Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 85 of 227

  Ummi ta fara sanar ma ranar da zai zo, ita kuma ta sanar da Abiey duk da kasancewar basa cikin yanayi na fahimtar juna a yanzu, sai dai babu wanda ya sani sai Dr Zainab ita ma saboda an yi a gabanta ne. Falon Dr ta zauna tana ta tsokanar Namra kamar ba yarta wai bata shiga kitchen ta taya Ummi aiki amman yau da yake saurayi zai zo har da ita ake komai, Juwairiyyya da Yesmin sai dariyar suke.
Dr Zainab na fita Nimra ta tashi ta nufaci kofa a hankali ta bude ta leka ganin babu kowa saman ya bata damar fitowa tana sanda kamar wacce zata yi sata ta tura dakin Ummi ta shiga ta duba ko'ina bata ga waya ba sai ta fito ta shiga dakin Namra nan ma bata samu abun da take so ba, ta fada dakin Mahmood, shi ma baya nan wayarsa ma bata nan sai Umar dake zaune a kan kujera yana kallon wasi series a laptop.

“Umar dan Allah wayarka zaka ara min”

“Okay”

Ba tare da tunanin komai ba ya cire key ya mika mata wayar sai ta karba ta fita ta koma dakinta da sauri, number Ameer ta saka ta kira wayarsa sai ta ki shiga, saboda ba shi da number ba, ya saka only wadanda yake da number su za su iya kiranshi, ta gwada hakan ya fi a kirga bata shiga ba, daga karshe ta yanke shawarar aika masa da sakon sanar da shi cewar ita ce ya kira ta.
Sakon na shiga kiransa na shigo wayar Umar dake hannunta dariya mai kamar kuka ta amsa kiran ta kara a kunnenta.

“Hello Ameer”

“Nimra how are you?”

Sai ta fashe da kuka.

“Kai ma kansa ba kalau ba, Ameer ina cikin wani hali kamar zan mutu, na rasa ya zan yi na yi missing dinka”

“I miss you too i miss your touch your smell, ina ta tunanin ko a wane hali kike a yanzu, na so na kira Umminki amman ban san me zan ce mata ba, i don't know why ina dai jin kunyarta, wayarki ma tana hannuna i thought zasu kira su karba ba su kira ba”

Ta rike wayar da hannu biyu taba jin kamar ta shige ciki saboda muryar Ameer da take ji.

“Ina kaunar ganinka Ameer, dan Allah ka zo?”

“Ina?”

“Gidanmu, ka zo ka fada musu cewar kana sona kuma zaka aure ni, damar da ka ce min kana jira yanzu ne ya dace ka yi haka, so that mahaifina ya yarda sona kake da gaske, ya yarda aurena zaka yi”

Yayi shiru kamar ruwa ya ci shi.

“Ameer”

“Nimra.. Listen to me let me think about it”

“Ba abu ne da yake bukatar tsayawa tunani ba, a yanzu ya dace ka yi komai Ameer, saboda Abiey yace kasa da wata daya zai mana aure ni da yar'uwarta Namra, ita a yau ma wanda take so zai zo ya gaishe da su Ummi, idan ba ka yi haka a yanzu ba ba za su yarda da gaske aurena zaka yi ba”

“Nimra....”

Sai kuma yayi shiru.

“Nimra.. Ba zan iya yin haka ba, abun kunya ne a gareni ace na zo ina ta hauka akan kanwar abokiya kuma makiyina, bayan iyayenta sun nuna min tsantsar kiyayya, ko baki ji abun da mahaifinki ya fada ba a lokacin da ya zo ya tafi da ke?”

“Ameer karka duba komai, kai da bakinka ka fada min cewar ka shirya fuskantar duk wani kalubale akaina...”

“The things is.... I'm fucking lie, ba gaskiya na fada miki ba, shiyasa na kasa yarda na barki ki sake aikata kuskure, saboda zaki kara jefa kanki da iyayenki a cikin damuwa ne kawai, and maganar Allah na tausaya miki matuka”

“Me kake nufi Ameer?”

“The whole life da muka yi is set up, na shirya haka ne saboda na rama abun da ke da dan'uwanki kuka min, kuma na bakata ran iyayenki kamar yadda nawa ran iyayen ya bace, sai dai yanzu na gane da gaske kin fada so na kuma kin shiryawa komai akaina, sai na ji tausayin amman ni ban taba jin sonki ba even for once, da farkon haduwa dake na dauke ki kamar kawa ne ina jin na sake dake back then na gane komai shiri ne ke da yayanki Maleek sai na shiryawa daukar fansa”

“Karya kake Ameer, wani ya cilasta ka fada min haka saboda a raba mu, kana tunanin yi min wannan karyar zai saka na daina sonka? Nooo”

“I know be kama na fada miki haka a irin wannan yanayin da kike ciki ba, amman dole ne na fada miki gaskiya saboda ki samu natsuwa ki daina wahalar da iyayenki da ke kanki, ina tausayinki Nimra na ji ba dadi a abun da na aikata, and ina gode Allah da baki ban kai ga yin mu'amala dake ba, duk da na yi attempting amman baki ba ni dama ba, you're a good girl, na yaba da wannan....”

“Someone forced you to say this”

“No one can force me Nimra kin fi kowa sanin waye ni, idan kuma baki sani ba ki tambayi dan'uwanki, babu wanda zai cilasta na fadi abun da ban yi niya ba ko kuma ban shirya yi ba”

“Wannan ba kai ba ne, na san waye Ameer dina, ba zaka fadi haka ba, na akwai abun da yake faruwa”

Ta yanke wayar tana kuka zuciyarta kamar zata fashe, gashi jikinta daman babu wani karfi domin bata iya cin komai, fashewa ta yi da kuka sosai ta kwala wani uban ihu da sai da mutanen da ke kasan stairs suka ji. Ummi ta shigo dakin da sauri Namra da Yemin na bayanta kamin Juwairiyyya da Dr Zainab su shigo. Ummi ta zauna kusa da ita ta ta dafa ta.

“Lafiya?”

Ta kasa magana sai kuka take, tun ana rarrashinta cikin dadin rai har suka gaji suka fice. 3pm Namra na dakinta tana shafa hoda wayarta ta yi ringing tana ganin mai kiran ta yi saurin aje powder ta dauka.

“Hello”

“Baby girl anya tafiyar nan zata yi a yau kuwa?”

“Miya faru?”

“Har yanzu jirginmu be tashi ba”

“Amman dazun ka ce min gaku nan zaku shiga jirgi kuma?”

“Eh mun zo zamu shiga sai kuma ta aka fasa”

“Ban gane aka fasa ba, akwai wata matsala ne?”

“Matsalar shi matukin jirgin Kishi yake yi baya son na hadu da matata”

Murmushi ne ya subuce mata.

“Kai dai kullum a cikin zolaya kake?”

Shi ma murmushin yayi mai sauti.

“Ga mu nan bakin gate din gidanku zamu shigo ke nake son na fara gani idan mun shigo”

“Okay i can't wait...”

Ta aje wayar with so much excite a nufi inda mayafinta yake ta dauka ya yafe, ta fice da sauri. Dakin Ummi ta shiga tana murna kamar ba ita ba.

“Ummi gashi nan ya zo”

Ummi dake rike da waya tana nunawa Waira hotuna da dauka na zomonta ta dago ta dube ta.

“Har ha iso, ki fara kai shi bangaren Abiey ya huta tukuna, kim ga gidan na mu da baki kar mu fito tarbarsa ya ji wani iri”

“Shi ma yace ni yake son ya fara gani ai”

Ummi ta girgiza kai tana mamakin yadda abubuwa suka canja ba a ko jin kunyar fadawa iyaye wani abun. Da dariya Namra ta fice daga dakin, sai Ummi ta tashi ta isa gurin Windows din dakinta ta janye curtains din a hankali tana kallon Motar da ta kunno kai cikin gidan, Waira ma ta tashi rike da zomonta tana shafawa ta bi bayan Ummi, daman duk inda Ummi take Waira tana gurin. Da murmushi Ummi take kallon motar tana jindadi farincikin a yau Namra ta kawo musu wanda take so gida. Front door aka fara budewa wani kyakkyawan matashin saurayi mai ruwan fulani ya fito yana sanye da shadda da hula cikin kamala, a take murmushin dake fuskar Ummi ya bace, ta kara daga curtains din tana son tantancewa kama ce ta yi yawa har ta bace haka, ko kuma mutumen da take gani shi din shi ne a zahiri? Amman taya za'ace shi ne har yanzu da kurciya? Waira ma zaro ido ta yi ta saki Zomon dake hannunta a tsaye ya fadi kasa ta taba sarkar wuyanta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.