Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 86 of 227
“Sulen...”
Ta kamin ta bar gurin ta nufi kofar dakin ta bude, kamar zata tashi sama haka ta sauko downstairs tana wani tsalle kai ka ce kafafuwanta cirewa za su yi, Maleek dake zaune yana a falon ya bita da ido kamar yace mata lafiya, sai kuma ya ji ba zai iya ba, ta bude kofar falon da karfi ta nufi inda aka faka motar tana kiran sunansa tare da tuna mata da sunan da yake kiranta.
“Sulem... Sulem...Sulem... Babe Girl.. Babe Girl...”
Namra ta juyo tana kallonta, shi ma kallonta inda ake kiran sunansa a birjice yake yana ganin Waira ta ware hannayensa ta iso gareshi da gudu ta daka wani uban tsalle ta fada jikinsa ya rumgumeta....
Waira na barin gurin Ummi ta juyo da sauri tana kallonta jin ta ambaci sunan da take yawan kira a gidan, kamin ta runtse ido tana gani abun kamar almara! Kama ce ko kuma shi din ne? Ko jininsa?
“Ummi me kuka cewa Ameer?”
Ummi ta bude idonta dake cike da tashin hankali ta kalli Nimra dake tsaye hawaye shar a idonta.
“Ba mu ce masa komai ba”
Ummi ta amsa mata cike da nauyin baki, Nimra ta saka hannu ta share hawayen dake taba mata baki.
“Ummi kun cilasta shi fada min cewar shi ba da gaske yake so na ba, kuna tunanin hakan zai saka na daina sonsa? Kuna tunanin hakan zai saka na fasa abun da na yi niya?”
“Ba mu fada masa komai ba Nimra, wata kila Allah ne ya dube ki ya kawo miki abun ta sauki”
“Idan ke baki yi ba, to Abiey yayi, miyasa za ku min haka Ummi? Ba ku son farinciki ne? Me na yi muku? Me Ameer ya tare muku? Ummi ko da zaku yanka ni ku cinye nama ba zan daina son Ameer ba, kuma ba zan fasa aurensa kamar yadda nake da niya ba, ko kun daura min aure da wani ba zan zauna ba, kun san fi kowa sanin addini ya hana auren dole, hakkin da nake da shi akanku ne ku aura min wanda nake so”
“Enough Nimra....! Mind you ina lallabaki ina daga miki kafa ne saboda kar damuwar ta yi miki yawa, amman ba kiji na fada miki ba zaki auri Ameer ba, ko da kuwa shi kadai ya rage a duniyar nan, ko zaki gudu ki tafi wani gurin idan ma wannan ne abun da kike da kuduri har yanzu to ki daina, gurin kowa zaki je ko ki kai kararmu ba za ki auri Ameer ba”
“Saboda me?”
Nimra ta tambaya a tsawace sai Ummi ta daka mata tsawa.
“Saboda Addinin Musulunci ya haramta aure a tsakaninku”
“Ta ina? Ummi kin san me kike fada kuwa? Ameer fa musulmi ne, ba kafiri ba. Duk wank abun da zaki fada ba zai hana aure a tsakanina da shi ba, matukar ba gawata kike son gani ba.”
“Saboda Nonon da Ameer ya sha ya saki shi kika kama kika sha har na yayeki, yadda aure yake haram a tsakaninki da Maleek haka ya haramta tsakaninki da Ameer”
Nimra ta yi murmushin takaici, abun is some how amman ta san wannan duk shiri ne
“Ta nan kuma kuka bullo...?”
Ummi ta dauke ta da mari.
“This is Reality Nimra ki dawo hayyacinki... Wai so kuke ku haukata ni?”
Ta fashe da kuka.... Nimra kuma ta dafe kunci tana kallon Ummi...
[6/17, 10:57 PM] My S Line: *Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
36
Kallon da ya fi kama da na ga mahaukaci Namra ta fara yi mata ganin ta zo a guje ta rumgume mata bako.
“Yarinyar nan fa bata da hankali”
Ta fada ta karasa inda suke zata janyo Waira da kafafuwanta ke lake da na bakonta sai Shuraim ya ja baya ya girgiza mata kai yana murmushi kana ganin fuskarsa ka san farinciki a ciki shimfide. Waira ta dago ta kalleta sai ta saka hannunta ya shafa fuskarsa ta ja kumatunsa har sai da ya kyalkyale da dariya mai sauti, ita ma ta fashe da dariyar ta kara rumgume shi kam kam kamar za a kwace mata shi, ta kasa yarda Shuraim din ta ne, mutumen da bata taba tunanin zata sake ganinsa ba a rayuwarta, mafarkin be taba kawo mata zai dawo gareta ba.
“Baby Girl”
Namra ta kalleshi da yanayin mamakin da kuma kufula da kishi a lokaci daya na rumgumar wata macen da bata san alakarsu ba. A zatonta ita yake kira shi kuma da Waira yake ita ma Waira ta san da ita yake domin a zatonta ita kadai ce yake cewa Baby girl. Ta sauke kafafuwanta ta sauko tana rike da hannunsa dayan hannunta kuma tana nuna masa zoben dake wuyanta.
“Sulem... Your ring”
Ta saka hannu ta rika zoben yana dubawa fuskarsa dauke da murmushi. Hakan yayi daidai ta fitowar abokinsa dake cikin motar ya nufo su yana murmushi with confused a the same time.
“Ban taba tunanin zan sake haduwa dake ba, lokuta da dama ina tunaninki na ce yanzu ko ina yarinyar nan take, tana raye ko mace ko wani abun ya same ta, wata kila saboda hankalina ya kara kwanciya Allah ya sake hada mu so that na ga yadda kike rayuwa”
Maganar yake kallon idonta masu matukar daukar hankali.
“Sulem.... Ina son Sulem.... So much so much”
Tana fada tana juya kai wani kalar farinciki da nishadi ne a zuciyarta da baya misaltuwa. Shuraim ya saka hannu ya taba fuskarta gaba daya ta bata masa da masoyiyarsa Namra dake gurin farincikin sake ganinta ya mantar da shi cewar shi suriki ne a gidan.
“Kin yi kyau sosai, kin canja Waira kamar bake ba”
Ta yi murmushi ta sake rumgumeshi, a nan ya dago sai suka yi ido hudu da Namra da fuskarta ke hade sai ya dan rage murmushin da yake yaja baya ta cire jikinsa daga Waira, abun ka da mai dauki sai ta kama hannunsa ta saka cikin nata ta sarkafe.
“Waira”
Ta juyo jin an kira sunanta a tsawace ta kalli saitin katon windows din falon Ummi da aka bude ta kalli Maleek dake tsaye.
“Shigo ciki...”
“Sulem ne...”
Sanin kamar ba zai maimaita mata furucin ba ya saka ta saki hannun Shuraim idonta na cika da kwalla.
“Sulem karka tafi...”
Shuraim da abokinsa sun dauke idonsu daga kallon Maleek, Shuraim ya kalli Waira yayi mata murmushi.
“Ba yanzu zan tafi ba, idan kuma zan tafi zan miki magana je ana kiranki”
“Aa ka zauna duka a nan please Sulem...”
“Shuraim...”
Ya gyara mata, a kokarinta na gyarawar sai ta sake furta sunan a yadda take fada.
“Sulem....”
Yadda ta kira sunan ma ya masa dadi, sai kawai yayi murmushi ya kalli Namra da har lokacin ta saka sakim fuska.
“She's my patient”
“Just...”
Ta tabe baki tana yatsina fuska kamar ta ga abun kazanta. Murmushi kawai yayi ya duba agogon hannunsa kamin ya kalli abokinsa da shi mamakin yake ya ce.
“Ma maybe ka manta ta amman na sha baka labarinta”
Abokin ya dan yi murmushi be ce komai ba sai kallon fuskar Namra yake yana karantarta. Ba dan kar yace ta wulakanta shi ba da a gurin zata barshi tsaye, for which reason zai rumgume wata a gabanta, at first ma ta dauka wata alaka can sai bayan sun gama murzar juna zai ba fada mata cewar patient dinsa ce.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.