Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 113 of 227
“Ummi...”
Muryar Waira ta saka suka juyo gaba dayansu suka kalleta tana tsaye bakin kofa kanta ba dankwali kamar kullum sai kallonsa take idonta a waje daman can sarki tsoro ce balle ta ga suna kuka. Maleek ya saki Ummi ya saka gefen rigarsa ya share hawayensa ya nufo kofar da Waira take tsaye da niyar ficewa sai suka jiyo karar Yesmin dake kitchen hakan yayi daidai da tsayawar motar Jabir, Umar daki daki ma ya fito da gudu domin Namra ta rike kowa kira take tana fada masa yar'uwarta ta mutu har da wadanda be kamata ta kira ba. Kan kace kwabo gidan ya karade da kuka kana ji kasan an rasa rayuwa mai tsada, Waira ta gudu a inda ta saba boya ta boye tana kuka sosai kamar ranta zai fita, domin tana matukar son Nimra, Ummi da Nimra su ne mutane da ta fi kauna bayan Shuraim da Eid..
Wani tashin hankali be bayyana ba sai da aka iso da gawarta a falon Ummi, gata kwance cikin karaga an daure babban dan yatsan kafarta da dan'uwansa, an daure hannunta ba ta motsi an lullube da babban zane. Kowa kuka yake a gidan domin ba su taba dandana zafin rasa rai ba sai a yau, ba ma kamar Namra dake ta kara tana fisge-fisge ji take kamar ace tana da ikon bada kyautar rai da sai ta bawa yar'uwarta.
“Ni kam na yi bakar tafiya, tun da na iso gidan nan bakaken abubuwa kawai suke faruwa, da nasani ban zo ba”
Shi ne abun da Dr Zainab ta fada tana kuka. Maleek ya kalleta yana istijara.
“A'uzubillahi minal shaidanin rajin, Mommy ki daina fadar haka be dace ba, mu fa musulmai ne ko kuka da kuka duk be dace na ba a son ana tsare gawa ana mata kuka”
“Allahu Akbar, yau yata ta canja suna daga Nimra zuwa gawa kaico mai rai”
Ummi ta fada tana kara fashewa da kuka sosai. Maleek da Jabir da Umar ne suka rika gawar aka maida ita a wani empty daki dake kasa saboda idan an haura da ita stairs zai zama aiki, idan kuma aka barta a falon za su tsareta da kuka ne duk da kasancewar falon babba ne mai kamar wata karamar fada. Tun da aka shigo da gawar Nimra a gidan Abiey be fito daga dakinsa ba, kuma ba kuka yake ba sai dai yayi shiru wani abu ya tsaya masa a kahon zuciya... Hoton gawarta da ya gani a asibitin bayan Namra ta kira shi ta fada masa ya rasa yarsa ya doshi asibitin ya ganta a lokacin da aka fito da ita daga dakin da aka shiga da ita domin bata taimakon gaggawa, sai dai ina mai ajiya ya karbi abarsa, mai kira yayi kira babu tsaya, tarin kwararin likotoci ko kayan aikin basa hana mutuwa ko karin wa'adi.
The death of Nimra hit every one of them, domin ba su saka mata ran mutuwa, even though likitan yace za su iya rasa ta, kuma numfashinta ya gagara sauka normal kamar yadda yake. Sai just like yadda mafi yawa mutane suna daukar bugun zuciya kamar baya saurin kisa, but ana haduwa da ajali kuma kowa da silar mutuwarsa. Waya kan waya aka rika kiran Abiey tun daga familynsa na bangaren Ammy har zuwa na Mai Martaba, da na Yesmin amman ya kasa amsa kiran kowa sai na amininsa Sauban. A lokacin da Abiey ya amsa wayar, Sauban ya fara shimfida masa kalaman hakuri da juriya da kuma yadda da kaddara, Sauban ya tunatar da shi abubuwa da dama daga rayuwarsu da baya yayi masa kalamai na kwantar da hankali da saukar da natsuwa. Duk da haka idon Abiey ko kwalla be yi ba balle hawaye. Bayan ya tabbatar masa da gobe zai yi sammakon biyo jirgin safe daga Dubai to Nigeria sannan suka yi sallama. Abiey ya aje wayar ya mike tsaye ya taka yana jin kafarsa kamar ba tashi ba gaba daya jikinsa ma ya sauya as well as zuciyarsa. Ya fito daga bangaren yana jin yadda yanayin gidan ya canja gaba daya saboda rashin yarsa, Nimra ce ta biyu da yafi kauna a cikin yayansa bayan Maleek, domin ita ba kamar Namra take ba da girman kai ko ji da kai, she's very friendly tana zama ta yi hira da shi kamar yadda Maleek ya dauke shi aboki ko ma fiye da haka. Ta kofar baya ya shigo bangaren Ummi ya daga kai yana kallon yan'uwa da suke kusa na garin Abuja da suka cika falon duk kuwa da kasancewar dare ne. Dr Zainab ta fi kowa fahimtar ďan'uwanta tana ganinsa ta san abun da ya kawo shi sai ta fada masa inda gawar yarsa take. Ya taka da kafarsa ya murda kofar dakin ya shiga, sai yayi arba da ita tana kwance a cikin karaga slowly ya karasa kusa da gawar ya sunkuya ya saka hannu ya yaye zanen da aka rufa mata, fuskarta ta bayyana gata kwance kamar ta yi magana amman ba dama, hannu ya saka ya shafa fuskarta yana tuna maganarsa ta karshe da ita a asibiti, ya risina ya sumbance ta sai a lokacin hawaye suka cika idonsa har suka diga a jikin gawar. Yana kokarin mikewa tsaye sai ga Maleek ya shigo da sauri daman baya falon a lokacin da Abiey ya shigo da ba zai bar shi ba.
“Abiey haba me zaka yi a nan kuma?”
Abiey ya juyo ya kalleshi hawaye na masa zuba idonsa yayi ja sosai kamar wan watsa masa yaji a ciki.
“I'm here to tell na yafe mata duk wani hakki nawa da yake kanta kuma na nema mata gafara”
“Ganinta a haka zai haifar maka da damuwa, damuwarka kai da Ummi matsala ce a garemu”
Abiey ya daga dansa ya mike tsaye, Maleek ya rufe gawar hannunsa na rawa idonsa na kuka ya rika mahaifinsa suka fice daga dakin.
A Daren babu wanda yayi bachi, daga Ummi har Abiey da sauran yan'uwan da suke shakikanta, domin sauran familyns Abiey komawa suka yi gida saboda an fadi cewar sai gobe da 10am za'ayi jana'izarta. Kusan kowa kwana yayi yana nema mata gafara ban da Waira da bata san kalar addu'ar da zata yi mata ba, sai kuka kawai take jikinta na rawa. Babu wanda ya bi ta kanta daman Ummi ce da Nimra masu kulata Nimra ta tafiyarta tafiyar da babu dawowa, Ummi kuma imani da yarda da kaddara ne kadai ya hana ta fita hayyacinta, amman ta yi kukan da ya canja kamaninta ya kusan tashin rashin lafiyarta sai dai bata fadawa kowa ciwon da take ji. Misalin 3am Maleek ya fito waje ya daga dakin da gawar Nimra take saboda ance ba a barin gawa ita kadai, and shi ne mai karfin zuciyar da zai iya zama da ita. Shesshekar kuka ya ji a bayan kujerar da ta saba boya, definitely ya san ita ce a gurin mamakin yadda take ta kuka har yanzu ba ta yi bachi ba. Lekawa yayi sai ya same ta a takure idonta har ya fara duk sanyin ac dakin be hana ta tara gumi ba. Dagowa ta yi ta kalleshi idonta yayi ja sosai fatar idonta ta kumbura, farar fatar fuskarta ta yi ja sosai saboda farar bata bata son wahala, hancinta ma yayi ja. Da hannu yayi mata alama da ta taso, sai ta girgiza masa kai ta kwantar da kanta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.