Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 202 of 227
“Idan na dawo zai ci, ni ma na fara ci ban koshi ba, zan ci a nan”
Ummi ta masa kallon rashin yarda ta kara matsowa ta kai hannu ta dafa kirjinsa.
“Maleek na san baka jituwa da dan'uwanka, please karka yi wani abun da zai bata tsakaninku, bana son na ga kuna samun matsala”
Maleek yayi murmushi.
“Babu wata matsala da zamu samu Ummi, ba zamu sake fada tsakaninmu ba, wacan ma na rashin fahimtar juna ne haka ne Ameer?”
Ameer ya kalli Ummi yana murmushi.
“I promise, babu abun da zai sake shiga tsakaninmu maganar banza ba ba zan sake fadawa Maleek ba, mun girma yanzu Ummi you don't have to be scared”
Idon Ummi ya cika da kwalla ko da karya suke mata wannan abun na farinciki ne kuma zai kwantar mata da hankali domin abun da take ta fatan gani kenan. Maleek yayi ma Ameer murmushin karfafa guiwa sannan ya budewa Ummi kofa ta fita tare da Fiyya. A hankali suke takawa yana labartawa Ummi abubuwan da suka faru da suka isa gurin motar ya bude mata back seat ta shiga, Fiyya na kokarin shiga ya rufe.
“Ke gaba zaki shiga kin san ai ba direban ki ba ne ni”
“I don't know why you hate me”
Ya kalleta irin really?
“Ni ni ban taba tsanar kowa ba”
Ya bude motar ya shiga ita kuma ta zagaya dayan side din ta shiga, kamar wanda aka yayewa yana haka yake jin kansa sai yake jin kamar ba shi ne yayi rayuwarsa ta baya ba, that's habits of his jin yake kamar ba shi yayi ruling dinsa ba, everything become like a dream to him, kamar dai kar ya shiga garin nan ya fito sai ya ji kansa fresh komai ya same masa kamar sabo. Ya samu freedom din kansa bayan an raba shi da aljanar nan dake tauye masa abubuwa ta iyakance masa ganinsa da jinsa ko yarda da akasin haka.
A cikin motar ya cigaba da bawa Ummi labarin garinsu Nuwaira wasu abubuwan da ya gani, da kuma suka faru Ummi da Fiyya suka cika da mamaki, tsabar mamaki Fiyya bata san lokaci da ta ce
“Toh ka rantse, taya za ace ga Sarkinsu ga kowa kuma baka ji tsoro ba ka fadi haka”
Ya wurga mata wata uwar harara.
“Karya nake nan?”
Ta yi saurin zip up her mouth ta tuna ai ba ita yake bawa labarin ba ma Ummi yake fadawa.
“Abun da mamaki ko Ummi?”
“Sosai ma, ban yi tunanin zaka fito lafiya shiyasa duk hankali ya tashi da Abiey ya boye min amman da ya ga ina kuka na kira wayarka bata shiga ba dole ya fada min gaskiya”
“Addu'a babu abun da bata yi ma mutum Ummi, kawai ka yarda da Allah sai ka saka gaba a duk inda zaka shiga, Allah ba zai kunyata ka ba”
“Na yarda da wannan Allah ya kara tsareku, kasan tun kamin yau na taba fadawa Abiey cewar ina ganin kamar akwai aljana a tare da kai amman ya karyata ni”
“Ni ma ban taba tunanin haka ba, ko a lokacin da Nuwaira take tambayata ina da mata ina daukar hakan a matsayin shirmenta, kin san yan yan 20 ko under 20 din nan ban cika daukarsu masu tsayyen hankalin ba, kuma ina mafarkin time to time amman ban taba daukar abun gaske ba”
Fiyya ta kalleshi tana jin kamar da ita yake a lokacin da yace 20yrs.
“Ka ga ai da na saka ayi maka addu'ar nan an samu sauki sosai halin kan nan ma ya ragu, ni na dauka ma ta rabu da kai, ashe tana nan daman ance musulman aljannu suna da wahalar magani kasancewar su musulmai, ba kamar kafirai da suke saurin konewa ba”
Fiyya ta kalleshi domin bata fahimce labarin da ake da kyau ba.
“That's mean kana da aljana mace kenan?”
Ya kalleta sai ta sauke idonta kasa.
“Na manta kina nan na saki baki ina ta magana a gaban bakuwa”
“Ba bakuwa ba ce, yar Mr Bashir ce yar autar gidan”
Ummi ta fada.
“Still dai”
Cewarsa, sai ta sauke kanta kasa tana jin babu dadi, bata sake magana ba har suka isa asibitin shi ma be sake cewa komai ba har ya faka, ya fito motar Ummi ta fito Fiyya ma ta bude ta fito yana gaba suna baya ita da Ummi.
“Safiyya”
“Uhm”
“Karki damu da abun da Maleek zai miki ko yace, sometimes yana da kaushi but sannu sannu yana ta sauko rayuwar da nake son yayi ita yake ta koya, addu'ata ce Allah yake amsawa, da ada ne ba zai ma yi magana a gabanki ba, kuma ba zai ce miki uffan ba”
“Na gani ai, na taba gwada gaishe shi lokacin da muka tafi gidan tare da Ya Ameer amman be amsa min ba, ni ma na yi mamakin ganinsa haka a yanzu”
“Ba san yadda nake jin dadi a raina ba, ko da zan mutu a yanzu, indai har abun da na gani a yau zai daure tsakaninsa da dan'uwansa da kuma canjin rayuwarsa zan tafi cikin farinciki”
Fiyyah ta yi shiru domin bata san abun da zata sake fada ba. Duk abun da abun da Ummi take fada Maleek yana saurarenta, gabansu yake amman haka be hana shi kashe kunne ya ji komai ba. Kofar dakin ya fara tura ya tsaya Ummi ta shiga Fiyya ta wuce sannan shi ma ya shiga, Ummi ta karasa gurin gadon da Nuwaira take kwance tana bachi ta kwanto jikin gadon tana kallon fuskarta.
“Ke ma dai kin sha wahalar rayuwa, kara ni na jidadi lokacin da nake kamar ke, na yi kiriniya kuma na tashi da uwa da yar'uwa, kamin soyayya ta fado rayuwata ta tarwatsa wasu abubuwan, kuma bayan girma na sake samun farinciki na iyali da miji na gari. Amman ke kin tashi cikin wata kalar rayuwa da babu mai fatan samun kansa a irinta, ina miki fatan samun rayuwa mai kyau mai tsabta a gaba, ban sani ba ko zan rayu har zuwa lokacin da zaki samun farinciki ko aa, ni dai kam kin zama silar samuwar wani bangare na farincikina, kin zama silar canjawar rayuwar ďana Maleek, kin kusanto da Ameer a gareni, toh ni da me zan gode miki Nuwaira?”
Ta dago ta kalli Maleek.
“Allah ya bata lafiya, kuma ya baka ikon riketa amana”
Maleek yayi murmushi.
“Aure ne da aka daura na al'ada ba na gaskiya ba, idan har za a daura mata aure to za ayi na musulunci ne, beside ita take da damar zabar wanda take so”
Damuwa ta bayyana a fuskar Ummi.
“Bana son a sake samun matsala tsakaninka da Ameer, da dai an barshi a haka kowa ya dauki kaddararsa, idan ma auren za a sake daurawa sai a sake”
Da baki Maleek ya nunawa Ummi Fiyya dake tsaye tana kallonsu. Sai ta girgiza kai.
“No you can talk ni babu ruwana bana irin wannan munafurcin, ba zan fadawa kowa ba, ban taba yi ba”
“Bangaren Ameer zaki dauka ki kwashe ki fada masa komai”
“Kai da shi ba ku da banbanci a gurina, kaima dan'uwana ne kamar yadda yake dan'uwana, Mommy tace duk wani mai alaka da Ya Ameer mu rike shi fiye da yadda Ya Ameer zai rike shi, domin ba mu da banbanci a gurin Daddy dukanmu yayansa ne, har ma ya fi mu gata”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.