Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 227

“Wai waya maka wannan abun ne?”

Momy ta tambaya a yayinda yake goge fuskarsa da tawul.

“Wani banza ne, ai sai na masa hankali”

Tana jin haka sai jikinta yayi sanyi, domin ta san a cikin biyu dole ayi daya, wanda ya aikata wannan abun be san waye Ameer ko kuma wani ne wanda ya fishi isa da jin kai, tabbas ta san Ameer ba zai kyale ba sai ya rama, wanda ramuwar zata iya zama ta zalinci ga wadanda suka yi laifi ko kuma ta zama kofar budewar wata sabuwar fitinar domin shi ma wanda za ayi ma ba zai kyale Ameer ba.

“Wannan zafin zuciyar duk na minene Ameer miya hada ku?”

“Abokina ne ďan group din mu ne”

“Ai zaka iya yafe masa indai har abokinka ne, Manzon Allah Sallalahu alaihi wa'asalam.... ”

Bata karasa ba ya mike tsaye ya nufi inda keys dinsa suke ya dauka.

“Bana bukatar wannan kullum da anyi abu ki wani fara yi min wa'azi bana so, musulunci be yarda a cutar da kai ka kyale ba”

Ya fada mata sannan ya fice a fusace, binsa ta yi da kallo har ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya.

“Wannan fushin naka yayi yawa Ameer, dole ne na fara baka ragowar ruwan sallah La'asar saboda ka rage wannan yawan fushin, sai dai ta yadda zaka yarda ka karba ka sha ne matsalar”

Tana rufe baki Ameer ya turo kofar dakin ya shigo, sai da gabanta ya buga sau hudu a lokaci daya.

“Ka yi mantuwa ne?”

“Sarewata zan dauka”

Ya amsa mata da muryar dake kara bayyana har yanzu akwai fushi da bacin rai a tare da shi. Boutique dinsa ya shiga ya bude box din da yake ajiyar sarewar ya daukota tana kamshin turare ya fito, ko kallon inda Momy take tsaye yi ba ya fice. Yadda yake saukowa stairs din sai ka dauka fasa kasa zai yi domin da karfi yake sauke ko wane taku na kafarsa a kasa har suna fitar da amo.
Aljannun tsabtarsa ba za su bar shi ya shiga motar da ya dawo da ita yanzu ba, saboda gani yake kamar yawun da Maleek ya watsa masa a fuska sun shafi motar daman rigarsa tun a hanya ya cireta ya jefar. Wata motar ya nufa ya cire ledar da aka saka aka rufe ta ya jefar kasa ya bude motar ya shiga yayi mata key, kamin ya isa gate masu aikin bude gate din gidan har sun kammala aikinsu domin sun fi kowa sanin yadda ya tsani jira a bude masa gate.
Tuki kawai yake ba dan ya san gurin da zai tafi ba, baya son zuwa gurin abokaninsa domin ya san za su dame shi da maganar Maleek ne, kamar yadda Step mother dinsa ta fara bashi hakurin akan abun da bata sani ba wannan dalilin ya saka ya baro mata gidan ba dan yana da gurin zuwa ba sai dan ya jira daga wa'azin da take son yi masa.

Gefen wasu manyan itatuwa ya faka motarsa, nesa da wata motar yan mata guda biyu dake zaune gefen motarsu sun shimfida carpet suna ciye ciyen kayan kwalan da maskulashe. Fitowa yayi rike da da sarewarsa a hannu ya hau bayan motarsa yana ta kallon titi da babu motoci sai jefi jefi, har lokacin zuciyarsa tafasa take tana wani tiriri, be taba jin kaskanci da wulakanci ba irin na yau da Maleek ya tofa masa miyau a fuska, Ameer yana ganin babu wanda ya isa yayi masa wulakanci ko ya tozarta shi sai dai shi yayi ma wasu, amman a yau Maleek ya masa kuma a gaban friends dinsu.

“Tun da ka fara sai ka karasashi Maleek sai ka kai kasa da guiwoyin ka kana ba ni hakuri Maleek”

Har wani tauna hakora yake yana furzar da numfashi da karfi kamar shi yayi masa laifi. Ya dade yana kallon sarewar dake hannunsa sannan ya kaita bakinsa ya fara busawar irin busar da babu wanda ya iyata a isa saninsa sai shi da wanda ya koya masa, yana jindadin busar sarewa ko wace kala ce balle kuma wannan da take ta musamman a gurinsa, tana saukar masa da nishadi a duk lokacin da yake yinta, lumshe ido yayi yana busar cike da karewa. Fararen yan matan dake zaune gefen motarsu suna motsa baki suka fara kallon junansu da mamaki, kamin su mike tsaye suna lekonsa.

“Wow.... Nimra kin ji wannan?”

Dayar ta fada tana kallon dayar dake kokarin rufe kanta, sai duk suka yi murmushi suna jin yadda busar ki tsara iska tana shiga kunnuwansu kamar ana musu susar kunne. Wanda aka kira da Safna ce ta fara daga kafa ta taka zuwa gurin motarsa tana lekensa, kamshin turaren da ya ji ya banbanta da na shi ne ya sanar masar akwai wani bakuwar hallita a kusa da shi, a take ya daina busar ya bude idonsa a hankali, wani karamin yaki ya murza da idonsa da zuciyarsa dake mugun bugawa da karfi kamin ya samu nasarar kawar da idonsa a cikin kwayar idonta.

“Ya aka yi?”

“Busa muka ji kana yi mai dadi”

Ta fada tana kallonta with smile on her face, shi ma murmushi yayi kamar ba shi ba, ya dan daga kafada sannan na sauko saman motar, ba tare da ya sake cewa komai ba ya bude motarsa ya shiga ya bar ta a gurin tsaye.

WAIRA POV.

Al'adarta ce yin rawa ko babu kida hakan ya saka ta sauko tsaunin da ta hau tana taka rawar kamar yar makada. Eid ya karaso gurin ya mika mata hannunsa ta rika ta karasa saukowa.

“Abinci zan ci yanzu”

Ta fada da yarensu, ya gyada mata kai.

“Mu je gida mu ci”

“Lambu zan je”

Ta sake hannunsa ta nufi hanyar da zata sadata da lambun da gudu tana gudu tana tsalle har ta isa, bata bi ta kan yayan itatuwan da suke take akan itacecen ba ta fara daukar wadanda suka fado kasa tana ci, wani ma tsuntsaye sun ci shi amman bata damu ba take ci haka nan, ba tare da ta wanke ba sai dai wanda ta tauna da ji da kasa sai da zubar.

“Da kin wanke dai Waira”

Ta juyo da sauri domin ta firgita bata san da mutum bayanta ba, ganin Eid ya saka ta lake kafada daya ta fara yin baya baya.

“Atud shie”

Be ma'ana ba zata wanke ba, shi ma dai ya san fada kawai yayi domin bata da kyama ko kadan, kuma bata da tsabta ita da kasanza kamar twins ne, da za a bashi neman wani abu da Waira ta wanke shi kamin ta ci am ba shi babban aiki, komai kazanta guri zata iya kwana kuma ta tashi ba tare da ta wanke jiki ba, wannan ya saka dakinta yake cike da beraye da jajayen zakaru da wani lokacin ma a tare take cin abinci da su, basa tsoronta har rufa take dasu idan zata kwanta, berayen kam ta sha saka su a aljihunta ko a rigarta tana yawo da su. Tun abun yana damun Eid yana mata magana har ya gaji ya fara saka mata ido, domin ba zai iya canjata daga yadda take ba, haka kuma ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma yawan yi mata magana yana saka su yin fada.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.