Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 225 of 227
“Ka ji ko? Kuma zata iya baka wata fa tana da yan mata manya”
“Duk babu nata a cikin rikonsu take, kuma ni daga ake ai bana fatan kari”
“Ummi dai tace ka rike ni amana ai”
“Oh Ummi ta hada ni da aiki ko kallonki na yi kika ji baki gamsu ba sai kin tuna min da wasiyar Ummi, da ta rasu da na shiga uku da rigimarki, toh Allah yasa tana da rai dole a daga min kafa, kuma rike manar Ummi baya nufin a hana ni kara aure”
“Auren zaka kara kenan?”
Yayi dariya ya rumgume ta ta baya.
“You make me hate wannan Hajiya Jamila more, daman Ummi ta fada min duk abun da ta yi mata a can baya ai, ni bana son wanda be son Ummi kuma gashi tana cewa zaka kara aure”
“Wacan ai duk ya wuce yanzu, ba ki har ganin Ummi take Abuja ba?”
“Ni ban gani ba”
“Baki nan lokacin amman taje kuma ba gashi mu munzo ba? Ke tsaya ma wai me kika sani a auren mace biyu?”
“Na sani ba, ka dauka ni jahila ce? Islamiyar da muke zuwa ai ina ganin masu miji daya su biyu, kuma Malam yana mana bayani ai, ni bana son na ga wata macen ta so ka, shiyasa nake son gobe ta yi mu tafi gida ma”
Gefen fuskarta ya sumbanta.
“Ni bana da wannan ra'ayin ma, baki ga Abiey ba tun bayan rasuwar Mahaifiyarsu Yasmeen be sake aure ba, ni ma bana son yawan aure mata daya ta wadace ni da yarana biyar ko hudu kamar dai Ummi”
Ta juyo ya kalleshi.
“Ni ina so da yawa kamar goma”
“Zaki iya haifar yara goma”
Dirty words ya watsa mata a kunne sai ta daga kai, alamar ta yarda.
“Laa ashe yarinyar nan ta lalace yanzu bata da kunya”
Ta yi saurin rufe fuskarta tana dariya sai ya rungume ta a kirjinsa daman duk tsayin nata iyakarta kafadarsa. Kamin goben ta yi Nuwaira duk ta matsu daman can bata son zuwa ba ita dai ta tsani Hajiya Jamila tun a lokacin da suke daf da zuwa Ummi ta fada mata abubuwan da Hajiya Jamila ta yi mata, sai ta ji duk ta tsaneta daman kuma ita bata iya tsanar mutum ba, gashi kuma ta yi mata zancen yan matan da suke gidan ita kuma ta maida abun gaske. Misalin sha daya na safe jirginsu ya tashi daga Katsina zuwa Abuja, a duk zaman jirgin Ameer yana kusa da matarsa hannunsa cikin nata, ba motsinta ba har numfashinta lura yake da yadda yake fita da shiga balle kuma idan ta yi zaman da be gamsu ba sai ta ji kamar zai yi effecting babynsa dake cikinsa ne.
Two days da dawowar wani sabon laulayi ya kama rufe Humairah daman tun da ta samu cikin kusan kullum cikin laulayi take idan ta yi wata daya lafiya wata biyu ko uku da zai zo sai ta ci kwakwar wahala. Around 2am mai ya tasheta sai ta sauka saman gadon a hankali ta nufi toilet a kasa ta zauna ta tara bakinta a ta yi da kwara aman. Tana cikin yi ta ji Ameer a bayanta yana shafa bayanta da hannunsa sai sannu yake fada mata cikin yanayin damuwa, kusan abun da ta ci da rana sai da ta amaye tass sannan ta samu sukuni, yana wanke mata tana hawaye domin tana wahala sosai da cikin nan. Da kansa ya cire rigar bachin dake jikinta ya cire tasa ya kunna shower ya tara jikinta sai ya tsaya daga bayanta ya saka hannayensa a gaba a karkashin cikinta ya daga mata cikin yayi sama sai ya lumshe ido tana jin kamar babu cikin ma gaba daya a jikinta nauyin cikin ya cire lamo ta yi a jikinsa ruwan dake sauka a saman kansa suna saukowa a kanta, kuzarin da ta rasa sai ta ji ya dawo har bachi ya fara daukarta a haka.
“My guideline”
Ta bude idon a hankali.
“Bachi zaki ki yi?”
Ta daga masa kai tana kara kwantawa a kirjinsa. Ya kashe shower ya dauko tawul ya daura mata ya daura ya riko hannunta suka fito saman gado ya kwantar da ita sai ta bata masa fuska domin ta san ba lallai ne ta iya bachin ma.
“Shiiiiiiiiii zaki yi bachi yanzu nan?”
“How?”
“Ina zuwa”
Wani lotion ya dauko ya matsa a hannunsa ya fara shafa mata a kafarta tana mata massage a hankali, a duk time din da yayi rubbing kafarta sai ya sumbance feet dinta har ya gama ya bude drawer ya dauko karamin cup din honey ya aje kusa sannan ya hau saman gadon ya ya fara bin jikinta yana shafa mata cikin siga mai dadi da kwantar da hankali.
“Kina bukatar cin wani abu? Kin ga ki amayar da komai”
“Aa bana so”
“Please ko kadan ne”
Kamar zata fashe masa da kuka ta ce.
“Ka daina min magiya bana so mana”
“Na daina, I'm sorry”
Ya sumbanci goshinta, sannan ya dagata ya jingina da gadon ita kuma ya kwanta jikinsa zumar ya dauka ya bude yana saka yatsansa ya lakato ya kai mata a baki.
“Bana so na ce bana son komai ba”
Da sauri ya janye hannunsa, domin ko kadan baya son bacin ranta a yanzu, ba dan tana da cikinsa sai dan hallayarta da dabi'un gashi ya sameta cikakkiyar mace, ba kamr yadda yake tunanin duk budurwa ta ta wuce 20 ba za a samu samu budurci a tare da ita ba, amman abun ya canja tunaninsa kuma ya tabbatar masa har gobe akwai na kwarai, and Humairah mace ce mai yawan dora shi a hanyar kwarai, tana nuna masa kulawa yadda yake son samu a mace, a yanzu kam ya yarda idan Allah ya hana ka wani abun zai baka wanda ya fishi ko ba komai Humairah cikakkiyar mace ce mai wayo da kaifin basira. Samun cikin da ta yi kuma sai ji a duniyar babu abun da ya fi masa wannan farincikin, be taba sanin dadin da ake ji idan aka taka matakin zama uba ba sai da matarsa ta samu ciki, wani lokaci haka zai zuba mata ido yayi ta kallonta irin he can't believe cikinsa ne a jikinta ya kamanin yarsa ko dansa zai kasance abun da ya yake yawan ayyanawa a ransa.
Digon zumar da ya sauka a bakinta ta lashe sai ta dan karkato ta kalleshi.
“Hubby”
“Hummm me kike so?”
“Zan sha zumar”
“I knew it ke da kike sarkin kwadayi, kuma zuma tana kara lafiya sosai fa”
Ya sake daukowa ta bude baki idan ya lakato sai ya saka mata har sai ta tsotse yatsansa sannan ya cire ya sake sakawa haka yayi ta mata har ta yi bachi. Sai ya zare yatsan a hankali ya saka tissue ya goge mata bakinta inda ba zai fita ba ya lakata yawunsa ya shafa ya gyara mata bakin sannan ya rufe zumar ya mika hannunsa ya aje ya dauki remote ya kashe wutar dakin, haka suka kwana daga ita har shi ba su farka ba sai da asuba shi yana jingine da gadon ita kuma yana kwance a kirjinsa.
Suna gama sallah ya cire hijab dinta ta aje, ya san yadda take matukar son kamshinsa dan haka ya dauko rigarsa mai maballai ya saka mata, babban riga ce sai ta dan sauko mata cikin kayanta ya duba ya dauko short ya saka mata wanda ya tsaya iya guiwarta ya saka mata hulla sannan ya zaunar da ita saman gadon ya durkusa kasa ya kama hannayenta ya rike.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.