Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 164 of 227
“Humairah ba zaki gane ba, ni ban yi da cin mutuncinsu a bakin gaskiyata nake nufin biya duk abun da aka kashe da za su muna min gadara da shi a gidan”
“Sun raga maka da ba su hada maka da duka ba, Ameer ko kana so ko baka so dole na fada maka gaskiya domin ni yar'uwarka ce a yanzu, ina son na ga ka gyaru rayuwarka ta yi kyau, abun da ka yi be dace ba, kuma hakan yana kara bata alakarka da su ne kawai”
“Humairah ina son yarinyar nan, na lura so kike su yi amfani da wannan damar su cutar da ni saboda ita”
Humairah ta juyo ta kalleshi.
“How much do you love her?”
“Very much”
“Kamar yadda Nimra take son ka ko kuma ya dara?”
Ya kalleta irin me ya kawo wannan maganar a nan.
“Saboda tana maka son da har ka mutu ba zaka samu wata mace mai sonka kamar ita ba, son da ya saka zuciyarta bugawa a lokaci daya kuma ta rasa rayuwarta, amman kasan abun da ya fi komai ciwo? Kai baka taba sonta ba, kuma ka yaudareta”
“Ba sai kin tuna da wannan ba, already I'm hurt”
“No you didn't da baka fada son Waira ba, yarinyar da zan iya tabbatar maka da babu soyayyarka a zuciyarta, amman ka fara fada da dan'uwanka akanta, kai ma kuma kana sonta saboda kyaunta”
“Ba saboda kyauta nake sonta ba, i just love her, saboda ita na yi ma Daddy karya cewa na aureta tun kamin yau, kuma da wannan damar zan yi amfani na raba ta da gidan Ummi, ta koma mallakina a karkashin ikona”
Humairah ta masa kallon mamaki.
“Me yasa ka yi haka?”
“Saboda na lura Daddy na son gabatar min da wata a matsayin matar aure, ni kuma zuciyata a yanzu Waira kawai take so, daman ban taba son wata mace ba sai ita”
Dauke wuta Humairah ta yi na dan lokaci kamin ta samu damar sauke ajiyar zuciya.
“I thought you change”
“I changed shiyasa zuciyata ta fara son Waira”
“Amman ka fada min tana da duk wani abu da kake so a jikin mace, kai ma kuma kana da duk abun da mace zata so a jikin namiji, amman Waira ba zata so ka ba, ba baki nake maka ba, kuma ba wai duba nake na gani ba, amman tabbas ko da ka auri Waira sai fitini da tashin hankali ya faru a tsakaninku, idan ma ka samu aurenta kenan”
Wannan karon kallonta yayi a tsawace ya ce.
“Dole na samu aurenta, ke ba malamar duba ba ce baki isa ki fada min abun da zai same ni ko ya faru ba, sake miki da nake ya saka kina ganin kanki daidai da ni har kina fada min magana anyhow”
Ta yi murmushi.
“Ada can ma da nake kallonka a matsayin dan Mr Bashir na fada maka balle a yanzu da na san waye kai? Ni da kai duk daya ne Ameer, banbancin ni da kai, ni bana iya butulcewa wanda ya kyautata tun da kurciya har girma, sannan idona ba ya rufe ka kasa fahimtar mai so na, kana girma amman kana rayuwar da kanenka na goma na baya irinta, ai ko dan kunyar abun da ka yi ma Nimra be kamata ka kalli idon Ummi ka ce zaka yi jayayya da ita ko mijinta akan wata yarinyar da ka kasa sonta da taimaka mata a lokacin da take da muni ba, sai da suka rike ta suka wayar da ita suka gyarata ta yi kyau sannan ka fara sonta, kuma har kake fadar kana kaunarta. Ameer baka canja ba, kuma ba zaka taba canjawa ba sonka ya maka yawa, baka kula kowa sai kanka”
“So now ke ma ganin laifina kike bayan duk abun da ya faru da ni”
“Me ya faru da kai? Me ka rasa? Barin ka da Ummi ta yi ya saka ta rasa wani abu? Gashi amman ka kasa cire haka a ranka kullum laifi kake dora mata, and now na yi tunani ko rayuwarka Mr Bashir ya ce yana so zaka cire ka bashi saboda ya rike ka kamar dansa, kuma ya so ka fiye da yadda kaken son kanka, ka juya dukiyarsa da duk wani abu da yake da iko da shi a yadda kake so, and now saboda zai gabatar maka da auren wata wata kila yarsa ce sai ka bijiro masa da karya? Idan ya gane gaskiya anya zai sake rikonka a matsayin da? Ameer ina fada maka gaskiya ne saboda ina yar'uwarka kuma ina ji maka tsoron abun da zai je ya dawo, Mr Bashir be cancanci butulci daga gareka ba, haka Ummi bata cancanci cin mutumcin mijinta ko yayanta akanka ba, duk ranar da Ummi ta bar duniya zaka gane ka yi kuskure”
“Baki taba soyayya ba, bakin yadda ake ji ba, what if Abiey yana som aurawa Maleek ita fa? dan haka... ”
Be karasa ba ta tari numfashinsa tana daka matsa tsawa kamar wani sa'anta.
“Toh yanzu ka san yadda ake ji ai, zaka dandana kwatankwacin abun da Nimra ta ji a yanzu, domin hakkinta ba zai barka ba. Kuma Allah ya waddaranka Ameer tirrr da dan'uwan da zai zabi soyayya sama da mahaifiyarsa da dan'uwansa, da kuma mutumen da ya rike shi kamar dansa.... A yanzu kana kokarin datse soyayya ne bayan kuma ka ki karbar soyyayar dake hade da rayuwa, har sai da mai soyayyar ta rasa rayuwarta, ban yi farinciki da kasancewar dan'uwana ba a yanzu dan'uwan dake share hawaye nake so, wanda zan kalla na yi alfahari da shi ba wanda zan kalla na tuna ya cutar da wasu ba, ya nuna son kai a rayuwarsa sama da ta wasu ba, and should be the last time da zaka rumgume ni, ni ba yar'iska ba ce ba zan yarda ka lalata min rayuwa kamar yadda ka lalata ta Nimra ba”
Ta fisgi jikinta da karfi ta fice harabar ta barshi tsaye da mamaki da kuma karin bakincikin wanda yake ciki. A duk fadin duniya a lokacin da yake jin kansa da kuma a yanzu da yake sauke girman kansa Humairah ce kadai macen da zata kalleshi ta fada masa magana son ransa kuma ya kasa yi mata komai. Ta fada masa maganar da tafi wanda Namra da Maleek suka fada masa, gaskiya take fada masa ko akasin haka shi a yanzu ba zai gani ba, domin idonsa rufe suke akan Waira, shi dai ya san yana sonta kuma ya shirya batar da komai akanta zuciyarsa bata taba kamuwa da son wata mace ba sai Waira, kuma ba zai iya juriyar rasata ba.
HUMAIRAH POV.
Cikin asibitin ta koma tana tafe tana hawaye har ta isa bakin kofar dakin da Hajiya take, bata damu da goge hawayen ba ta tura kofar haka ta shiga fuskar shakab sai kuka take kamar wanda akai wa mutuwa, kalaman da ta fadawa Ameer ne suka cinta, bacin ran da ta saka masa ne abun yake damunta, me yasa bata iya rike bakinta ta ta fada masa duk kalar maganar da ta zo daga bakinta? Why? Gashi a yanzu tana jin zafin abun kamar ita aka fadawa bacin ran da ta gani a idonsa ya hana hawayenta tsayawa, tana shiga ta fada jikin mahaifiyarta dake hira da Hajiya ta fashe da kuka ta zauna a kasa kanta a cinyar Bahijja.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.