Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 150 of 227
“Zahra kin fi kowa san wacece Hajiya, tun kamin ki auri Deen har kika aure bayan rasuwar da auren da kika yi babu abun da baki gani ba na halinta. Dan haka ki saka mata ido a yanzu ki bita a yadda take son tafiya”
Ummi ta mike tsaye tana sauke ajiyar zuciya.
“Ina burin kyautatawa kowa Ya Maryam, ina son na kyautata mata, na san shi Baba ba zan iya samun yafiyarsa ba, amman ita ai tana raye yafiyarta nake son na nema a yanzu, ba zan iya da hakkin mutane da yawa ba”
“Idan kina son neman yafiyarta sai ki bi ta hanyar ďanki Ameer mana, tun da shi kun samu kyakkyawar fahimta da shi”
“Bana son na saka shi cikin matsala ta ne, burina kawai na kyautata mata irin kyautatawar da zata mantar da ita abun da na yi mata har ta furta cewar ta yafe min, amman ta ki ba ni wannan damar, yanzu kin ga sallamarta za ayi a asibiti na ce zan ba su gurin da za su zauna mai kyau, saboda Ameer ya fada min inda suke zaune ba shi da kyau kuma akwai mutane da yawa a gidan amman ta tsaya kai da fata ita bata bukatar komai daga gareni, dauren min fuska da take ma abun yana damuna sosai”
“Daman ba zai yiyu ta saurareki cikin kankanen lokaci kuma ya fahimce ki ba, dole na sai kin bata lokaci kuma kin yi hakuri, ki kwantar da hankalinki Zahra ke dai kina aikata hakan ne da zuciya daya, dan haka ki yi hakuri kuma kar hakan ya saka ki fasa kyautata musu, ai ita ma idan zata yi adalci kin yi musu duk yadda ake yi, kuma girma ya kama yanzu, ta san kuma karfi ba daya ba, ba zata iya ja dake ba idan ma ta ce zata yi shari'a ne, kuma silar wannan abun ba gashi Mr Bashir ya dauke mata nauyin komai ba? Wannan ma kawai jindadinta ne, dan Allah karki saka damuwa a ranki kin san dai yadda jikinki yake”
Ummi ta sauke ajiyar zuciya, zata sake maganar Waira ta mike tsaye tana fadin.
“Ummi assignment din ba'ayi min ba, kuma gobe school za su min fada idan ba ayi ba”
Ummi ta rage murya.
“Dauki assignment din ki tafi falo duk wanda kika tarar ki ce yayi miki assignment din”
“Toh”
Ta amsa sannan ta nufi kofar fita ta bar Ummi tana ta wayarta, tana fita dakin Namra ta shigo rike da waya a hannunta, can one seater ta zauna tana kallon Ummi dake waya.
Waira dakinta ta shiga ta dauko jakarta ta bude ta dauko littafin da aka bata assignment din ta dauki pen ta sauko kasa. Maleek ta tarar zaune a kasan carpet, ya rufe ko ina na jikinsa da jacket, kafarsa ma sanye da safa kansa ma na sanye da jar hular sanyi. Tea mai zafi na gabansa da kananan cincin a plate ya maida hankalinsa gurin Plasma dake kunne yana kallon wani documentary da ake a Al Jazeera. Zuwa ta yi ta tsaya kansa sai kuma ta ga kamar hakan be dace ba, a kokarin na yi tarbiyar da Ummi take dorata ta zauna gefensa tana kallon yadda dress din yayi masa kyau.
“Ya Maleek ga assignment da aka bani a school sun ce gobe za a kawo”
Juyowa yayi ya watsa mata wani banza kallo ya dauke kai. Bata damu ba ta fara bude littafin tana nuna masa.
“Ni kika maida kafiri kenan? Idan karatun Allah ne sai dai ki samu Ameer, yanzu kuma da yake na boko sai kika kawo min ga dan iska da duniya ko?”
Salon magana da yayi ya bude mata babi da ta yi masa fahimta ta dabam.
“Ni ban ce kai dan iska ba ne, iska ai ba shi da ďa, duniya ma bata da ďa”
Ya watsa mata harara ya dauke kai.
“Aka ce miki ni jahili ban san komai a addinin ba”
“Baka taba fada min ba, shi ma da farko ba tambayarsa na yi ba, shi yake fada min yanzu kuma da nake jin dadi shiyasa nake tambaya”
Ya kalleta ya dauke ido, ganin kamar ba zai mata ba ya saka ta mike tsaye tare da zomonta da littafin.
“Ummi ce ta ce idan na sauko duk wanda na gani na bashi assignment din yayi min”
Banza yayi mata har sai da ta fara taka stairs sannan ya kira sunanta.
“Waira”
Hausawa suka ce mai nema dole a biye yake, haka ta juyo ta dawo ta zauna a gabansa. Sai ya karbi littafin ya bude har ya kai gurin assignment din, ita dai kallonsa kawai take tana yana ta mata solving math, ta saka hannayenta ta rumgume jikinta saboda sanyin da ake a waje ga kuma na Ac da tun da ta zo gidan bata san wata rana da aka taba kashe shi ba, gwara ma daki akan rage ko a kashe amman a falo ba a taba shi komai sanyi komai zafi ko damina. Sai da ya gama solving din sannan ya cire jacket din dake ya rufa mata saman jiki, ya cire hular kansa ya mika mata, sai ta karba sannan ta karasa saka jacket din ta saka hular.
“Ki daina zama haka kina jin sanyi”
Murmushi ya bayyana a fuskarta ta kalli kanta tana fuskarta na kara fadada da annshuwa kallo daya zaka yi mata ka fahimci jindadin dake ranta na karramata da Maleek yayi ya bata rigarsa da hularsa saboda tana jin sanyi. Hannu biyu ta saka ta dauki tea cup din dake gabansa ta rike da hannu ta sha. Ya kalleta duba irin na mai rauni ta tarin damuwa a zuciya, ta sakar masa dara daran idonta tana murmushin ta ya fadar masa da gaba.
“Sanyi nake ji, kadan na sha”
Ta fada sannan ta aje cup din ta dauki cincin daya ta ci.
“Thank you Ya Maleek”
Kallonta kawai yake ya kasa cewa komai har ta mike tsaye ta dauki notebook din ta nufi stairs tana shinshina rigar dake ta kamshin turarenta, yau dai kam Maleek ya faranta mata rai. Dakinta ta shiga ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta sai dariya yake kamar sabuwar mahaukaciya, ranta fes ta farinciki kamar wadda aka yi ma gafara.
AMEER POV.
Ya kai hannu ya shafa fuskarsa yana kallon titin da motocin dake gabansa.
“Ina son idan Hajiya ta koma gida, zan yi magana da Daddy”
“Akan me?”
Humairah dake gefensa tana kallonsa ta tambaya. Ba tare da ya kalleta ba ya amsa mata.
“Waira”
Sai a lokacin ta dauke idonta daga barin kallonsa ta fuskanci gabanta.
“Ummi zata yarda?”
“Me zai haka? Ummi tana son abun da nake so”
“Ita yarinyar fa?”
Ameer yayi murmushi tunawa da ita kadai da yayi abun faranta rai ne a gurinsa.
“Bata da matsala ta saba da ni, ita kanta da za a tambaye ta wa take so zata fadi sunana ne”
Humairah ta hade wani abu da ya tsaya mata a makoshi ta juyar da kanta tana kallon wani gefen.
“Are you okay?”
Ya tambaya jin ta yi shiru tana kallon wani gurin na dabam. Sai ta amsa masa ba tare da ta kalleshi ba muryarta kasa-kasa kamar wadda aka cilastawa magana.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.