Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 198 of 227
“Toh a bar mu mu kara mana, sai a gane waye jarumi”
Ya fada da kakkausar murya yana tabe baki kamar zai yagashi.
“Ba mu taba gwada yaki ba, kuma ba zamu gwada saboda wata korariya a garinmu ba, ban yi tunanin karfin tsafi zai yi tasiri a gareshi ba, ko da ya ce ba zai aureta ba, ba samu yarda ta aura daga garemu ba wannan shine magana ta karshe”
Eid da duk sauran mutanen da suke fadar suka risnar da kai domin nuna biyayya ga Umarnin Sarkin da ba a musawa. Eid ya dago yana kallon Maleek fuska kamar an aiko masa da mutuwa, zuciya kamar bakin maciji dake cike da dafi, ya fice daga fadar yana hararar Maleek yana huci kamar zai fitar da hayaki. Duk wani abun da ake fada Maleek be ji ba, domin da yarensu suke maganar, Waira kuma jinta da ganinta tunaninta mamakinta zuciyarta da ruhinta gaba daya sun tafi gurin mutumen da take kira da yayanta wato Ya Maleek. Furucinsa na cewa yana son aurenta da jarumtar da ya nuna akanta sadaukarwa neman kareta sassauta ra'ayinsa da nema mata farinciki da yanci wani abu da ya kai ta rubuta a dutsen da ba goge zane da alkalamin zinari. Hawaye take irin hawayen da ba zata iya fadar na minene ba a yanzu, na farincikin abun da Maleek yayi mata ne ko kuma na samun yancinta ko kuma na komawa da zata yi gurin matar da ta zame mata uwa? Ko kuma dai na fasa kasheta da aka yi ne? Wata kila kuma na tsafin da suka ce sun yi ta aikawa Maleek ne be same shi ba.
“Nuwaira...”
Kamar wadda aka jefowa numfashi daga sama haka ta zabura ta dawo hayyacinta, sai ta lumshe ido tana jin ba a taba kiran sunanta da dadi kamar yadda Maleek ya kirata a yau ba. Rufe idon da ta yi sai ya saka shi tunanin ko bata ra'ayi ne musamman ma da yayi arba da hawayen dake zuba a idonta gashi tun da ya furta maganar take kallonsa ta kasa cewa komai kuma ta kasa dauke idonta daga gareshi.
“Ko baki so ne? Karki damu, na yi hakan ne saboda na sama miki hanyar fita daga garin nan, idan sun amince sun ba ni aurenki da zarar mun fita ba aurenki zan yi ba, za a miki aure ne best on zabinki”
Rashin Eid a fadar da zai iya fassara musu abun da Maleek yake fada, ya saka Sarkin amfanin da nasa baiwar ta tsafi ya yi communicating da aljannunsa suka fassara masa abun da Maleek ya fada, hakan kuma ba karamin dadi yayi masa, domin ya fahimci Maleek ba gaske yake son Waira ba, hakan na nufin zai fara mata yi mata butulci da zarar sun bar garin kenan, kuma hakan ya nuna Waira bata son shi, a kokarin Sarki na bakanta musu ya kalli na hannun damansa ya ce.
“A fadawa Dardu ya tada busa ya hura wuta, mata su fara nika ganyen za a daura aurensu a yanzu”
Nuwaira ta bude ido da sauri ta kalli Sarki domin daga ita sai jama'ar garin suka iya jin abun da Sarki yake fada ban da Maleek. Sarki ya kalleta yana tana tauna hakora ya ce.
“Zamu aura miki shi, kuma zamu cire duk wani tsafi da kariya ta mu da take jikinki yanzu nan, kuma duk wani abun da zai faru ko ya biyo baya karki neme mu, babu mu babu ke da zuri'arki”
Kasa cewa komai ta yi sai har lokacin hawayen ba su daina sauko mata ba.
[8/12, 6:08 PM] 🦋-🦋: 77
Duk wata al'ada da ake gudanarwa kamin bikin auren sai da sarkin ya saka ka yi ta, ba a daura auren ba sai da suka hanka hannun Nuwaira suka cire layar dake cikin hannun nata, suka shafe jikinta da maganin da ke karya duk wani kalar tsafi na mutum, sannan aka daura musu auren har aka yi aka gama kuka take na azabar cire mata layar da aka yi a hannu. Maleek ya nemi izini ya koma masaukinsu ya dauki wayarsa sannan suka rakosu har bakin kofar garin suna tafiya ana wasa farar kasa a duk inda suka taka da haka har suka fita daga cikin garin. Kamin su isa gurin da motar Maleek take Nuwaira kamar zata fadi taka take taka kasar kafarta babu talkami ga jikinta sai rawa yake tana jin wata kalar azaba kamar an tsaga mata duka jikin. Maleek ya rigata karasa gurin motar ya bude mata back seat ta shiga ta kwanta domin bata iya zaman kirki ma, tun da ta rufe ido bata bude ba har ya kama hanyar Abuja. Sai da yayi tafiya mai nisa kiran Ameer ya shigo wayarsa shi har ya manta da waya a jikinsa ma sai a lokacin ya tuna. Hannu daya ya saka ya ciro wayar aljihunsa dayan hannun kuma yana driving da shi all his thoughts is Ummi ko Abiey ne ya kira but ga mamakinsa sai yayi arba da Number Ameer, haka nan kawai ya ji baya bukatar amsa kiran dan haka ya aje wayar a gefen seat ya cigaba da tukinsa a haka Ameer yayi masa kusan miss calls 30 da ya gaji da jin ringing din ne ya dauki wayar sai ya kiran Abiey ne ke shigowa wannan karon and ba zai ki amsa kiran mahaifinsa haka nan kawai ba.
“Hello”
“Maleek kana ina? How are you? Are you okay?”
“Ina lafiya kalau Abiey babu abun da ya same ni Nuwaira ce kawai bata da lafiya ina hanyar Abuja yanzu haka tare da ita”
“Alhamdulillah, amman me kake nufi tare da ita?”
“Labari ne mai tsawo Abiey but at the end dai sun ki karbarta sun yafe ta, and sun aura min ita bayan sun rabata da duk wani tsafi da yake jikinta”
“What? Okay Allah ya kawo ka lafiya”
“Ameen ina Ummi?”
“Tana saurenka muna tare da kowa a nan ka kula da hanya, mun yi magana da police akan cewar za su tafi yau su taho da kai bari na kira na fada musu kana hanya”
“I will”
Ya aje wayar ya maida hankalinsa gurin tukin yana yi yana dan juyawa ya kalli Nuwaira da idonta suke rufe.
“Nuwaira Nuwaira”
Ta bude idonta daker ta kalleshi.
“Sannu”
Bata amsa masa ba ta sake maida idon ta rufe. Haka yayi ta da ita har suka fara jiyo kamshin garin Abuja, ba shi tsayawa komai sai Allah ko ruwa be sha ba tun da suka bar Katsina har suka kusa isa Abuja. A lokacin da ya isa da ita cikin garin Abuja be sauka a ko'ina ba sai asibiti, domin ya lura da Nuwaira ta galabaita har bata iya bude idon ma idan ya kirata sai nishi take kamar mai nakuda.
AMEER POV.
Cikin wani yanayi na rashin lafiya ya isa gidansu Humairah ba dan ta kira a waya ya kasa amsa ba kuma yayi mata alkawarin zuwa ba da ba zai tafi a wannan yanayin da duniyar bata mishi dadi ba. Yana fakawa harabar gidan ta fito ta tarbe shi da far'ar irin na zumudin ganinsa sai dai yanayinsa da ta ganin bayan fitowa daga motar ya saka jikinta yayi sanyi daukin ganinsa da take sai ya ragu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.