Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 44 of 227
“Akwai allurar da ya kamata ayi miki da yamman nan amman babu ta anan, dole sai naje pharmacy na siyo”
“Daman an taba barin mutum babu magani a irin wannan ciwon haka? Kamata yayi kamin ka ba su takardar transfer ka haɗa musu da ta magani ai”
Cewar Mahafinsa.
“Hankalina ya tashi ne shiyasa ban tsaya na yi abun da ya dace ba, domin har yanzu gani nake kamar cutar da yarinyar nan za su yi”
Yana maganar Waira na kallonsa bata ko kibta ido gaba daya hankalinta ya tafi gareshi kamar tana jin abun da yake fada, wani irin sakewa da natsuwa take ji idan tana kusa da shi, kamar sun fito ciki daya haka take jinsa. Ya nuna mata gurin zama.
“Zauna a nan can zan je na dauko magani”
Ta girgiza masa kai ko bata jin yarensa ai tana fahimtar zama yake son ta yi, ita kuma bata jin zata iya haka ita kadai har sai idan tare za su zauna. Babu juyin duniyar nan da be yi ba akan ta zauna ya tafi ya siyo mata magani amman ta ki, da ya zaunar da ita sai ta tashi tana riƙe masa hannu.
“Ashe kuwa idan zs a tafi da ita akwai aiki”
Amsawa Hajiya Hajara.
“Nima shi nake gani, saboda bata yarda da kowa sai ni, na ji suna zancen ayi mata allurar bachi, amman na faɗa musu cewar zai iya cutar da ita saboda ba ciwo take ba, balle ace tana kwana ba bachi”
Sai tausayinta ya kara kamasu, musamman ma Mahaifinsa, sai da yayi da gaske sannan ya ɓanɓare hannunta daga rikon da ta yi masa ya mikewa Maimoon ta rike masa ita da karfi, ya fita da sauri domin kokarin kwace kanta take a hannun Maimoon tana kallonsa alamar so take ta bishi. Tana ganin ya fice sai kwala uban ihu da ya saka a dole Maimoon ta sake ta ba shiri sai ta koma gefen kujera ta rakube tana ta kuka, tun tana kukan da ruwan hawaye sai ga jini na fito mata a idon amaimakon hawaye, babu wanda ya kula a cikinsu, saboda Hajiya Hajara ta ja mijinta gefe ta inda zai kalli TV da kyau, Maimoon kuma tana kitchen tana mulka tuwon shimkafa da tun kamin magariba ta gama miyarsa. Hannu biyu Waira ta saka ta taba jinin dake zubo mata ta kalla, take hankalinta yayi mugun tashi domin bata hawayen jini Eid ne yake hawayen jini idan yayi kuka, kukansa kuma yana nufi abubuwa da yawa abu ne mawuyaci yayi kuka idan kuma yayi to ta ɓace masa ne. Tsafi aka jefata da shi ko kuma Eid ne a cikin wata matsalar wata kila kuma Eid din ne a kusa, ta leka falon tana kallon ko'ina kamin ta dawo ta sake boyewa daga nan kukanta ya tsaya. Tana ta sauren abun da zai sameta.
“Ina take?”
Shi ne abun da Dr Shuraim ya fara tambaya a lokacin da ya shigo falon, Mahaifiyarsa ta fada masa inda take boye. Gurin ya nufa ya lekata har ta zabura sai ta tuna tafiya yayi ya barta sai ta koma ta zauna ta hade fuska ta juya masa baya, shi kam ba ta fushin da take yake ba jinin da ya gani a fuskarta da hannunta ne ya daga masa hankali. Ya aje ledar maganin dake hannunsa da sauri ya kama hannunta yana dubawa.
“Ina kika samu jini?”
Ta kalli hannayen nata, sai ya juya da sauri ya kalli iyayensa.
“Ta jima kanta ciwo ne?”
“Miy faru?”
“Jini ne a fuskarta da hannu”
“Subhanallahi jini”
Hajiya ta karaso tana dubawa.
“Tun da ka fita bata fito daga gurin nan ba, in da ba ta jiwa kanta ciwo ba, to babu wanda ya taba ta, sai dai ko idan ciwon dake hannunta ne”
“No duba da kyau ki gani, babu jini a hannunta ko kadan”
Ya nuna mata hannun, kamin ya shiga yi ma Waira na kurame, yana nuna jinin yana tambayarta da hannu a ina jinin ya fito. Sai ta nuna masa idonta a nan ya maida hankali gurin idon sai ya lura har yanzu akwai sauran jini a ciki dubawa yake sosai ko zai ga inda ta ji ciwo a idon har jini yake fito mata.
“Yarinyar nan abar tsoroce Shuraim ka yi saurin hannata musu ita kar ta mutu a hannunmu, tun da nake a rayuwata ban taba jin mai kukan jini ba amman yau Allah ya nuna min, anya mutum ce kuwa? Idan kuma mutum ce to sun riga sun bada jininta mutuwa zata yi”
Cikin yanayi dake nuna be jidadin maganar Hajiyarsa ba ya juyo ya kalleta.
“Haba Hajiya, yanzu da ace tana ji ai sai ki saka ta shiga tashin hankali, ba a saurin yake hukuci ga abun da baka sani ba”
“To sannu Malam, ga zahiri kana gani zaka ce kar a yanke hukunci ku ji min wani ikon Allah, Doctor ka ga wani abu? Kukan jini yarinyar nan take”
Mahaifin Shuraim ya turo wheelchair dinsa da kansa irin ya karaso gurin da mamakinsa yana kallonta ganin ido yayi mata yawa ya saka ta boye fuskarta.
“Bata son kallo, bari na mata allurar sai na kaita dakin Maimoon ta kwanta”
“Ba dai Maimoon ba kam Shuraim ta cinye min ƴa ana kwana, ko kuma ta mutu ace ita ta kasheta? Aa lalala ni ai lamarinta a yanzu ya ba ni tsoro, bana jin zata kwana a gidan nan ma ka maida ita inda ka daukota can gurin police din su sai su sama mata inda zata kwanta”
Bude baki yayi zai yi magana sai mahaifinsa ya goyawa Hajiya baya.
“Gaskiya, karka aikata irin kuskuren dana aikata wanda nake nadama har yanzu, garin taimako ka jefa kanka da mu a matsala, ko kuma ita yarinyar ma gaba daya”
“Bata yarda da kowa yanzu Abba kai ma ka gani kuma idan nace zan maidata fitina ce”
“Bata yarda da kowa idan za a kaita abujar kai zaka kaita ne? Ji min wata maganar banza? Karka janyo mana masifa Shuraim dan Allah ka maida yarinyar nan gurin tun ranka be bace ba”
Waira ta dago ta kalli Shuraim tana iya fahimtar fada ake masa, wata kila kuma duk saboda ita ne.
“Hajiya mun riga mun yi magana da su, sun ce da safe za su zo su dauke ta sai kuma yanzu na maida musu ita? Idan na kaita a can wani abun ya sameta still ba mu fita daga zargi ba”
“Kara ta mutu a hannunsu, duk abun da zai sameta ya sameta a can, ba nan ba, ka tashi ka kai yarinyar nan na ce maka Shuraim”
Ta daka mashi tsawar data saka shi sa hannu biyu ya dafe kansa da hannu biyu. Waira ta sakarwa Hajiya Hajara ido daman tun da suka dannenta suka mata wanka take tsoronsu balle kuma yanzu da take yi ma Shuraim fada har ya rike kansa.
“Shikenan zan mai da ita”
“Yanzu kuma ba sai anjima ba, daman can ban da karanbani dauko ta ba, haka kawai daga yarinya tana kuka sai ka ce sai ka zo mana da ita”
Tausayinsa sai ya kama Waira ta san duk saboda ita ake masa fada, ba zata fadi abun da suke cewa ba, amman ta san akanta ne suke masa fadan, shi ma tausayinta yaji hakam ya hana shi yi mata allurar da ya siyo sai ya bude maganin kawai ya balla ya saka mata a baki, sai ta bude bakin a hankali saboda yarda da ta yi da shi ba zai cutar da ita ba ya saka mata maganin ta fara sotsawa jin yana da daci ba a yadda ta yi tsammani ba ya saka ta yi yunkurin zubarwa sai ya girgiza mata kai.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.