Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 13 of 227
“Mi... Mi... Miye... Ha.. Ka...”
Ya furta daker sai kuma bachi ya sake yin gaba da shi, har saurayin yayi abun da zai yi ya gama ya fita motar ya zagaya side din da Maleek yake ya ciro wayar Maleek ya kashe ya maida masa aljihunsa sannan ya rufe motar yayi tafiyarsar.
Haka Maleek yayi ta kwasar bachi a motar tun karfe biyar na yamma har garin Allah ya waye. Shi ma saboda rana ta fara haska idonsa ne motsawa ya fara yi a hankali yana jin yadda jikinsa yayi tsami a ko'ina kamar ba na shi ba, wutansa sai ciwo yake har ya haifar masa da tari.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un miya faru ne”
Ya tambaye kansa yana murza idonsa wannan lokacin ciwo suke masa tsakanin jiya da suke masa nauyi, gaba daya ya kasa tuna abun da ya faru, gashi ya gagara gane inda yake.
“Ya salam”
Ya fada kansa ya sake maida idon ya rufe ya dauki tsawon lokaci a haka sannan ya bude idon cikin rashin kuzari ya mika hannunsa ya bude motar ya fita ya tofar da yawun bakinsa yana karewa gurin kallo.
“Ina ne nan kuma? Miya kawo ni nan?”
Ya sake risinawa cikin motar ya dauko gorar ruwa dake cikin motar ya wanke idonsa ya kurkure bakinsa sannan ya saka hannu ya lalabo wayarsa ya kunna kamar jiran yake a kunne wayar sai ga kiran mahaifiyarsa Hajiya Zahra ya shigo a take.
“Hello”
“Maleek kana ina? Ina kake? Me ya same ka?”
Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai fada, ya daga gorar ruwan ya cika bakinsa ya hade.
“Miya faru?”
“Kamar ya me ya faru? Tun jiya baka dawo gida ba kuma wayoyinka a kashe ko'ina na bincika ba a ganka ba”
“Yeah...”
Ya fada yana tuna abun da ya faru, jiya yana tare da abokansa ya fara jin bachi, ya shiga motarsa har wani saurayi ya zo ya taimaka masa.... Kamar walkiya haka komai ya dawo masa a akwakwalwa lokaci daya ya tuna komai da sauri ya jefar da ruwan dake hannunsa.
“Who's that guy?”
Ya tambaya a yayinda wayar take a kunnesa.
“Waye?”
Ummi ta yi zaton sa ita yake, sai ya kashe wayar ya shiga motarsa cikin wani irin bachin rai da bakin ciki marar misaltuwa, kam yayi ma motar key kira ya sake shigowa a wayarsa, daga Abiey har na Kannensa da abokansa be daga ko daya ba, tukin kawai yake yana tuna yadda saurayin yayi kissing dinsa kamar a mafarki. Ransa be kara baci ba har sai da ya isa gidansu yana faka motarsa mahaifiyarsa da kanensa suka fito da sauri sannan mahaifinsa dake bayansu, kallo daya yayi musu ya fahimcin suna cikin tashin hankalin rashinsa musamman ma mahaifiyarsa da har lokacin kuka take, ta matsa kusa da shi sosai kamar ta rumgume shi sai dai babu dama domin danta baya son haka.
“Maleek ina ka shiga? Ka daga mana hankali miyasa ka kashe wayarka?”
Kamin ya amsa tambayar Ummi Mahmood ya jefo masa tasa tambayar.
“Ina ka shiga Maleek? Jiya babu wanda yayi bachi a gidan nan kuma an bincika ko'ina ba a ganka ba”
Ya dauke idonsa daga kallon kanensa ya kalli Abiey da shi ma tambayar yake masa.
“Ina ka shiga Maleek?”
Ya amsa kiran wayar da Abdull yake masa.
“Abdull ina gida”
Ya sauke wayar ba tare da ya jira abun da abokinsa zai tambaya ba. Sannan ya kalli mahaifiyarsa dake ta zubar da hawaye tausayinta ya kama shi.
“Ummi lafiyata kalau”
“Ina ka shiga?”
“Ban sani ba, na fito daga inda muke zama zan dawo gida na kwanta sai bachi ya dauke ni”
Cikin kallon rashin fahimta Abiey ya ce.
“Shigo ciki”
A tare suka dunguma gaba daya suka shiga cikin falon, kowa ya samu guri ya zauna sai kallon Maleek suke da idonsa suke da ja har lokacin ga wani ciwon kai da yake jin yana son saka shi gaba. Ya fara shimfida musu labari tun daga fitarsa gida har zuwa isarsa Q-town da abubuwan da suka faru be boye komai ba ciki har da kissing dinsa da Guy yayi.
“Maybe wani abu aka saka maka a drinks din”
Mahmood ya fada Maleek ya kalleshi yana daga masa kai.
“Ni ma abun da nake tunani kenan, kuma shi ma wannan saurayin turo shi aka yi”
“Wa zai maka wannan?”
“Wannan kuma sai na natsu ko kuma wani za'ayi ma aka yi kuskure”
“Ko dai abokin da kuka samu matsala da shi ne?”
Abiey ya tambayar yana kallon wayar Maleek dake ringing.
“Karka daga wayar nan, bari mu gama magana”
Maleek ya aje wayar gefe ya shafa kansa.
“Ba na jin zai yi haka”
“Wani lokacin wanda baka tunani shi zai aikata maka abu, wata kila kai baka dauki abun da zafi ba amman shi ya dauka kuma gashi har ka ce wani yayi kissing dinka wannan abun ba a saba da shi ba, kuma baka san manufarsa ta yin haka ba”
Cewar Namra cike da damuwa.
“Siyasa ai ba zamu kyale ko waye ba, musamman yadda ya tashi hankalinmu a gidan nan jiya, a inda ya kaika ya aje wani abu zai iya samunka a can din ma, kuma duk wanda zai maka wannan abun zai iya silar rasa rayuwarka, dole mu gane ko waye wannan tun daga kan drink din da ka sha”
Abiey ya fada with serious face, Maleek ya kalleshi cikin yanayin dake nuna baya son iyayens su shiga cikin lamarin domin yana jin kamar Ameer ba zai iya masa haka ba, duk kuwa da kasancewar wani bangare na zuciyarsa na raya masa shi din ne.
“Abiey wannan a tsakaninmu ne?”
Hajiya Zahra ta daka matsa tsawa.
“Wani irin a tsakaninku? A tsakaninku wani zai maka haka? Wannan shi yake nuna friends dinka ba mutanen kirki ba ne, su waye ma friends din duk ba mu sani ba, basa zuwa gidan nan sai dai ka je can kana haduwa da su wani guri”
Abiey ya saka hannunsa ya ciro wayarsa dake aljihun jallabiyarsa yayi dialing.
“Duk masu aikin gurin sai an dauresu sai sun fadi wanda ya saka su”
“Abiey kar aja abun nan da nisa kar aje inda ba a so”
Cewar Maleek domin ya fi son a bar maganar a hannunsa.
“Ba za a bari ba, Maleek kuma sai an hukunta yaron nan ko dan gidan uban waye, domin zai iya kashe ka ma”
Ummi ta fada cikin bacin rai, Nimra ta ce.
“And the most annoying part ma Yaya baya iya zama ya fadawa kowa damuwarsa sai dai ya bar abu na cinsa Allah kadai ya san abun da ya faru a tsakaninsu amman be fada ba, gashi abu har ya fara wuce gona da iri”
Kallonta kawai Maleek yayi ya mike tsaye ya nufi hanyar stairs.
“Ja ka a duba lafiyarka, whats if yayi poisoning dinka?”
Ya juyo ya kalli mahaifiyarsa dake maganar.
“Zan je, wanka zan yi na yi sallah tun jiya ban yi magariba ba”
Sannan ya juya ya hau sama yana jin yadda Abiey yake yi ma abokinsa bayanin yadda ďansa ya dawo.
“Ba zan sake bari ya rabi friends dinsa ba, ba mu san su waye yake abota da su ba, ji yadda suka saka shi ko sallah be yi ba, dole ne a hukunta ko waye....”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.