Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 36 of 227

16

WAIRA POV.

Yanayin iskar dake shiga da fita hancinta ba irin wanda ta saba shaka ba ne, yanayin hasken dakin da gininsa kadai ya sanar mata ta baro duniyarta. A ina take? Shi ne abun da ya fara zuwa ranta, daki ne yalwatacce irin na marasa lafiya, an saka labule a inda take kwance an mata shinke da wadanda ke gefenta. Yanayiyar da take ji ke sanar da ita cewar ba ita kadai ce a cikin dakin ba, tunanin dalilin zuwanta gurin take tana son ayyana cewar mutuwa ta yi ko kuma a wani gurin take na dabam. Ta dago hannunta da sauri ta kalli inda macijin ya cijeta sai ta ga an nada mata wani farin abu an daure hannun, ga wani karfe a gefen hannunta na hagu da aka rataye wata jakar leda da bata san na minene ba, zabura tayi ta tashi zaune jin kamar akwai abu a hannunta ya saka ta duba hannu sai ta samu an daura mata wani karamin abu an saka wata yar fata an danne. Idonta ta dora a gurinta tana dubawa a iya zurfin tunaninta jininta ne ake sha ko kuma aka sha. Da sauri ta sauko saman gadon na Asibiti jin kamar ta taka ruwa ya saka saurin duba kasa, wani farin abu ne a kasan mai sulbi sai sanyi yake, ta koma saman gadon da sauri ta rumgume kanta tana jin wani sabon hawaye na cika idonta, tsoro ya gama cika zuciyarta ya bayyana a jikinta, domin ko wane bangare na jikinta sai da ya amsa. Hannu ta saka a jikin kayanta sai ta ji aljihunta wayan babu komai, da sauri ta kai hannu ta taba kanta nan ma babu komai, hannun mai lafiya ta saka ta dafe kanta ta kwala wani uban ihu, duk wanda ke Ward din sai da ya tsorata, Nurse din da suke duty da ranar suka iso kanta da gudunsu.

“Lafiya miya same ki?”

Ganin dukansu sun saka tufafi kala daya ya tsorata, ba zata ce ba mutane ba, domin suna da duk wani abu da take da shi sai dai tufafin jikinsu da yarensu ya banbanta da nata. One after the other ta rika binsu tana kallonsu so take ta ga fuskar wanda ta sani amman ina, babu fuskar da ta sani a cikinsu, gashi ta kasa fahimtar yaren da suke mata. Dayar dake sanye da safar hannu ta kai hannu ta taba hannunta sai ta yi saurin buge mata hannun ta kara matsawa baya.
Kamar kurma haka ta zame musu, bata aikin komai sai hawaye tana kara matse jikinta da ginin dake bayanta, gaba daya ji take duniyar ta juye mata upside down, ta kasa gane a ina take da su wa take? Waya kawo ta a nan duk bata sani ba, idan ma ta sani me zata yi? Komawa a garin nan ta san ba zai yiyu ba, haka zama a inda macijin ya cijeta ma ba zai wadata da komai ba, sai dai abun da bata fahimta ba, wanda ya kawo ta nan me zai mata? Me yake nema a gareta.?
Wani namijin ne na dabam ya zo dubata, sai dai shi baya sanye da kalar tufafin dake jikin mata, nasa tufafin kala dabam ya dora wata farar riga sama. Hannu kawai ya kai ya taba kafarta sai ta ji tsikar jikinta ta tashi,  kallonsa take a fuska be mata kama da wanda ta sani ba, sai dai jikinta na bata taba sanin mutumen da bata san waye ne ba, ko kuma ta taba ganinsa ko kasancewar tare da shi sai dai ta kasa tuna a ina balle ta san waye shi. Shi kam be ce mata uffan ba ba kamar sauran matan dake ta damunta da magana ba, su ma da suke masa magana be amsa musu ba, sai hannunsa da ya saka aljihu ya ciro Apply ya mika mata ganin ta ki karba sai ya aje a saman gadon ya kai hannunsa jikin fuskarta ya share mata hawayen da suka zubo mata, nasa idon na cika da kwalla, da sauri ta kai hannunta zata dafa shi sai yayi saurin dauke hannun kamar ya san abun da take nufin aikatawa. Ba tare da yayi magana ba ya fice daga gurin Nurses din dake tsaye sai mamaki suke, ganin be fadi komai ba be kuma dubata yadda ya dace ba yayi tafiyarsa. Ganin ta ki magana sai kuka take ya saka suka tunanin bata iya magana, tunanin bata jin yarensu be zo musu a rai ba, domin wasu ma sun dora mata hauka ganin tufafin dake jikinta ga kuma tarin dattin daya boye ainahin kyaunta.

Tun suna mata magana cikin dadi rai har suka gaji suka tafi suka kyaleta, daman irin Asibitin nan ce ta Gobnati ta marasa galihu da ba a ciki kula da mutum kamar babbar Asibiti ba, ko kuma Private Hospital, bata kallon ko'ina a yanzu sai kasa Tile din dake kasa take son tantance minene a gurin da yake sanyi dazun data taka, komai ya zame mata kamar mafarki, wacan rayuwar ta garinsu take jin tana marmari sai dai babu halin komawa a yanzu. Jin yan hanjinta na kukan sanar mata neman agajiya ya saka ta dauki Apple din da ya aje a gurin ta kai bakinta ta gutsura ta ci, tsoro baya bari ta tauna yadda ya kamata idan ta saka shi a bakinta ta raba shi biyu ko uku sai ta hade, da haka har ta cinye, sauka ta yi a hankali sai ta sake jin irin sanyi dazun hakan ya saka ta komawa saman gadon ba shiri, sai ta takure kanta ta fashe da kuka. Hankalinta be kara tashi ba sai da ta ga shigowar wasu mutanen na dabam ba na dazun ba, ba kuma wadanda ta taba gani ba, wadannan sanye suke da bakin kaya gaba daya jikinsu.
  A nan ta gane kowa ya banbanta, sai dai bata iya gane akida ko al'adar kowa balle ta iya fahimtar ko tufafin jikinsu suna walkiltarsu ne, wadanda suka zo yanzu kuma saka ta suka yi gaba da tambayoyi kala kala, suna rike da abun abun rubutunsu, kamin Likitoci uku su sake ziyarta ciki har da wanda ya zo dazun be mata magana ba, sai gashi shi ma yana mata tambayoyin da bata fahimcin yaren ba balle ta bada amsa. Ruwa a gorar dayan dan sanda dake sanye da bakin tufafi ya mika mata tare da abincin a takeway, ta sani tana bukatar ruwa sai dai tsoronsu da rashin sanin waye su mutanen ya saka ta kasa mika hannu ta karba, Apple din da likitan ya aje mata dazun ma bata taba ba, cikinsu kuma babu wanda ya damu ya tambaya waya bata apple din. A kokarinsa na burgeta ya bude abincin dake cikin robar takeaway, dafadukar shimkafa  ce da cinyar kaza. Sam bata gane cewa shimkafa ce ba domin am sarrafa ta ba a babin da ta sani ko ta taba gani ba. Hawaye ke mata zuba kamar an bude karamin fonfo tsoron take gashi ta rasa gane yaren da suke magana da ita, ga mutanen sun kashi har kashi kashi kowa tufafinsa dabam, wani abun da ya bata tsoro kuma yadda suka tsareta wasu na kallonta wasu na damunta da magana wasu na rubutu, hankalinta be kara tashi ba sai da dayan likitan ya miko hannnunsa ya riko hannunta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.