Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 112 of 227

Humairah ta yi fuskar mamaki jin wani abun banbara gwai, tana kokarin fahimtar hanyar da yake dorata, kamin ta zaro ido ta rufe baki da sauri tana kallonsa...

UMMI's POV.

Cikin rauni da fargabar zai dauko ko ba zai dauka ba ta zabura a lokacin da yanke kiran nata. Sai ta hade yawu da karfi ta zauna bakin gadonta, daman dai she wanted to know halin da yake ciki domin ta fahimci yana da saurin fushi da zuciya, kar ya jefa kansa a wani hali. Sakon kar ta kwana ta aika masa sannan ta aje wayar ta mike tsaye sai ga kira ya shigo, da sauri ta dawo ta dauki wayar a zatonta Ameer din ne ya kirata sai ta ga Namra. Lumshe ido ta yi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa kiran.

“Assalamu Alaikum Namra....”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Shi ne ya biyo bayan sallamar da Ummi ta yi wayar dake kunneta ta subuce ta fadi kasa...
[7/2, 9:43 PM] My S Line: 46

Labarin da Mahmood ya bashi ya zama masa wani sabon lamari a cikin kai da be taba mafarkin faruwarsa ba. A tunaninsa Mahmood zai fada masa cewar Ummi tana dauke da cutar cancer su tattauna akan cutar, amman sai ya fada masa wani labarin na dabam da fi karfin tunaninsa ya firgita kwakwalwarsa.

“Ya za'ayi na yarda da wannan? Ummi bata taba auren wani kamin Abiey ba, da ma Abiey ka ce sai na ce yes saboda Mahaifiyarsu Namra, amman Ummi bata taba aure ba, kuma bana tunanin zata samu ďan ta hanyar da be dace ba, idan ma gaskiya ba ne me zai saka ta ta boye tsawon shekarun nan bata bayyana ma kowa ba? Kuma ko sau daya bata taba nuna cewar Ameer ďanta ba ne? Maybe dai Ameer ya shirya duk wannan ne?”

Mahmood ya kalleshi.

“Da wa zai shirya? Ummi zai hada kai da ita ta fadi karya saboda me? Kuma ba shi ya fada ba ita ta fada in her own mouth, babu wanda ya matse ta, shi kasan a yanayin yadda ya bar gidan bana tsammanin zai yarda domin daukar yake ma bata cikin hayyacinta”

“Taya wai Ameer zai zama ďan'uwan mu? Not just dan'uwa ma ace dan Ummi ne wai ita ta haife shi da kanta? Ai kai ma kasan ba zai yiyu ba, wannan ba abun da hankali zai kama ba ne”

“Then ask her”

“Baka ganin halin da take ciki? Ba ta a halin da ya kamata ayi mata wannan maganar, amman ai dole gaskiya zai fito saboda Abiey ba zai dauka ba”

“Yanzu baka fahimci labarin da na gama baka ba, kenan? Abiey ma ya san da wannan, shi da kansa ya zo yayi mata fada akan me yasa ta fadi wannan abun sai gashi na gabatar masa da ciwonta a dole ya bar zancen”

“Amman taya Ummi zata haifi da ace bata bashi kulawa ba kuma be girma a tare da mu ba, ko sau daya bata taba fada mana labarinsa ba? Kuma shi Ameer mutanen da yake kallon a matsayin iyayensa ya alakarsu take da su kenan? Taya ma duk haka ta faru idan ma da gaske ne? Kuma shi Ameer ya san da haka ko kuma yaya? Kuma ďan ma na waye? Na mahaifinmu ne ko na wani”

“Nima ina son na sani sosai, sai dai bana son mu zurfafa tunani kar mu tunanin abun da be kamata ba, mu jira kawai mu ji ta bakinta zai fi, for now dai dole zata fada mana tun da gaskiyar ta bayyana”

Maleek ya gyada kai mamakin ya cika kansa har ya rasa ta ina zai fara tunani, abun sam be kama kanshi ba.

“If ma da gaske ne miyasa Ummi bata fada ba lokacin da muka samu matsala da shi? Karka manta fa har fada ta rika yi saboda ba a kama wanda yayi min aika aikar ba”

Maleek ya fada yana ciro wayar dake aljihunsa ya duba kiran Namra, he pick up the call ya kara a kunnensa kukan da ya ji tana rerawa har ya hana maganarta fita shi ya fara daga masa hankali.

“Namra are you alright?”

“Ciw...ciwo... Ciwon... Nimra ya tashi and.... She... Couldn't survive.... ”

“What do you mean?”

Ya tambaya da karfi. Sai ta amsa masa da ihu tana fashe da wani kalar kuka mai karfin gaske

“We lost her...”

“Innalillahi
Innalillahi
Innalillahi.... Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”

Haka ya rika furtawa sai a karshen ya samu hada kalmomin gaban dayansu, ya mike tsaye rike da wayar try to control himself.

“Lafiya?”

Mahmood ya tambaya shi ma yana mikewa tsaye ganin hankalin ďan'uwansa a tashe.

“Nimra ce we lost her...”

Maleek ya fada hawaye na zubo masa. Mahmood ya duke da sauri a gurin yana buga hannayensa a teburin dake gabansu har sai da hankalin mutane ya dawo kansu. Maleek ya yi following call din Namra amman bata daga ba ya sake kira bata daga ba sai ya nufi Waiters ya biya kudin ruwan da aka kawo musu ya fice da gudu, ya saka key din motarsa kusa da sau uku sannan ya shiga daidai ya shiga motar ya murza key da irin sifar da be taba tashin mota a haka ba. Kamar ya sato motar haka yake tukin yana ratsa motoci har ya iso gida, be tsaya danna horn asan da zuwansa har a bude masa gate ba a wajem gate din ya bar motar ya fito da gudu ya bar motar a kunne ya tura karamar kofar gate din da karfi, jin ta a rufe ya buga mai gadin ya bude masa, kamar an korasho haka ya shigo cikin gidan da gudu su kansu ma'aikatan gidan sai da suka tsorata, ta gudu ya shiga falon kitchen ya fara nufa ya leka sai ya tararda Hanne a ciki da Yesmin suna hira suna aiki, ya fito da gudu ya haura stairs din kamar zai zame, ta tura kofar dakin Ummi da sauri ya shiga.

“Ina wayarki Ummi ara min zan kira wani?”

Ummi ta juyo ta kalleshi hawaye na kwaranya a idonta.

“Mun rasa Nimra ko ba haka ba?”

Tsaye yayi cak ya rasa me zai ce mata eh haka ne, ko kuma aa ba haka ba ne? Tausayinta ya zame masa biyu. Daker ya cira kafarsa ya isa gurin da take tsaye ya rumgume mahaifiyarsa abun da be sani ba shi ma hawayen yake kamar ita, sai dai shi yana kokarin ya fita karfin hali ne saboda ta samu kwarin guiwa kar ita ma su rasa ta daman ba lafiya ce ya wadece ba.

“Ki yi hakuri Ummi mutuwa bata da magani”

Sai ta dago kamar jira take ta bashi amsa tana hakki tana kuka

“Haka ne Maleek, mutuwa bata da magani, na rasa mijina na farko a lokacin da nake da kurciya, na rasa mahaifina tun kamin girmana na rasa mahaifiyata a lokacin da girma ya fara kamani, yanzu kuma na rasa yata, bana fatar na sake rasa kowa kuma.. Bana fatar na sake ganin gawar kowa”

Ya saka hannayensa ya rike fuska yana kuka naman fuskarsa na rawa.

“Mu kuma ba ma fatar ganin gawarki Ummi, ba ku fata kar Allah ya nuna mana wannan ranar”

Ya maida ita kirjinsa ya rumgume ita kuka shi kuka aka rasa mai rarrashin wani....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.