Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 45 of 227

“Maimoon kawo ruwa”

Ya kwalawa kanwarsa kira, sai gata da kofin ruwan data debo a tap ta mika masa ya karba ya kai mata a baki, abun ka da wanda be saba ba da zo hade maganin sai ya tsaya mata a makoshi ta kasa hadewa ta dawo da shi a hannunta, sai ya karba ya balla wani ya bata ta kora mata da ruwa a dole ta hade da sauri haka yayi ta mata har ta anye sannan ya rika hannunta suka mike tsaye. Ya nufi gurin da ta zubar da kayanta ya dauka ya mika mata ta rike da hannun da baya ciwo, shi kuma ya rike wuciyar hannun ya jata suka fice daga falon, binshi kawai take kamar wata igiya har ya isa gurin motar da suka shigo dazun, a tsoro ya kamata jikinta ya fara rawa a taken hawayen na jini suka fara mata zuba, shi kanshi yayi mamakin ganin hawayen jini a idonta. Bude motar yayi ya dauko tissue ya goge mata hawayen, hakan nan ya ji yana sha'awar rumgumarta saboda ya kwantar mata da hankali, ba dan yau kadai ba har da gobe dan ya san da mota za aje da ita Abuja. Rumgume ta yayi yana shafa bayanta alamar rarrashi, yanayinsa sai yayi mata kamar na Eid da baya son kukanta. Bata san lokacin data kankameshi ba ta fashe da wani irin kuka mai karfi, jikinta na bata rabuwa zai yi da ita, bata san yaushe zata sake ganinsa ba, haka kuma bata san hannun da zata fada ba, bata san waye zai fahimce kamar shi ba. Dagota yayi ya duba idonta a yanzu din ma hawayen jinin ne, ya dauko wani tissue ya goge mata sannan ya bude mata front seat, wani irin dauke numfashi ta yi ta kalleshi, sai ya dafa kafadarta zai shigar da ita sai ta rufe ido gam jikinta ya fara rawa, hannunsa ya saka ya bude mata idon tana kallonsa sai ya girgiza mata kai, bata fasa hawayen ba, shi kuma be fasa goge mata ba har ya zaunar da ita cikin motar, sai ta ki yarda ta zauna a inda ya zaunar da ita ta sulale kasa ta matse kanta ta zauna a inda ya kamata ce kafafuwanta ne a gurin. A hankali ya rufe motar saboda kar ya daga mata hankali ya zagoyo ta dayan side din ya shiga ya saka maganinta da tufafinta a back seat ya kunan motar a hankali ya fara tukawa kadan kadan har ya fice daga gidan. Ganin ta ki daina hawayen kuma ta kasa rufe idon ta kasa daina kallonsa ya saka yayi mata murmushi ya mika hannunsa ya rike hannunta.

Tausayi take ba shi sosai, ya san zata san wahalar rayuwa a inda zata je, idan ma ta rayu kenan idan kuma ta mutu fa? Kamar yadda mahaifiyarsa tace? Ko kuma yadda yake zargin tsafi za'ayi da ita? Tafiya yayi mai nisa har sai da fita unguwar, gidansa incomplete building ne, be gama ba balle yace ua tafi can ya kwana ba kuma zai iya kwana a hotel ba, gashi baya jin zai iya kaita gurin police din a yanzu idan wani yayi kokarin keta haddinta fa? Yadda take da masifar kyaun nan zata iya jan hankalin wani ya ji yana sha'awar yin alfasha da ita. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya dauki hanyar gidan nasa da yake ginawa gimbiyarsa dake Abuja, da kansa ya fita ta bude gate din ya shiga da motar sannan ya dawo ya rufe gate din, fita yayi ya zagaya side din da take ya kwantar da kujerar ya dagota ta dora masa ya share mata hawayen, babu haske a gidan a dole ya bar hasken motarsa a kunne ya kunna na wayarsa. Ita dai kallon gurin kawai take ya dauko carpet ya shimfida a gafenta ya zauna kasa ya jingina jikinsa kusa da kujerar da take zaune saboda ta samu natsuwa. Be daga daga gurin ba har sai da aka yi sallah Isha'i be sha wahala samun ruwa da bula ba saboda akwai rijiya a gidan, kuma akwai butocin da masu aiki suke amfani da su su yi sallah ko kama ruwa a duk lokacin da aikin ya kawo su, da kansa ya bude rijiyar ya debo ruwa ya zuba a bukatar yana juyowa sai ya ganta tsaye bayanshi, murmushi kawai yayi ya zauna bakin rijiyar yayi alwala ta sake biyoshi har inda ya aje carpet din dake ta zauna a kasa tana kallonsa har ya gama Sallah. Rikata yayi ya maida ita cikin motar ya rufe, sannan ya zagaya side dinsa ya shiga ya zauna ya rufe bayan ya kwantar da kujerarsa. Juyowa ta yi tana kallonsa sai ya sakar mata murmushi, be ce mata uffan ba ita ma ba ta iya magana da yarensa balle ta fada masa abubuwa da yawa dake son bawa wani labari. Sai karfe tara Hajiya Hajara ta kira wayarsa da gangan yaki daga wayar har sai da ta yanke sannan ya saka ta plane mode, ita dai kam ban da aikin kallonsa babu abun da take har bachi ya dauketa daman a gajiye take kamar wanda ta yi yakin duniya. Bachi tai sosai sai dai ta yi shi a takure saboda ba gado ba ne kuma ba tabarma ba, a cikin mota ne duk yadda ta so ta wala ba zata samu haka ba, bata farka ba sai da ya tashe ta da kanshi, sai ta bude idon a hankali ta kalleshi sannan ta tashi zaune. Fitowa yayi da kafafuwanta ya rike hannunta ya kaita inda zata yi fitsari ya aje mata buta, yana juyowa sai ita ma ta juyo bata saba sarki idan ta yi fitsari ba balle ta gane cewar fitsari yake nufin ta yi. A kokarinsa na fahimtar da ita ya saka hannunsa a daga rigarta ya dukar da ita, sai ta fahimci manufarsa, mikewa ta yi tsaye sai ta juyo ta kalleshi, ganin hakan ya saka ya juya baya sanin idan yayi nisa zata iya cewa ba zata yi fitsari ba. Tashi ta yi ta zo gabansa ta tsaya tana dage sai ta saka hannunta daya ta rufe masa ido daya, a take rufe idon gaba daya yana murmushi, ta daga hannunsa ta kai gurin kunnensa, sai ya saka hannu biyu ya rufe kunnensa.
Dawowa ta yi ta yi fitsari a inda ya nuna mata Hankali kwance, bata jin kunyar aga cikinta ko wani bangare na jikinta, sai gabanta da kirjinta, daman a gurinsu kirjin mace da kasanta ne a abun kunya a gurinsu, shiyasa gurin kawai suke damuwa su rufe, a gurin namiji kuma kasan ne kawai abun kunya, wannan na daga cikin dalilin da ya saka mazan garin basa damuwa da saka riga ko tufafin da zai sitirta jikinsu. Bata yi tsaye ba ta mike tsaye ta ja wandonta sannan ta dawo gabansa ta tsaya, shi ya ji cewar ta gama ya bude ido, juyawa yayi ya dauko butar ya mika nata yana mata alamar yadda zata gage cewar ta wanke fuskarta da baki, sai ta girgiza kai daman wanke baki ko fuska idan an tashi da safe ba al'adarta ba ce, yana daga daga cikin abun da ta tsana. Juyin duniya yayi Waira ta ki yarda ta wanke bakin nan nata daga duniyar kazanta, shi kan mamaki kawai yake daman haka take fama da kazanta ko kuma koya mata aka yi. Mota ya saka ta sai ta sake zaunawa irin zaman da ta saba idan ta shiga mota ta zauna a kasa, ta rufe ido bata dago ba har ya isa gurin masu siyar da fruit kasancewar da safe be samu wasu abubuwan ba, sai lemu da abaya ya siya mata, ya sake shiga motar yana sauke ajiyar zuciya. Sai a lokacin ta bude ido saboda ta ji kamshin abaya. Zobensa na azubarfa ya cire ya mika hannu ya dauko rigarsa ta yaga ya saka zoben yayi mata sarka da shi ya saka mata a wuya, sannan ya dauki diary sa da biro yayi rubutu akai ya mika mata, ta karba ta rike. Ya ja motar suka nufi CID office, fita yayi ya zagaya gefenta ya fito da ita ta dauko maganinta da kayanta ya mika mata kayan maganin da ledar kayan marmarin daya siyo mata kuma sai ya rike ya rufe motar yaja hannunta sai taja ta tsaya tana kallon gurin, a gurin ya barta ya shiga ciki yayi musu bayani sannan ya bukaci mai uniform din gida ya zo ya rikata kuma kar a shiga da ita gurin saboda zata tsorata sosai. Haka kuwa aka yi dayan ya cire uniform dinsa ya saka kayan gida bayan Dpo ya ba shi umarni saboda kawo ta da Dr sai da yayi musu karyar cewar Tiyata zai shiga kuma yana tsoron kar azo daukarta ba shi kusa. Dr Shuraim ya mika masa maganin sannan yayi masa bayanin abubuwan da take ci, sannan ya mika mata ledar fruits din ya nuna kanshi yana gabatar mata da sunanshi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.