Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 82 of 227
Bayan ya wuce ta dawo cikin falon ta fara neman zomonta da ya bata daga inda ta aje shi.
“Uteee Teee Uteeee”
Kiransa take da yarenta kamar an fada mata yana jin abun da take fada, abun da bata taba yi a gidan ba wato magana da yarenta shiyasa har yanzu babu wanda ya san kalar yaren da take a gidan.
“Ukur tek fi, utee utee kat...”
Fada masa take idan ya fito zata ba shi abinci mai kyau mai dadi. Ta fara leken kasan kujerun dake falon sai ta hango inda yake boye jikin wata kafar kujera, rarrafe ta yi ta isa gurin ta kama shi ta fito tana dariya ranta fal da farincikin da ta manta when last ta yi murna na samuwar wani abu.
“Daga yau sunanka Zill”
Ta fada da yarenta sannan ta mike tsaye ta nufi hanyar Kitchen. Tana bada baya Maleek ya saukowa daga stairs din da yake tsaye ya nemi guri ya zauna da mamakin yaren da ya ji a bakin Waira.
Ita kan tana leka Kitchen din ta ga Hanne da Ummi a ciki sai ta ja ta tsaya ba tace komai ba.
“Me kike so Waira?”
“Barta ta dauki abun da take so, it's high time ace komai sai an yi mata, ita ma ya kamata ta fara mu'amalantarmu kar mar yan'uwanta”
Ummi ta fada tana juyowa ta kalleta, sai Waira ta lake kafada tana son yi kukan shagwaba.
“Waya baki zomo?”
Ummi na tambaya sai dariya ta biyo bayan kukan da Waira take son yi.
“Teacher....”
Ta amsa tana shafa shi.
“Ke kika ce masa kina so?”
Ta girgiza kai.
“No amman tana so”
“Ina so”
Ummi ta gyara mata.
“Ina so”
Ta sake fada.
“Ummin za ci abinci”
“To zo ki daukar masa”
Ta shiga cikin kitchen din ta nufi gurin da ake aje kayan marmari ta dauki kwatankwacin abin da ta san tana ci ta saka a plate. Hanne ta kalleta tana gyara tumatur ta ce.
“Zomo ya fi son giďa da salat ko karasss”
Waira ta kalli Ummi.
“Ummin zaki siya Karass, gida salak”
“Muna da karas a fridge ai sai dai a nemo giďa da salat, Hanne duba mana Fridge akwai karass ki dauko mata”
Hanne ta nufi inda Ummi ta fada ta bude ta dauko ledar karass biyu, domin Ummi tana sakawa a kullashi a leda kamar na siyarwa aje idan an antashi amfani sai dai a dauko kawai. Waira ta karba ta dora sannan ta fito falon hannunta rike da plate daya dayan kuma rike da zomo, wayo idonta ya fara yi tana kallon inda zata aje zomon be gudu ba, duk abun da take Maleek be kalli inda take ba. Takowa ta yi a hankali sautinsa ganin shi kadai ne a falon, kusan lokaci daya aka cire masa tsoronsa daman ta rage tsoronsa domin ya dan canja ba kamar da ba, dazun ma saboda ta ganshi da bulala ne ya saka ta tsorata.
Ta nufe shi ta aje plate din kasa ta kama zomon da hannu biyu ta dora masa saman jiki ba tare da tambayarsa zai rike mata ko akasin haka ba, da sauri ya dago yana kallonta irin lafiya kike?
“Kar ya gudu rike sosai da kyau”
Ganin zomon zai sauka jikinsa ya saka yayi saurin rikewa kamar yadda ta bukata.
“Good”
Ta masa thumb up, bata san baya son mace ta taba jikinsa ko ta rabe shi ba, domin bata taba rumgumarsa ko taba shi ta ga abun da yake damunsa ba, a iya tunaninta bashi da halin kirki ne a farkon zuwanta gidan, daga baya kuma ta ya sauko har yakan zauna ayi hira da shi sai ta fahimci ya jefar da wacan halin nasa ne marar kyau, yanzu ya shirya mu'amala da kowa.
Bata tare da tunanin komai ba ta juya ta koma kitchen ta dauko wuka da wani babban tray ta dawo inda yake zaune rike da zomon ta zauna a kasa ta fara yanka karass din tana yanka apple, shi dai kallonta kawai yake, he's feel something different about her, lokuta da dama tana masa abun da baya iya musa mata ko yi mata magana, not like other girls da zai iya kashewa ma idan suka masa haka, tun bayan marin da ya taba mata a karon farko da taba jikinsa be sake sha'awar kai hannunsa a jikinta da sunan duka ko hukuncin ba, a wacan karon ma da ta rika shi ya ji wani yanayi na dabam ba zai iya bayyana yadda yake ba, ba jindadi ba ne kuma ba na rashin dadin ba, wani abu ne da be taba jin irinsa ba a rayuwarsa yana ďaya daga cikin dalilin da ya haddasa masa daukewar numfashi na wucin gadi, wata kila saboda mace bata taba rumgumarsa ba ne, balle ya san ya dumin jikin mace yake idan ya gwaraya da na namiji duk da kasancewar a fusace ta hau stairs din a wacan lokacin bacin ran da be san na minene ba.
There is something special about her, her unique skin colar da gashinta da ya banbanta na kannensa, the way she talk idan ta kama dole iya zaman da ta yi a gidan na shekara daya ua fahimci tana da kiyaye doka, domin duk wani abun da ta san za a mata fada idan ta aikata tana kokarin kiyayewa musamman a abun da ya shafe shi, bata cika magana ba hakan na matukar burgeshi da ita domin baya son yawan surutu tana da natsuwar da idan ba a kusa da Ummi ta zauna ba zata nemi bayan kujera ta boya. Yana fara kallon kyakkyawar hallitar da Allah yayi a fuskarta na dagon hanci da blue eyes ga karamin pink lips sai zuciyarsa ta buga da mugun karfi kamar zata fisgo ta fado kasa. This is first time da yake kallonta da wani irin kallo da be taba yi ma ya mace ba, kowane motsin da hannunta yake da na abun da take yankawa har zuwa zaman da ta yi da kuma daukar abun da ta yanka ta ci, even taunawar da take kallon yadda bakinta yake motsi yake.
“Waira...”
Ummi wanda ta fito daga kitchen ta yi tsaye cak tana kallon ikon Allah. Maleek da Waira suka kalli inda take, Maleek mamakin tsayuwarta a gurin yake ya manta da abun da yayi a yau sabon abu ne da be taba yi ba, Waira kuma jiran take ta ji abun da Ummi zata fada bayan kiran sunanta da ta yi. Ummi ta karaso gurin ta nuna zomon dake hannun Maleek, sai Maleek ya kalli zomon.
“Oh ta ba ni rikonsa ne waya taba zomo?”
“Kuma ka rika?”
Ta kalli Waira ya kalli zomon ya daga kafadunsa he can't tell why ya rike mata zomon.
“Ummin ai baya ciwo”
So take tace cizo. Ummi ta yi murmushi dake tare da hawaye daman kukanta a kusa yake.
“Wow...”
Mikewa yayi tsaye ya taku daya ya kara matasawa inda Waira take zaune tana facing dinsa, ya dora mata zomon saman jiki ya kabe jikinsa ya nufi hnayar fita falon. Ummi ta duka a gurin tana kallon Waira.
“You're so special Waira, zuwanki gidan nan ya taimaka min sosai kin canja rayuwar ďana, sanadinki na fahimci abun da ban fahimta ba akan Maleek, komai yana da sanadi, ke ce sanadin canjawa Maleek”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.