Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 227

“Marry ta zo nan?”

Ta gangan ya kira sunan abokiyar sheki ayarsa saboda Maleek na gurin kuma ya san yadda Maleek ya tsani haka.

“Ba ta zo ba, saboda babu wanda yake irin sana'arka a nan”

Maleek ya fada ba tare da ya kalli abokin nasa ba, sai dai zuciyarsa tafasa take saboda ya ambato masa abun da ya fi tsana a duniya. Wani shu'umin Murmushi Ameer yayi yayi relaxing akan kujerar.

“Yeah saboda na fi ku lafiya ne”

“Ka fi mu samun zunubi dai, domin baka tsaya ga bahaushiya sai ga Kirista”

“An zo gurin, bana son bahaushiya ne saboda hausawa suna barin gashin kai, ni kuma kyama ta tana da yawan da bana son ganin gashin kai a mace, saboda haka bana iya rabar mai barin gashin kai, sai wanda zata aske ko zaka samun bahaushiyar da bata barin gashin kai? I can pay”

Ya karasa yana murmushin shakiyanci. Sai a lokacin Maleek ya dago ya kalleshi yana kokarin danne bacin ransa dan kar ya bayyana a fuskarsa.

“Ka samu wata daga cikin familynku mana, ka bata kudin da kake takama da su, zata aske kai ta baka abun da kake bukata”

Yana fadar haka ya mike tsaye ya dauki makullinsa ya nufi hanyar fita daga gurin. Yana da daf da ficewa Abokinsa Dawood ya ce

“Haba Maleek be kamata ka yi fushi ka tafi saboda wannan yar maganar nan ba”

Juyo yayi cikin fushi yana nuna Ameer da shi ma ransa yake bace saboda maganar da Maleek ya soka masa.

“Then ku gargadi abokinsu ya daina yi mana zancen riba da faduwar kasuwancinsa a nan, domin babu mai hannun jari a irin kamfanin da yake kwasar zunubi”

Ameer ya mike tsaye a fusace ya nufi gurin da Maleek yake tsaye.

“Da kudinka na ke biyan Marry ne? Ko kuma jikinka ne?”

Maleek ya matso kusa da shi.

“Allah ya tsare jikina da rabarar macen da take halalina ma balle haram kuit”

Ya karasa tare da watsa masa yawu a fuska, har sai da Ameer ya rumtse ido, Maleek ya saka kafarsar ya fice daga gurin. Wannan karon ba Dawood ba har Tarig da Babu Abdul sai da suka mike tsaye, Abdul yayi saurin karasowa kusa da Ameer ya dafa shi, domin duk fadan da suke da Maleek be taba tofa masa miyau a fuska ba sai yau.

“Wannan abun na ku ya fara yawa”

Ameer ya bude idonsa da suka kade da ja saboda tsananin bacin rai.

“Sai na kashe yaron nan Abdul ni zai watsawa yawu a fuska? Ni ni Wow”

“No Ameer ka san Maleek baya son zancen mata, amman ko da yaushe kai kake takalarsa, i know abun da yayi maka a yanzu be kyauta ba, amman idan zaka zauna a gurin baka yi abun da zai taba shi ba, Maleek ba zai taba ce maka komai ba”

Cewar Tarig da duk abun da ake be yi magana ba sai yanzu. A fusace Ameer yake kallon Tarig yana fadin.

“You take his side”

“No this is not the right time to take anyone side kawai ina fada maka gaskiya ne”

“Sai na koya masa darasi Wallahi, ni zai watsawa yawu a fuska? Ya san nawa fuskata take? Ya san yadda na tsani kazanta? Sai yayi nadamar wannan abun mark my words”

Ya fisge kansa daga rikon da Abdul yayi masa ya fice kamar zai tashi sama.

MALEEK POV.

Ummi na zaune Balcony tare da yan matanta Maleek ya faka motarsa ya fito a fusace ya nufo kofar falon da suke zaune, tun daga fitowarshi motar zuwa tafiyar da yake take karantar halin da ďanta yake ciki har ya karaso yayi mata sannu ya shige ciki, a take yanayin fuskarta ya canja annashuwa da far'ar dake tare da ita suka gushe, tana tsananin son Maleek irin son da take karantar damuwar ďanta a take, yana cikin farinciki ko akasin haka ko kuka yayi sai ta gane, idan damuwarsa mai yawa ce ko kadan duk tana iya karantar hakan a fuskarsa da cikin idonta. Da sauri ta sauke magen dake jikinta ta mike tsaye ta isa gurin kofar falon ta tura, da kamar fargaba ta kwankwasa kofar dakinsa bayan ta tura kofar ta ji ta a rufe. Sanin kansa ne mahaifinsa ne kadai zai kwankwasa masa kofa idan ya rufe sai kuma kanensa wanda ya tabbatar a yanzu bayan gidan, idan ba dayansu ba ne to mahaifiyarsa ce, ba zai iya barinta ta yi ta tsayuwa a jikin kofar dakin tana jiransa ba, haka kuma ba zai iya ce mata ta tafi ta kyale shi ba, kamar yadda ba zai iya hana ta shigowa ba, a dole ya sauko da kafafuwansa daga kan gadon ya taka ya isa gurin kofar ya cire key din ya murda kofar ya bude, ya maida dubansa kasa kuma ya kasa furta mata komai.

“Zamu iya magana? Maleek”

“Akan me Ummi”

“Ka shigo ranka a bace me ke faruwa?”

Ya saki kofar dakin ya juyo ya dawo gurin gadonsa ya zauna, sai ta zauna nesa da shi domin ita da ta haifi abun ta tafi kowa sanin halin danta ciki har da abubuwan da yake da kuma wadanda baya so.

“Me ya faru? Na san laifin da kanwarka ta yi maka be isa ace shi ya haifa maka da wannan fushin da na gani a fuskarka ba, fada min miya faru?”

“Ummi”

“Na'am”

Ta amsa tana kallonshi.

“Kin san idan ina da damuwa Abiey nake fadawa ko? Ban saba zama dake na fada miki matsala ta ba, haka ne?”

Ta daga masa kai.

“Na gode da kulawa bari naje waje na sha iska...”

Kamin tace komai har ya mike tsaye ya bude kofar dake dakin ya fita ta backyard ya rufo kofar ya barta a gurin zaune. Lumshe ido ta yi tana jin wani abu na mata yawo a zuciya.

“Ya Allah kar na rasa wannan ma, na rasa ďan da nake kauna, wannan ka sani Allah ina kaunarki, amman yana ta kara yin nisa da ni, Allah ka taimake ni kar na rasa shi”

Addu'ar take yi ma kanta ba tare da ta daga hannu sama ba, domin da hannaye ta tare hawayen da suke zubo mata, cikin rashin kuzari ta mike tsaye ta fice daga dakin. Sai dai Maleek ya dauki lokacin da yake kyautata zaton Ummi ta fice daga dakin sannan ya mike tsaye yana kallon harabar dake cike da iska mai dadi ga itatuwa na ta kadawa.

“Mi na aikata da nake ta karbar wannan sakamakon? Why? Me zai saka na tsani mata me suka yi min? Allah ka sani ina cutuwa, Allah ka yaye min damuwata ka ba ni lafiya idan cuta ce take damuna”

Ya koma zaune cikin damuwa, ba zai iya zaunawa yayi hira da mahaifiyarsa ba, and no matter me yake damunsa ba zai iya fada mata ba, saboda baya son hirar ta tsawaita, amman a haka kullum tana yawan nuna masa kulawa tana son ta kusantarshi irin kusanci uwa da ďa, shi ma wani lokacin idan yana cikin damuwa ya kan ji kamar ya same ta ya fada mata amman ba zai iya ba.
Hannunnsa ya saka ya tare hawayen da suka cika idonsa suke kokarin zubowa a kumatunsa.

____________________

Maleek anya rayuwa zata yi a haka?
Team Waira marar son wanka ina kuke 😂
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.