Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 94 of 227
“Ban sani ba, amman dai tsakanin kwana hudu zuwa biyar akwai wanda ta rabu dashi saboda wasu matsaloli,ban sani ba ko shi ya haifar da wannan matsalar”
“Yeah daman ana samun irin haka, amman ba kasafai ba gaskiya sai ga mutum da suka dauki abu suka saka a rai, kamar wadanda suka rike abun sosai a ransu ko kuma ba su taba samun irin wannan damuwar ba sai a lokacin, but most of the time ciwon zuciya yana farawa da ciwom kirji rashin samun wadataccen numfashin ciwon kai da canjin bachi da dandano abinci wani lokacin ma har abincin baka so. Sai dai bugun zuciya abu ne mai matukar hadari da akan iya rasa rai ko rayu, musamman ma irin nata da duk kokarin da muka yi mun kasa samun daidai bugun zuciyarta, wannan ya saka na bukaci ganinku, saboda na fada muku gaskiya idan akwai abun da zaku yi wanda kuka san shi ne silar ciwonta sai ku aiwatar saboda samun lafiyarta”
Ummi ta fashe da kukan data kasa rikewa, ta tashi da sauri ta fice daga office din. Tana tafe tana hawaye har ta iso kebantaccen dakin da aka aje Nimra na masu hannu da maiko, a nan ta samu damar daidaita nata numfashin ta yaki zuciyarta har kukan ya tsaya mata, sannan ta tura kofar ďakin ta shiga. Namra da Mahmood ne a cikin dakim tsaye suna kallon Nimra dake kwnace sanye da oxygen ta lumashe ido kamar mai bachi, har sai da Ummi ta karaso kusa da gadon da take kwance sannan ta bude, a nan suma suka gane ba bachi take ba.
“i thought bachi take ma”
Mahmood ya fada, Namra kan ido ya mata bata iya magana hawaye kawai take ganin yar'uwarta a cikin mawuyacin hali. Ummi ta zauna a kujerar dake gefen gadon ta mika hannu ta rika hannun Nimra. Wayar Mahmood ta yi ringing hakan ya saka shi ciro wayar daga aljihunsa ya fice daga dakin, Namra kuma ta matso kusa da gadon tana kallon yar'uwarta.
“Kullum Ummi ke take yabo cewar kin fini far'a kin fi ni son mutane kin fi ni jarunta, yau kuma ke kika kasa jure zafin rabuwa da wani? Har kika zabe shi kika bar mu?”
“Namra be dace ki yi mata wannan maganar yanzu ba”
“Ummi ban ni na fada mata, shi fa idan ya rasata wata budurwar zai sake, nan da shekara ma ya manta da ita, mu kuwa idan kika zabe shi kika bar mu mun rasa ki kenan har abada, ba zamu iya cigaba da rayuwa babu ke a gidan nan ba, rayuwa zata zame mana ta dabam, tare muka taso Nimra tun kurciya har girma sai yanzu da muka girma zamu fara kafa na mu iyalin sannan zaki fara canja min? Kin san tashin hankalin da na shiga?”
Tana maganar da fada hawaye na mata zuba. Nimra ta lumshe ido hawaye suka sauko ta gefen fuskarta.
“Namra wuce ki fita waje, idan kin natsu sai ki dawo, amman ki daina daga mata hankali”
Namra ta bi umarnin Ummi ta fice daga dakin, sai Ummi ta kara matsawa tana kallon Nimra da idonta ke rufe.
“Nimra ki rika tunawa da mu mana, dubu yadda yar'uwarki ta shiga damuwa”
Ta kai hannu ta cire oxygen din dake bakinta ta bude idon
“Ke ma ai kin shiga damuwa ai Ummi”
“Eh amman mu muka ja komai, musamman ma ni, kina kallona ni da mahaifinki a matsayin wadanda suka hana ki auren wanda kike so, kin nuna biyayya a garemu Nimra tun da har kike gudum bacin ran mu ki yi soyayya da shi a boye, kuma na gamsu ba ki watsar da tarbiyar da muka miki ba, saboda baki bashi kanki ba, abun da kika aikata kuskure amman duk da haka na yaba da yadda kika rike mutuncinki”
Ta maida Oxygen din dake taimaka mata gurin numfashi har sai da Ummi ta gama maganarta sannan ta sake cirewa.
“Ummi da gaske ke ko Abiey ba ku cilastawa Ameer rabuwa da ni ba?”
“Wallahi ko magana ba mu sake yi da shi ba, tun bayan da ya kira mu muka zo muka dauke ki, Nimra ba dan dalilin da na fada miki ba, Wallahi da na miki alkawari ko sama da kasa za su hade sai na aura miki Ameer, saboda ina son farincikinki kuma ina jin kamar nakasu na gurina ace kina son wani abu na kasa yi miki shi”
Ummi ta fashe da kuka, Nimra ta cire Oxygen din.
“Ba mu rasa komai ba tun tashinmu har girma, ban san wata rana da kika yi mana wani abu na cutarwa ko kuntatawa ba, ba ki bar mu mun yi kewar uwa ba, tun da na girma ban san wani abu maraici ba, Wallahi Ummi har mantawa nake cewar a cikin wata uwar muka fito ba ke ba, saboda kin maye mana gurbin komai”
Tana maganar tana tsayawa saboda numfashinta dake gargada.
“Da ace na ji maganar ku da nima ban fada a wannan halin ba, a yanzu ba son Ameer ne ya fi kona min rai ba, Ummi ya yi min rantsuwa kuma ya fada min a iya gaskiyarsa cewar shi tun asali baya so na, kawai yayi hakan ne saboda ya dauki fansa, sai dai yaji tausayina bayan komai ya faru shiyasa ya hana ni guduwa, Ummi idan na yi tunanin ta wani bangare sai na gane gaskiya yake fada, Ummi wannan kalmar ta fi tsaya min a zuciya fiye da kokarin raba ni da shi da kuka yi”
Ummi ta kara jimke hannunta with shock.
“Yaushe ya fada miki haka?”
“Dazun, na kira shi da wayar Umar dake hannuna ya fada min haka, shi ne dalilin da ya saka na kasa numfashi....”
Ta lumshe ido daker ta bude kana ganin yadda take jan numfashin kasan tana cikin wahalar numfashi.
“Miyasa yayi miki haka toh?”
“Saboda ya dauki fansar Ya Maleek da kuma ni da yake ganin kamar hada kai aka yi da ni a cutar da shi”
Ummi ta hade yawu da tana jin bacin rai akan abun da Ameer ya aikata for the first time, miyasa zai fada mata hakan a lokacin da take cikin tashin hankalin rabuwa da shi? Kuma daman can ba sonta yake tsakani da Allah ba da akwai aure a tsakaninsu haka zai saka mata ya ki aureta ya bayan yayi breaking heart dinta?
“Ummi ina kaunarki sosai”
Ta fada tana kara jimke hannun Ummi tare da dagowa ta sai Ummi ta kai jikinta kadan ta rumgumeta, suna haka aka turo kofar dakin Abiey ya shigo fuskarsa dauke da damuwa sosai.
“Tun da muka kawo yarinyar asibiti kin ki barta ta huta, a gabanki dazun likitan ya fada mana cewar hutu take bukata, na san kuma idan kina dakin nan ke ba zaki huta ba ita ma ba zata huta ba”
Ummi ta daga jikin Nimra ta mike tsaye gaba daya tana kallonta da hawaye a idonta.
“Mutuwa kadai ta isa ta shiga tsakanin uwa da ya Abiey, idan bana kusa da ita damuwata karuwa take, kuma zamana a kusa da ita ita kuma kara mata damuwa yake”
“Dan Allah ki kwantar da hankalinki, ciwo ne fa kawai zata ji sauki ta tashi kamar ba ayi ba, yanzu da wanne zan ji tashin ha kalinki ko ciwonta?”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.