Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 50 of 227
“Good Girl, i like you”
Ya furta yana jin kamar wani target dinsa ya kama hanya.
“Is she the one?”
Ta tambaya duk kuwa da bata san abun da yake kallo a wayar ba, sai ya dago ya kalleta.
“Who?”
“Girlfriend”
Yayi wani miskilin murmushi
“Tun da kike a rayuwarki kin taba jin na yi maganar budurwa?”
“Noo amman na san kana da ita”
“No Fiyya ni bana boye komai ai, idan akwai ta definitely zaku sani, more especially you, kin san you're my favorite, so ni bana da budurwa?”
Ya maida hankalinsa gurin wayar yana tunanin irin sakon da zai tura mata.
“Amman miyasa? Ni Wallahi ban taba maka magana ba ne kawai amman na dauka kana da girlfriend”
“Idan har zan yi budurwa zan zabo mai tsada ce, kuma har yanzu ban taba cin karo da wanda ta yi daidai da ra'ayi na ba, idan har zan so mace dole sai mai matukar tsabta wanda bata taba sanin miye kazanta ba a rayuwarta, wacce ke wanka da tsabta kamar yadda nake, who can cook delicious food, mai yawan kamshi wacce idan an rabe ta babu abun da zan ji sai Kamshi, mai matukar kyau fara sosai yar gidan masu kudi, mai ji da kanta, kuma wacce idan na ce ta aske gashin kanta zata aske yi kamar dai Angel, sannan kuma Virgin”
“Wacece kuma Angel”
“Wata Ahlil Kitab ce, kin san su babu ruwansu da barin gashi, kuma tana da tsabta irin yadda nake so a jikin mace”
“Tab za a samu duk mai abun da ka lisaffa amman ban da yawan tsabtarka da kuma aske gashin kai, sai idan ka samu wacce bata ta gashin daman”
“Za a samu wata rana, duk da na san dukan abun da na lissafa abu ne mai wahala a yanzu ba musamman ma virgin din, domin yan mata yanzu tun a waje suke siyar da mutuncinsu da kudi ko da sunan soyayya, ke kanki bana iya shaidarki a yanzu”
Ta zaro ido tana kallonsa da mugun mamaki har tana nuna kanta.
“Ni.... Na yarda na bada mutuncin ne ai sai Momy ta ci Ubana”
“Lokacin da za ku yi ai babu wanda zai sani, ita kanta Momyn ba zaki bari ta gane ba, ku yaran zamani ne kun fi iyayenku wayo”
Ya fada kamar ba da shi ba, ya mike tsaye yaja kujerar baya.
“Good Night”
Ya fice daga gurin yana taba wayar, fiyya ta bishi da kallon mamaki har fice daga falon gaba daya.
“Kasan yan matan da ka lalata kenan shiyasa kake fadar haka”
Ta fada bayan ya fice.
Motarsa ya nufa ya sai jingina yana jin nan ne safe place da zai samu damar aikata abun da yake son yi.
“After all abun da kika Hada kai da dan'uwanki kika min be wadatar ba sai kin sake cutar da ni da cewar na dauko wata yarinya a motar? Why Nimra? Me na tare muku ne? Miyasa ba ku son ganin farincikina?. Ban tsammanci kalar wannan rayuwar daga gareki ba, a farkon ganin da na yi miki na aminta da ke shiyasa zuviyata ta natsu da ke, ashe akwai abun da kike shirya min, kin kyauta Nimra kuma na gode”
Ya tura mata bayan ya gama rubutawa, so yake ya kalailaye zuciyarta ya siye da kalaman dauraya ya yaudare ya karye mata guiwa kamar yadda ta yi masa.
“By the way, akwai sarewata a cikin motar, ki aiko min da ita a inda muka saba haduwa dake”
Ya sake aikawa, daman sarewar na daga dalilin da ya saka ya nemi handling dinta a IG. after ya gama tura mata ya dago jikin motar ya dawo cikin gidan, yana tunanin yadda sakon zai riske ta, yana misalta irin amsar da zata ba shi Idan har yayi nasarar karya mata zuciyar.
Yana shiga dakinsa amsar sakon da ya tura ya fara dawo masa tun yana karantawa a tsaye har ya kai ga zaunawa.
“Dukan abun da kake zargin na aikata saboda na cutar da kai ban aikata ba Ameer Allah shi ne shaidata, Maleek ma ba shi da wani buri ko kudiri na cutar da kai, sai dai kuskuren fahimta da kuka samu, kuma ni ban san ka bar motar a can ba balle har na saka a aikata maka abun da kake zargina da shi, mi zai saka na saka wata a motar dan kawai na cutar da kai, miye ribata idan na yi haka? Ka fada min garin da ka tafi? Balle na aika wani yayi maka haka? Ka aminta da ni Ameer, ina cikin damuwar abubuwan da suka faru, mahaifina baya magana da ni saboda abun da na aikata na baka mota da kudi da wayata da na yi, har aka samu wata yarinya a motar ka”
Yana yi yana tsayawa har ya gama karantawa, yanayin yadda ta turo masa sakon zube a lokaci daya ya tabbatar masa da cewar ya fara yin nasarar karya lagonta, duk kuwa ba be san abun da take shirya masa a boye ba. Har yanzu be ji ya yarda da ita cewar ba da hadin bakin yayanta ta bashi motar ba.
“Sarewar kuma ban duba motar ba, balle na san abun da yake ciki saboda yau aka kawo motar tare da yarinyar a gidanmu, amman bayan komai ya lafa zan duba motar na dauko maka sarewar idan tana ciki, kuma ba zamu hadu a inda muka saba haduwa ba sai dai a gurin da muka taba zuwa da kai wajen Abuja, shi ma kuma idan har na samu sarewar domin ban san iya abun da zai faru idan mahaifina ko Maleek ya gan ni tare da kai ba”
“Really”
Ya fada bayan ya gama karanta sakon na biyu, sannan ya jefar da wayar saman gado ya cire rigarsa yana tunanin wata kila kuma ita ce take shirya masa wani zagon kasa kamin ya gama saka tasa gadar saren.....
DR SHURAIM POV.
“Wato ana yi ma mutun kallon mai hankali sai ka tarar babu hankali a tare da shi, ko kuma tunani zan ce?”
Hajiya Hajara ta fada tana masa kallon bacin rai.
“Yanzu ina yarinyar take?”
Cewar Mahaifinsa. Shuraim ya kalli mahaifiyarsa domin damuwarta ce ta fi daga masa hankali ya san mahaifinsa mai fahimta ne zai iya fahimtarsa amman Hajiya kam sai yayi da gaske.
“Ita yarinyar tana hannun Police na kai musu ita, ni kuma ina lafiya”
“Ina kwana? Kuma na kira wayarka baka daga ba daga baya kuma ka kashe wayar”
“Hajiya yarinyar bata yarda ta bar ni ba, a dole a can muka kwana ni da ita CID din, sai da safen nan da suka kama hanya sannan ta hakura, kuma kin san mace ce be kamata na barta ta kwana a can ba saboda mace ce, kuma na san idan idan na fada miki ba zaki bari na kwana a can ba ko dan yanayin jinin dake zuba a idonta ya kamata ace na tsaya a gurin gudun kar sai na dawo wani abun ya faru su ce ni na cutar da ita, shiyasa ban amsa kiranki”
“Aifa duk yadda zaka yi ka kare kanka ka sani, ku kullum ana nuna muku yadda za ku tsira sai son jefa kai a halaka kuke”
Fada ta yi masa sosai a washen garin ranar da ya koma gida, sa'arsa daya mahaifinsa ya masa uzuri har ma ya tare masa fada a gurin mahaifiyata. Sai da ta gama masa fadan tsab sannan ya fita daga falon ya shiga domin bangarensa yana wajen falon ne, ya shiga dakinsa cikin rashin jindadin rayuwa da Waira, har lokacin ya kasa natsuwa da inda za aje da ita, tunawa da yadda ta tsaya tana kallonsa ba ta yi kuka ba ya kara tausayinta a cikin ransa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.