Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 184 of 227

“Kin dawo gida, idan zai saka ki a mota dubu ba zata tashi ba, Sarki ne yake kira dole ne kuma amsa kiran, kai na idan ka shiryawa mutuwa ka taho mu tafi”

“Idan har zan tafi ba tare da ita ba, ba zan taba samun kaina cikin aminci ba, zan yi tunanin wane hali take ciki, kariyar da muka mata alkawari ba mu cika ba, saboda haka ba zan iya tafiya ya bar yarinyar nan ba”

Eid ya juya baya ya nuna ma Maleek kofar. Office yayi saurin karasowa kusa da inda suke

“Maleek karka yarda ka shiga baka san manufar ba”

“Ku dai ku tafi babu mai cutar da wani sai Allah zan fito lafiya na muku alkawari”

“Maleek...”

Dayan office ya dakatar mai kokarin hana Maleek.

“Ranka ya dade ra'ayinsa ya bi, mun dai mun yi iya namu idan ya ji zai iya shiga ciki sai masa addu'ar fitowa lafiya”

Duk yadda suka so su yi convince din Maleek kar ya bi Nuwaira be sauraresu ba, not just because of Nuwairar kanta, har dan yana son na nunawa Eid ba zai iya masa komai ba sai abun da Allah ya hukunta masa. Su dai kam ba za su iya kasada ba dan haka suka shiga motar su suka masa sallama suka tafi aka bar shi a gurin daga shi sai Nuwaira da Eid da kuma mutanen da ke bakin kofar garin suna jiran isowar Nuwaira.

“Yanzu zamu iya shiga da motar?”

Eid ya watsa ma Maleek wani mugun kallo ya kai hannunsa ya rika hannun Nuwaira sai ta fisge hannunta.

“Karka sake taba ni, ni a yanzu musulma ce haramun wanda ba dan'uwana ko uba ko mijina ya rike ni, na canja addini a yanzu ba addinina daya da kai ba, kamar yadda ba zuciyarmu ta banbanta”

Daga Maleek har Eid din kallonta suke babu wanda ya ce mat uffan. Eid ya juya ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya kalli Maleek daga sama zuwa kasa ya dauke kai ya cigaba da tafiyarsa. Sai da ya ba su tazara mai yawa sannan Maleek da Nuwaira suka bi bayansa, kamin su iso an bude kofar garin mutanen dake jiranta suka matsa suka bata kofa ta wuce tare da Maleek, ban da mamaki da kallon ikon Allah babu abun da Maleek yake, shi ko a mafarki be taba ganin mutane masu kalar tufafin da ke sanye a jikin jama'ar garin ba, daga maza har mata babu wanda yake sanye da rigar da ta sauko masa har masa, kuma babu wanda ya saka tufafin da suka suturta jikinsu kamar yadda shi yayi ko kuma Nuwaira. Tun daga kan gine ginen garin zuwa abubuwan amfaninsu gaba daya Maleek be taba ganinsu ba, domin bw rayu a kauye ba balle ya san wasu abubuwa, haka ma ba dan da ba ne balle ya ce ya taba ganin yadda rayuwar baya take. Sai dai wani abun da ya bashi mamaki ganinsu tsab tsab ba kamar yadda ya fara atba da Nuwaira ba da kazanta, yayi zaton zai tararda kusan rabin garin da kazanta amman be ga haka ba. Duk gurin da suka ratsa kallonsu ake wasu na mamakin dawowar Nuwaira tare da wani, bayan an yi shelar ta gudu, wasu kuma na mamakin yadda ta sauya tufafin jikinta take tare da wanda ya aaka tufafin da suka banbanta da na su, ga kuma fatar jikinta dake sheki farinta ta fita fess kamar wadda aka sauyawa mata.

A madadin ta bi hanyar gidan Sarki sai ta zabi dauke hanyar da dakinta yake, bangaren da take rayuwa a gurin da ta girma, kuma gurin da ta gudu ta bari, tna tafiya tana tunanin yadda rayuwa zata kasance mata ita da Maleek domin abu ne mai wahala ace Sarki ya yafe mata ita kanta da take yar garin balle kuma Maleek da ya karya dokar garin bayab yayi hayayya d Eid, idan ma sarkin ya yafe mata to zai tabbatar da mata da kudirinsa na bata sarauta ne, abun da take ta fargaba tun farkon tashinta, saboda ta san idan ta haihu mutuwa zata yi kamar yadda aka kashe iyayenta bayan haihuwarta, kuma addinin da ta sauya a yanzu ba zata iya aje shi ba, tufafin ba zata daina sakawa ba, haka ma abincin garin Garuk bata jin zata iya cinsa a yanzu, rayuwa a dakin kasa da babu wuta babu ac babu kujera babu babban gado, babu mai damuwa da tashinta ko bachinta anya zata iya a yanzu?

“Ina ne?”

Tambayar Maleek ce ta dawo da ita daga dogon tunanin da ya kwashe ta har ta iso gurin ba tare da ta sani ba. Gaba dakin ya kara lalacewa wani bangare na dakin ya rufga ciki, datti ciki ya karu daga ciki har wajen dakin kamar gurin zuba shara haka yake, sharar ma ta kazamai masu bari bola ba tare da sun tsabta ce ba.

“A nan na yi rayuwa, a cikin dakin nan na girma a nan makwancina yake, ci da sha na duk a nan suke abincina yayan itatuwa ne, zakaru da beraye ne abokaina”

Kusan mutuwar tsaye yayi yana kallonta, how come zata ce masa ta yi rayuwa a nan?

“Nuwaira ko dabobi ba za su iya rayuwa a nan ba balle mutum, ina danginki suke?”

“A nan muna kalar rayuwar da ba irin ta ku ba, babu mai damuwa da danginsa, idan ka zabawa kanka yadda kake so rayuwa babu mai ce maka domin me? Ba a takura maka ka canja baka takura rayuwar wani ka ce sai ya canja. Shiyasa nake mamakin rayuwarku kuma na yi mamakin yadda Ummi ta karbi ta nuna min soyayya da kauna ta rumgume ni ta ďanďana min dadin uwa”

Ya busar da iskar bakinsa a hankali be tana jin tausayin Nuwaira irin wannan karon ba, duk yadda yake tsammanin zai samu garinsu da rayuwarta abun ya wuce tunaninsa.

“Kuma a haka kike son dawowa? A haka kike son cigaba da zama a garin nan? Kalli yadda gurin nan yake”

Ta kalleshi tana hawayen tausayin kanta.

“To ya zan yi, ina da wani zabin ne?”

“Amman yanzu kika gama ce min an idan wani ya zabi yadda yake son rayuwa babu mai hana shi”

“Ba a ba mu wannan damar ba, mu ba a yarda mu aura daga wasu ko kuma wasu su aura daga garemu ba, ba yarje mana mu zauna a wani gurin mu yi rayuwa ta dindin bayan garin nan ba, sai idab wani laifin ka aikata aka koreka daga garin, balle kuma ni da idon kowa yake kaina”

“Wannan ba gurin rayuwa ba ne Nuwaira, Sarkinku ya danne muku hakki da yawa, kokarin bin tafarkin iyaye da Kakanin ya hallaka rayuwarku, duk wanda zai so ki rayu a nan ba masoyinki ba ne, babu wanda zai iya rayuwa a nan”

“Ni a nan zan rayu rayuwa a nan ya zame min dole, ba ni da wani zabi bayan wannan ba kowa yake sa'a da dacen rayuwa kamar ku ba”

Ya kai hannunsa ya saka yatsansa biyu tsakanin hancinsa ya cire hawayen da suka cika idonsa.

“Na ga hakan nima a yanzu, and Nuwaira you deserve a better life ya kamata ki yi magana ta fahimta da Sarkinku ki fada masa kin canja addini a yanzu kuma kina so ki yi rayuwa a wajen garin nan wata kila zai fahimta ya daga miki kafa”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.