yanzu na fito mota”
“Nemi guri ka zauna”
Ya koma cikin motar ya maida gambun ya rufe gabansa na faduwa.
“Akwai wani makami ko wani abun da zaka iya yi ma kanka rauni a kusa da kai?”
Ya juya ya kalli wukar da ya dauko daga restaurant, wadda ya firgita Humaira da ita.
“Eh”
“Matsar da shi”
Ya kai hannu ya dauki wukar ya bude motar ya fita ya jefar da ita sannan ya dawo cikin motar ta saka wayar hands-free ya lakata a mazaunin ta dake cikin motar.
“Done”
“Yarona akwai ruwa kusa da kai”
“Akwai ruwa a motar Ammy just go on”
“Matar da ta fada maka haka fara ce?”
“Fara ce sosai”
“Sunanta Zahra right?”
“Ban san asalin sunanta ba, amman dai Ummi Nimra take kiranta”
“Ita da mijinta yan asalin garin Kano ne?”
“Nimra ta taba fada min haka”
“Wani labari zan baka da ya shafi rayuwata, kuma ya gurbata zamana da mahaifika, ya nisanta ni da kai”
Ya gyara zamansa a cikin motar.
“Ina saurarenki”
“Mahaifinka ya taba baka labarin shekarun da muka dauka ba mu haihu ba?”
“Ya fada min”
“Amman be fada maka miyasa ya rabu da ni ba?”
“Har yau be fada min ba”
“Ameer na kwashe shekarar da ta kusa goma a tare da Mr Bashir, Allah be bani haihuwa ba, na yi iya yadda zan iya ta bangaren asibiti na da hausa amman Allah be bani ba, sai a yanzu na gane ashe ba a rubuto ni cikin wadanda za a rabawa kyautar yaya a duniya ba, yan'uwan mijina suka tsangwame ni, ni ma kuma na matsawa kaina, idan na ga yaya kamar na sace nake ji, ko kukan jariri naji sai hankali ya tashi, Ameer akwai kunci da damuwa matuka a zuciyar uwar da bata taba amsa sunan uwa a bakin jininta ba, ni kadai na san irin kuncin da mace take ji a lokacin da take sha'awar dandana azabar zafin nakuda da dawainiyar daukar ciki. Hankali ya tashi matuka a lokacin da mahaifinka ya gabatar min da magana aure, ina ta jin tsoron kar wata ta zo ta haihu ya juya min baya, duk kuwa da kasancewar ban ga alamar haka a tare da shi ba, a lokacin idan na hana shi aure ban masa adalci ba, kuma yan'uwansa ba za su kyale ba, ina ji ina gani aka daura masa aure sai zuciyata ta kasa hakuri har na fara bin bokaye, duk mace da ta shigo sai a fitine ta ta kasa zaman auren, a haka har ya auri mace hudu dayar har bari ta yi amman ban barta ta zauna ba, sabida jna kaunar mijina sosai. Daga baya na samu wani likita ya ba mu shawarwari akan hanyoyin da zamu bi mu samu haihuwa, a ciki akwai dashen kwan haihuwar, bayan ta tabbatar mana da cewar ni da shi duk bama da matsala zamu iya haihuwa a duk lokacin da Allah ya so, sai na kasa hakuri shi kuma ya ki ya amince da zancen dashen kwan da aka fada mana, yace ya fi son haihuwar ta zo daga Allah kai tsaye”
Ta tsinke zancen da take ta dauki ruwan dake kusa da ita ta sha. Sannan ta cigaba.
“Akwai wani Yayana sunansa Dr Hamid, kwararen likita ne dake aiki a Kano, da shi na hada kai yayi min duk abun da ya kamata na magani da allura na fara laulayi irin na masu ciki, kuma ya bani duk wani evidence da zan tabbatar wa da Mr Bashir da gaske cikin ne, farincikin da na gani a fuskarsa shi ya kara min kwarin guiwar cigaba da abun da nake, yan'uwansa suka dawi suna kaunata kamar sun lashe, daman na tsara cewar idan zan haihu zan bar kasar kamar yadda shi ma Mr Bashir ya bukata, na yi ta rainon cikina ni da Yayana muna ta neman inda zamu samu macen da zata ba mu ďa, ba mu samu ba saboda abu ne dake bukatar sirri, wata rana tsawan Yayana ya kira ni cewar an samu wacce zata siyar da cikinta saboda ayi wa mijinta aikin, na yi matukar murna kuma na jidadi, shi ya nema mana inda zamu hadu har muka ga juna muka kulla yarjeje ta saka hannu nima na saka, na bata copy takardar daya na rike daya dayar kuma tana hannun lauyana, a lokacin da zan haihu sai na ki yarda na bar kasar na haihu a gurin yaya a private hospital da yake aiki, tana haihuwa aka karbo yaron aka kawo min sannan na sanar da dangina da mijina cewar na haihu, mun dawo gida cikin farinciki sai dai yaro idan ya sha nono na baya Lafiya, idan aka bashi madara ko nonon wasu sai yayi ta zawo yana kuka, daga karshe a dole aka yanke shawarar gwada ba shi nonon mahaifiyarsa ta asali, ana gwadawa sai ya karba kuma be bashi matsala ba, hakan ne ya saka na rika aikawa ana tatsar nononta ana bashi daga baya kuma sai tace ba zata yarda da haka ba, sai na biyata kuma zai dai ta dawo gidana ta zauna, babu abun da ya wuce bin umarninta saboda ina son yaron, na sama mata gurin a gidan ta dawo ta zauna, ashe na matso da mutuwar aurena kusa ne ban sani ba, ta ko'ina akwai camera a gidan mu, kuma kanwar mijina Ummiter ta saka min ido sosai a lokacin saboda tana ganin kamar bana sonta na mallake yayanta kuma na kori yar'uwarta, zuwanta a cikin gidan shi ya tona asirina ya wargaza shirina, har mijina ya gano gaskiyar komai ya mallaka mata ďanta yace ba zai iya cigaba da zama da ni ba, babu kalar magiyar da ban masa ba, amman be saurareni ba, ni kuma hankali be tashi ba sai bayan da ya sake ni saboda soyayyar yaron ta shiga raina, sai dai kamin ya sake ni yayi min alkawarin ba zai fadawa kowa abun da na aikata ba, saboda rufin asirinsa da nawa, ba zan iya fadar dalilin dawowar yaron a hannun Mr Bashir ba, wata kila uwar yaron bata da bukatarsa a wacan lokacin ne, wata kila kuma mijin da zata aura yace baya son yaro, ko kuma tana tsoron fuskarta shari'ar yan'uwan uban yaron na asali ne, ko kuma dai arzikin Mr Bashir ta yi ke ma ďanta sha'awa saboda idan ya girma ita ma a sha miyar da ita, ni dai kam na san uwar da ta amsa sunan uwa take kaunar yaronta da gaske, kuma take son uban yaronta to zata zabi rike shi ne a ko wane hali ta shiga, yaran da muke naman Allah ya ba mu, amman ita ta samu ta wofintar? Wannan ai kamar butulcewa Ubangiji ne. Bayan rabuwar mu da Mr Bashir ya dade be yi aure ba, saboda ya gwada son uwar yaro sai dai tsoron saurayinta da ya dade yana farautarta yayi masa shigar rago, daga baya sai ya bar kasa tare dan saboda yana matukar kaunarsa da ya dawo kuma sai be zauna a Kano ba ya zauna a Abuja, ya saka ďansa makaranta mai kyau da yayi wayo sai ya fitar da shi waje, a duk tsawon lokacin nan kullum ina bibiyar rayuwar yaron ina zuwa ganinsa wannan ya saka shakuwa da aminci a tsakaninmu, amman ko na rana ďaya ban taba jin mahaifiyar yaron ta zo ganinsa ba, ban taba jin ta kira waya ta tambaye lafiyarsa ba, daga baya ma sai na samu labarin cewar ta haihu tana rayuwarta ta dabam, har sun bar garin Kano, sai dai ban san inda suka koma ba, na yi matukar takaici Ameer da yaron nan be girma a hannuna ba, da na nuna masa soyayya da gata fiye da yadda mahaifinsa yai masa, da be san wani abu maraicin rashin uwa ba... (Full story yana a cikin littafin farko wato CIWON SO labarin Zahra da Abiey da Deen da kuka Hajiya Jamila da mijinta Mr Bashir har ma da wasu, mai son zai iya min magana ya siya domin shi ma na kudi ne 08036126660) ”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.