Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 178 of 227
“Na ji dabam saboda ban saba ba”
“Zaki saba sannu, ki yi list din duk abubuwan da babu, idan ba zo sai ki ba ni a siyo, kuma ki gyara min daki daya zai zama ina da gida uku kenan gidan Daddy, Ummi, sai kuma nan”
Humairah ta yi dariya.
“Ka zauna a nan kuma? Kai da zaka yi aure?”
“Aure?”
“Yeah..”
Ta furta tana kallon Nuwaira, sai yayi murmushi ya girgiza mata kai, a take murmushin dake fuskarta ya gushe.
“How?”
Ta tambaya without saying it with sound. Sai ya daga mata kafadunsa.
“Ba kin min baki ba? Addu'ar da kika yi ma dan'uwanki ce Allah ya karba so get ready for your annoying brother”
Ya kalli Nuwaira.
“Let's go”
A tare suka sauka ya bude mata mota ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya bude bangarensa ya shiga, suka bar Humairah da mamaki da kuma tunani kala kala. Tun da suka hau hanya Nuwaira take kallon Ameer har suka kusa isa, shi kam ko da wasa be kalli inda take ba.
“Ameer ya kake ji a yanzu da kake da iyaye har uku?”
Sai ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba.
“Ba dadi, ina ji mn rayuwa ta juye min upside down amman zan saba, kowa da kaddararsa”
Ta dan ji babu dadi ganin yanayinsa ya sauya sakamakon tambayar da ta yi masa, ta kai hannu ta taba shi.
“I'm sorry”
Ya kalli hannunta sannan ya kalli fuskarta sai kuma yayi murmushi.
“Yanzu ba kin musulunta ba, kin san halal da haram dole ki kiyaye wannan idan kin koma garinku”
Ta yi saurin dauke hannunta domin gaba daya ta manta da wannan haramcin. Bata sake cewa komai ba har suka isa, ya fara a daidai balcony din kofar Ummi. All her thoughts is zai kashe motar ya fita ya zagayo ya bude mata, sai ta ga ya kalleta yana murmushin da ya zame masa dole ne kawai.
“Finally kin ga Daddy daman kin taba ganinsa ai, amman dai yau kun gaisa kun san juna sani na musamman, kuma kin ga third parents din na, na san baki bukatar komai a yanzu right?”
Ta daga masa kai sai kallonsa take kamar yau dai jin kallonsa ya fi mata dadi.
“Ba zan shiga ciki ba, a nan zan sauke ki kuma ina miki addu'ar Allah ya sauke ki lafiya, ya tabbatar da ke akan addinin nan kuma ya kareki ya saukar miki da natsuwa da kwanciyar hankali a duk halin da zaki samu kanki, na gode sosai da kika ba ni danar saninki, kasancewa da ke ya janyo hankali zuwa ga alakata da Ummi, ido ya bude na fahimci rayuwa a daidai fiye da baya da nayi mata fahimta baibai, na kasance da ke a yanayi na nishadi da jindadi, sanadinki na san kishi, sanadinki na san so kuma sanadinki na san zafin rabuwa thank you so much for the experience, ina miki fatan nasara a duk rayuwar da zaki samu kanki a gaba, and i hope zaki bar kyautar da na baki saboda kin rika tunawa cewa kin taba kasancewa da wani Ameer”
Shi yake magana ita take hawaye har ya gama, ya dauke idonsa daga barin kallonta.
“Idan kin fita ki bude baya ki dauki kayanki”
Ta bude motar ta fita tana jin zuciyarta na narkewa, cikin rashin kuzari ta rufe masa motar ta bude baya ta shiga ta kwaso kayan da Daddy ya bata da Mommy tana kallonsa ko zai juyo ya kalleta amman yaki ya kalleta har ta kwashe ta fita ta rufe masa motar. Sai da ta fara tafiya sannan ya juyo da fuskarsa ya kalleta shi ma dan ya san ba zata iya ganinsa ba kasancewar bakin gilashi ne kallonta kawai yake tana tafiya hawaye ya sauko masa, kamar ta san son ganin fuskarta yake sai ta juyo tana kallon motar hawaye na sauko mata har wani jan numfashi take kamar zata shide, jin take kamar ya bude motar ya fito yace mata da shi za a tafi har garinsu. Amman har ta gaji da tsayuwa ta juya ta shiga ciki be fito daga motar ba, sai da ta yi minti biyar da shiga ciki sannan ya bude motar ya fito ya jingina da motar yana kallon kofar falon, ya shafa kansa ya sauke ajiyar zuciya, can kuma ya daga kansa sama yana kallon saman, kamin ya juyo ya bugu motarsa da karfi, ya sake shurinta motar. Ya dauki lokaci a haka sannan ya bude motar ya shiga ya dauki hanyar gidansu, da hannu daya yake tuki hannu daya ya shafa kansa gaba daya zafi yake ji a jikinsa ya rasa me ke masa dadi, kamar ya haukace haka yake ji sanin cewar bankwana ne yayi da Nuwaira bankwana na har abada, domin ya san ba zata taba dawowa ba.
MALEEK POV.
A hankali ya saki curtains din dakinsa ya sauke ajiyar zuciya, slowly ya fito daga dakin ya sauko kasa sai ya ci karo da abun da be yi zato ba. Nuwaira ce kwance akan kujera sai rusar kuka take kamar wadda aka yi ma mutuwa. Sai da ya waiga ya kalli stairs sannan ya zauna a hannun kujerar yana kallon kayan da ta watsar.
“Me kike yi ma kuka?”
Kamar jira take sai ta dago tana fada masa abun da ke cikinta.
“Ameer ne, wai bankwana yayi min tun a yanzu ba zai bari sai gobe ba, kuma ba zai raka ni ba...”
Kallonta yake yana kokarin fahimtarta, tunanin sai ya zame masa biyu, bayan ganin da yayi ma Ameer yana kallon Nuwaira da kuma bugun motar da yayi and now ita tama kuka take.
“Do you miss him?”
“I don't know”
Ta fada cikin kuka sannan ta mike tsaye ta nufi stairs still tana kuka, bin ta yayi da kallo har ta shige sannan ya mike tsaye ya nufi dinning, Coffee ya hada ya zauna a gurin yana sipping Coffee a hankali his mind is somewhere else sai tunani yake yi.
The following Day da wuri kowa ya shirya, Ummi ta cika ma Nuwaira bayan motar da zasu tafi da kaya bayan kayanta da suke gidan, ta bata wasu ga kuma wasu da ta samu a gurin Daddyn da Namra, chocolate da biscuits ma kala kala Ummi ta yi mata bag dinsu dabam kuma ta girka mata abun da zata iya ci, ta hada mata tea a madaidaicin flask ta dafa mata eggs. Bayan an saka komai police din da za su zakasu suka iso, Nuwaira ta fito tana kuka domin bata son barin gidan saboda sabon da ta yi, kusan kowa na gidan ya zame mata kamar dan'uwa, su suka cike mata gurbin abubuwan da ta rasa suka dandana mata dadin duniya suka cireta daga kuncin da kazanta da cutar da take ciki. Jerawa suka yi a balcony din har Abiey da Namra Mahmood da Ummi, Abiey da Mahmood ne kawai ba su yi kuka ba, Ummi kam ba a magana daman ita gwanar kuka ce, Namra ma da ba komai ke saka ta kuka ba sai da ta yi hawaye, saboda kukan da Nuwaira take, one after the other ta bisu da kallo dukansu sun jera babu Ameer, a lokacin ne ta gane cewar shi ma ya zama wani bangare na rayuwarta domin rashin ganinsa a cikin mutanen da take kallo a matsayin danginta. Ta takowa ta rika hannun Ummi ta saka a fuskarta
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.