Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 117 of 227
Dagowa kawai yayi ya kalleta sai ta ga idonsa na zubar da hawaye ya kasa ce mata komai ya juyar dakansa ya hau stairs ya shige dakinsa. Kwantawa yayi ruf da ciki a take zazzabi ya rufe ciwon kai mai tsanani, yana jin wayarsa na ruru alamar kira amman ya kasa dagawa ya duba mai kiran ma balle har ya amsa.
UMMI's POV.
Ranar da aka yi sadakar ukun Nimra zuciyarta ta kwadaitu da son ganin danta, fiye da yadda jikinta ke son ganin likita. Bata son daga hankali kowa dan haka ta bar duk wani abu da take ji a ciki ranta tun daga ciwon jiki har zuwa son ganin Ameer da kuma son sanin halin da yake ciki, domin Maleek ya gabatar mata da duka abokansa da suke tare da suka zo masa gaisuwa har ma da iyayensu van da Ameer, ban da iyayensa da ba su san ma abun da yake wakana ba. Ta san idan tace tana son ganin Ameer ko sanin halin da yake ciki, yayanta da mijinta za su fahimta ba, ita kadai ta san yadda take ji kuma ta san halin da take ciki. Domin sosai mutuwar Nimra ta taba ba, bata iya cin komai a yanzu sai ka mata magana sau uku sannan ta amsa maka daya, irin wadanda tunaninsu yayi nisa damuwa ta sako gaba haka Ummi ta zama, musamman tana jin ita ma kamar nata mutuwar yana kusa da ita. Misalin 2pm aka yi addu'ar uku, wadanda suke kusa suka koma gidajensu na nesan ma da yamma wasu suka kama hanya, domin gaisuwar ta samu halartar mutane da daga daga abokai da dangi, Shuraim ma da ke ta shirya shiryen komawa Katsina a dole ya fasa saboda rasuwar, daman daga samuwar rai wato haihuwa sai kuma rasa shi mutuwa kenan ake yi ma irin wannan taron, ba ma kamar mutuwa.
Washe garin ranar da aka yi sadakan ukun Nimra da yamma lis guraren biyar da rabi, Ummi ta fadawa Maleek tana son ya kaita asibiti ta ga likitanta wanda ya saba duba ta. Duk yadda ta so ta fita ita kadai sai Maleek hakan be samu ba domin Waira tana jikinta tsawon kwanakin nan duk wani motsi na Ummi ta san da shi, ta kara takura matuka saboda taron da aka yi, da kuma rasa Nimra da ta yi sai take jin cewar tana ta rasa mutanen da take so take sabo da su, hakan ya saka ta shakuwarta da Ummi ya karu, Maleek kuma ya fi sassauta mata da tausayinta a yanzu fiye da can baya. Dan karamin mayafi Ummi ta saka ta yafa ta rufe kanta sannan suka shiga motar Abiey ma be so an barta ta tafi daga ita sai Waira sai Maleek ba, sai dai nuna masa cewar ta fi son zuwan ita kadai ya saka dole ya kyaleta.
Sai da suka yi nisa a tafiya ta gyara hannunta dake rike da carbi ta ce.
“Maleek ba asibiti zamu je ba”
Ya rage tafiyar motar.
“Ina zamu je?”
Ta sauke ajiyar zuciya kusan sau hudu sai a na biyar ta iya furta.
“So nake ka kai ni na ga Ameer, na san Mahmood be san gidan ba, ni ma kuma ban sani ba, mahaifinku kuma ko ya sani ba zai kai ni ba”
Maleek ya jiyo ya kalleta.
“Ummi Ameer fa kika ce?”
Ta shiru na wani lokaci sannan ta daga masa kai idonta na tara hawaye. Ganin zata zubar da hawaye ya saka Maleek saurin juyawa ya fuskancin gabansa.
“Why?”
“Ina son na san halin da yake ciki, buri na kyautatawa kowa na bawa kowa hakkinsa”
“Kina kallo amman Ummi ko gaisuwar nan be zo ba, bana son ganin fuskarsa ko kadan”
“Karka zarge shi da abun da ya faru duk laifina ne, da ban aikata abun da na aikata ba da duk haka be faru ba, shi ma baka san halin da yake ciki ba”
“Wane hali yake ciki Ummi? Halin da yake ciki ya kai wanda mu muke ciki? He's the reason da muka rasa Nimra? I will never forget that, saboda bakar zuciya da son kai irin nasa, and i will never forgive him”
“Ka kai je ka aje ni kofar gidan dan Allah sai ka yi tafiyarka”
“How comes ma za ace ke kika haife shi Ummi taya? Taya zaki haifi wannan ďan iskan wawan mahaukaci da babu komai a zuciyarsa sai sheri”
Ummi ta kai hannu ta dafe zuciyarta hawaye na sauko mata, ji take kamar ita Maleek yake zagi, domin ita ce silar komai a yanzu.
“Ya Maleek please”
Waira ta fada itama tana hawaye ganin uwar dakinta na kuka. Ta madubin gaban mota ya kalleta da hawayen da take ita ma ta kalleshi, be sake cewa komai ba ja motar. Be tsaya ko'ina ba sai a bakin gate din gidansu Ameer ba zai iya shiga ciki ba dan haka ya faka motar a waje. Ya fito ya budewa Ummi ta fito tana gyara hijabinta mai 3 in 1, Waira ta bude side dinta ta fito ita da Ummi suka doshi gate din gidan. Masu gadin na ganinsu ya mike tsaye ya bude musu gate ana musu sannu da zuwa, Maleek binsu yayi da kallo har suka shige sannan ya koma cikin motar wani irin zafin zuciya na dibarsa. Suna shiga harabar gidan Waira ta jiyo busar sarewar irin wacce Eid yake mata a garinsu, busar da babu wanda iya ta sai Eid busar da aka kirkira da tsafi, wanda wani be isa ya kwaikwaya ba, balle har ya iya. A firgice ta saki hannun Ummi ta falla da gudu sai kuma ta ja ta tsaya tana kallon gabas da yamma ta juyo ta kalli nan ta kalli can ta rasa ta ina busar take fitowa. Kara matsawa ta yi compound din sai ta jiyo sautin na fita ta wani gurin da take kyautata zaton Garden ne, da gudu ta nufi gurin tana jefar da mayafin kanta tana kuka marar sauti hawaye sharrr kamar an sako teku...
[7/5, 9:39 PM] My S Line: 48
Ummi har ta yi kamar ta bi bayan Waira sai kuma wata zuciyarta tace mata focus on abun da ya kawo ki gidan nan, dan haka bata damu ta bi bayan Waira ko kuma ta san abun da take yi ma gudu ba, sai ta nufi kofar shiga cikin gidan domin yin abun da ya kawota. Door bell din ta fara danna tare da gyara tsayuwarta, gabanta faduwa yake sosai domin bata taba risking aikata wani abu kamar wannan ba. Wata matashiyar yarinya ce ta bude mata kofar sai ta tsaya tana kallonta ganin bakuwar fuska.
“Mahaifiyarki tana ciki? Ko Ameer”
“Duka suna nan shigo”
Ta kauce daga jikin kofar Ummi tayi taking deep breaths sannan ta saka kafarta cikin falon. Katon hoton Ameer da aka zana da art ya fara mata maraba da zuwa, bata bukatar izinin zama dan haka ta zauna a daya daga cikin kujerun da suka fi kusa da ita. One after the other ta bi hotunan da suke falon da kallo cikin har da wanda Mr Bashir ya dauka tare da Ameer da kuma wanda suka yi a matsayin iyali daya da Mommy da yaranta.
“Bakuwa muka yi?”
Mommy ta fada tana saukowa a yayinda take yi ma Ummi kallon rashin sani. Ummi ta juyo ta kalli stairs fuskarta cike da damuwa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.