Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 126 of 227
“Innalillahi akwai yan'uwanta a nan?”
Ya tambaya yana kallon mutanen abokan bararta.
“Aa amman dai na san gidansu”
Cewar wata tsohuwar, kamin dayar ta ce.
“Akwai waya a jakar buhunta a dauko a kira iyalin”
“Kamin a kira iyalinta a yanzu dai ina son wani ya bini mu tafi asbiti”
Wacce ta fisu sauran kurciya ta kamata sai wasu mazan suka rika ta aka ciro kafarta daga karkashin motar, Ameer ya bude bayan motarsa aka saka ta, sannan dayar ta shiga ya rufe motar ana Allah ya sauwake. Da ada ne babu abun da zai saka Ameer tsayawa ba, ba tsohuwa ya kada be ko jajarin da aka haifa fa yau ne ya kade ba zai tsaya ba, kuma babu wanda ya isa yayi masa wani abu. Idan ma wadanda suka san shi ne sai dai aka kara a gidansu Mr Bashir ya dauki nauyin jinyar, wani lokacin kuma idan accident ya faru sai da ya ciro kudi ya watsa ma mutum yayi tafiyarsa. Amman yau shi ne da bude motarsa a saka masa wanda ya kade har jini na bata masa mota. Ban da private hospital din da suke zuwa be san wata asibiti ba dan haka can ya nufa da ita. Kai tsaye aa wuce da ita Emergency bangaren yan hadurra, a waje ya tsaya shi da macen da ta rakota ya karbi wayarta a jakar buhun dake hannun matar saboda ta tabbatar masa bata iya kira ba, bata iya amfani da waya ba. Da da ne ba zai iya rike wayar ba saboda ta fito a hannun da be sani ba, gashi wayar karama ce da ta kusan mutuwa har aka daureta da roba saboda murfi ya tsaya. Wannan kaddara ta sauya masa rayuwa da mu'alama, cikin har da walwalarsa da farinciki da yake a kullum. Bangaren kiransa ya shiga ya duba numbers din da take yawan kira da kuma wadanda ake kiranta.
“Kin san yadda ta yi saving number wanda za a kira”
Rasa number da zai kira ya saka Ameer ya kalli matar ya tambayeta.
“Eh ranka ya dade, sunanta Aisha jikarta ce ita kadai take da waya a gidan ma, kuma ita take cewa a kira mata idan za ayi kira”
Ya maida hankalinsa gurin wayar ya duba number farko da aka rubutawa Aisha ya kira a wayar ya mikwa matar.
“Toh Toh”
Ta karba da hannu biyu ta kara a kunne.
“Hello Aisha”
Matsawa yayi ya bata guri jin an amsa kira sai yayi gaba kadan yana rumgume hannayensa.
“Ranka ya dade ya sunan wannan Asibitin?”
Ya juyo ya fada mata tare da kallon agogon hannunsa.
“Hikima hospital”
Ta fadawa yarinyar a waya sannan ta sauke wayar.
“Tace gata nan zuwa, Allah sarki hankalinta duk ya tashi sai kuka take”
Ameer ya busar da iskar bakinsa ya sake kallon agogonsa a karo na biyu.
“Akwai inda nake son tafiya, za 'ayi muku komai a nan, karku kashe ko naira ni zan biya komai, kuma ki tsaya a nan ki kula da ita kamin jikarta ta zo, zan dawo a anjima”
“Toh ranka ya dade, Allah ya saka da alheri”
Ya kasa amsa mata da Ameen sai ya saka kai ya fice daga gurin. Daga asibitin kai tsaye ya nufi gurin wanki mota, shi ma da tambaya alexander ya isa gurin wankin motar da yafi kusa da asibitin domin be taba mai wanki mota ba, a gidansu ake wanke musu idan ma ya kama sai an kai toh ba shi yake kawai ba sai dai na bar motar a gida masu aikin gidansu, sai da isa gurin sai kuma wata zuciyar ta raya masa za su iya zargin wani abu, domin jinin mutum ne a motar ba kowa zai fahimta ba. Canja shawarar da yayi ne ya saka ya yi reverse sai ya canja hanya. Kamar ya san plan din da aka shirya isa makarantar a time din da suke daf da tashi. Waje ya tsaya ya aika mai gadin gate ya sanar da principal din yana neman Waira, har mai gadin ya ya tafi sai kuma ya dawo ya tambaya sunan babanta domin zai iya yiyu ba ita kadai cw Waira a school din ba.
“Ya sunana babanta?”
Ameer ya dan yi shiru yana nazari, be san sunan babanta ba kuma be san sunan da take amfani da shi a yanzu matsayin sunan uba ba.
“Waira Aliyu”
Ya fadi sunan mahaifin Maleek ba dan yana da tabbacin da sunan take amfani ba.
“Okay”
Ya juya ya shiga cikin makarantar. Be fadede ba ya dawo, sai aka bukaci Ameer ya shigo ciki domin tantance waye yake neman Waira. Yamutsa fuska yayi yana jin kamar yayi tafiyarsa, ya san idan ya shiga ciki za su tsare shi da tambaboyi ne da be san ma yadda zai amsa su ba. Ba dan kar tace ya karya mata alkawari ba da ba zai shiga ciki ba, haka dai ya daure ya fito daga motarsa ya shiga cikin makarantar, Security yana gaba Ameer na binsa a baya har suka shiga office din. Ameer ya mikawa mutumen hannu suka gaisa.
“Ka yi hakuri, dokoki ne na makaranta dole mu san wanda zai dauki dalibar mu, kuma dole mu san wanda ya kawo ta idan kawota aka yi, an kira mu daga gidansu an fada mana zaka zo, amman duk da haka ya kamata mu tantance waye kai, saboda hakkinmu ne kula da daliban mu matukar suna karanta”
Ameer yayi kamar yace musu shi ba daukarta zai yi ba ganinta kawai zai yi sai kuma yaji ba zai iya ba saboda gadarar ta tashi. Sun bashi littafi ya saka details dinsa, sannan aka kira Waira ta zo office din, ta shigo tana sanye da uniform, gashin kanta a fake a baya an sako shi ya sauko a bayanta, blue and black din uniform din ya mata kyau sosai. Tana ganin Ameer bata tsaya komai ta rumgume shi da murna.
“Da gaske zaka zo ashe”
“I said i will”
Ya amsa fuska ba yabo ba fallasa.
“Motana yana waje muje can mu yi magana”
“aa zaka jira mu tashi ne sai mu tafi tare, kai zaka kai ni gida zai mu yi magana a hanya”
“Let's talk first”
“Okay kaje ka jira ni a mota yanzu za a buga karaurawa”
Ya juya ya fice daga office din, sannan mutumen ya kalleta ya ce.
“Kin san shi?”
“Sosai”
“Okay ba wani matsala ko?”
Ta amsa masa babu da kai sannan ta juya ya fice. Ajinsu ta koma ta zauna a kujerar ta hada littafanta ta saka a jaka sannan ta kufa kanta a teburin da take karatun domin kowa da kujerarsa, haka take bata da sakewa a makaranta saboda suna mata kallon bare, gashi ita kuma ta kasa sakin jiki da saba da kowa, a kullum idan ta shigo makarantar tana maida hankali tayi abun da ya kawo ta ne, wannan ya saka take daga cikin students masu kwazo da saurin gane abu idan aka fada, ko aka yi musu bayani, secondly lessons din da ake mata a gida yana matukar taimaka mata sosai, sai dai sauran daliban da suka maida hankali kamar ita sun fita experience domin sun fara daga farko ne ita kuma ta hau abun ne daga sama.
Tana jin na kada ƙaraurawa ta goya jakarta da sauri ta dauko cake din da Ummi ta yi mata dake karkashin table dinta ta fice cikin zumudi ta nufi gate, a ka'ida idan za a fita daga makarantar sai anyi signed daga mai daukar har dalibai idan kuma School bus ce zata kai su gida zai sun yi shi ma mai tukin yayi da nufin shi ya kai su gida. Ita ta fara saka hannu a inda ta saba, sannan security ya nufi inda motar Ameer take ya kai masa littafi ya karba yayi sign din. Sannan ta bude front seat ta shiga yana kallonta sai ta sakar masa murmushi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.