Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 39 of 227

“Yarinyar fa ina tunanin kamar bata da hankali, tun jiya bata barin kowa ya taba ta kuma ta koma karkashin Bed din sai kuka take Halima tace min ko bachi bata yi sai ta leko sai ta koma ta boya”

Shiga yayi ya leka karkashin gadon sai ya hangota ta cunkushe guri daya ta rumgume hannunta mai ciwo. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya kunna flashlight dinsa ya haska ta sai ta yi saurin rufe idonta domin hasken yayi mata yawa, tun da take a rayuwarta bata taba ganin hasken gulub ko na fitilar hannu ba, iyakar su hasken aci balbal ko na wutar itace ko ta kara. Nurse din zata yi magana sai ya daga mata hannu ya kashe fitilar ya mika mata hannunsa.

“Baby girl zo nan”

Kin kallonsa ta yi balle ma ta mika masa hannun, mikewa yayi tsaye ya ciro kudi aljihunsa ya fita daga gurin ya aiki daya daga cikin masu sharar gurin ta siyo masa apple da ruwa.

“Tun jiya bata ci abinci ba, kuma aka rasa wanda zai kula da haka?”

“An kula fa masu jinya sun bata abinci ko dazun, amman ba ta ci ba ruwan kawai ta sha, kuma ta ki fitowa a kasan gadon”

“Police din jiya ba su dawo ba?”

“Bana jin sun dawo, shi ma wanda aka bari nan ba a nan ya kwana ba kuma be dawo ba, da sun dawo da mun samu labari kuma babu wanda ya zo dubata, ni ina ganin kamata yayi ace sun dauki hotonta sun saka a Internet ko Allah zai saka a dace da yan'uwanta”

Dr Shuraim dai be sake cewa komai ba, ya cigaba da duba masara lafiyar da suke gabanta, har sai ya gama sannan ya karbi aikan da yayi ma mai share sharen Asibitin, son ganin yadda zata kaya ya saka suka biyo bayansa har da wace ya aikan. Dukawa yayi ya lekata tana ganin fuskarsa sai ta yi saurin rufe ido. Sabuwar takardar ya karba ya dora mata apple din akai ya tura mata, sannan ya aje ruwa ya dauke kansa. Be yi zaton zata yi saurin aminta ta taba ba, sai gata ta miko hannu ta dauki Apple daya, ta fara ci da sauri, ko tsayawa bata yi ta tauna da shi da kyau take hadewa tsabar yunwar da take ji, ta sake miko hannu ta dauki na biyu ta cinye ta dauki na uku har ta cinye Apple din guda uku sannan ta miko hannu ta dauko gorar ruwan, murda ta yi sai ta ji mabudin da karfi ba kamar na dazun da aka bata ba, hakan ya saka ta turo gorar waje, Dr na ganin haka sai ya dauki gorar ya bude mata ya sake ajewa, sai gashi ta ziro hannu ta dauka ta sha ta turo masa rabi. A nan ya lekata sai ta sako masa ido tana jin sake jiki da shi ba kamar sauran da take ganinsu kamar dodo ba.

“Baby Girl zo nan”

Ya mika mata hannu, kalmar Baby Girl ya zauna a kanta, tun a jiya da ya furta mata ba kalmar kawai ba, har da wasu maganganu da aka yi ta dauki wadanda ake yawan furtawa duk kuwa da kasancewar bata san ma'anarsu ba. Kallon hannunsa dake sanye da safa take kamar mai tunanin zuwa, ganin hakan ya saka ya dawo ta hannu ya cire safa daman ba a san likita da kyama ba, ya sake mika mata hannu, ta dade tana kallon hannun kamin ta yarda ta mika masa nata, tana sai ya riko hannun ya janyota alamar yana son ta fito, tana ganin haka ta yi saurin sakin hannunsa, be gaji ba ya sake mika mata hannun yana furta mata sunan da yake son ta saba da shi, wannan karon buge masa hannun ta yi domin ta sanar da shi cewar ba zata fito ba, murmushi ya sake mika mata hannu a karo na uku.

“Baby girl”

Ta miko masa hannun ta kama hannunsa ya janyota sai ta somawa fitowa a hankali, tana lekowa ta ga ba shi kadai ba ta yi saurin komawa. Juyawa yayi ya kallesu

“Kun tsoratata”

Fita suka yi daga gurin suka ja mata curtains din suka labe suna lekonta.

“Baby girl...”

Ya fada bayan ya mika mata hannu, sai ta buge masa hannu a karo na biyu. Lekawa yayi ya ga irin zaman da tayi sannan ya daga kansa ya saka hannunsa yana tafiya da yatsunsa kamar tafiyar mutun kamin ya kai inda take sai ta buge masa hannu. Lekawa yayi mata fuska sannan ya mika hannunsa ya rama bugun da tayi masa a hankali, sannan ya janye hannun da sauri, kamin ya sake mikawa ta sake bugewa, haka suka yi har sau biyar sannan ta yarda ta rike hannunsa ta leko kamar wata bera ta kalli gurin ganin babu kowa ba kamar dazun ba ya saka ta fito gaba daya taba kallonsa da idonta kamar za su masa magana. Saurin kawarda idonta yayi daga barin kallon rabin kirjinta da ke waje, zagen dake kan gadon na asibiti ya dauka zai nada mata a jikinsa sai ta buge zanen, ganin hakan ya saka ba tare da kyamar komai ba ya cire lab coat din dake jikinsa ya saka mata sannan ya fara kokarin mikewa da ita tsaye a nan wata sabuwar rigimar ta bullo ita san ba zata mike tsayewa, ganin take kamar wani abun zai mata, har sai da ya kama rigar ya fara saka mata button din da karfi, sannan ta kalli rigar da take jikinta ba wannan karo na farko data saka rigar data rufe jikinta har guiwarta ba domin tana saka gown da take a cikin tufafin kala uku da suke duniya, abun da bata taba ba shi ne saka tufafin da engine ya saka har aka saka wani anini a jiki. Kallon rigar take sosai kamin ta kalleshi idonta sun yi zurun zurun irin na wandanda yunwa ta samu sa'arsu ta yi musu kamun kazar kuku, ga dan karen tsoron dake fuskarta kamar yayi magana. Murmushi ya saka mata a kokarinsa an kwantar mata da hankali da kuma sakawa ta aminta da shi.

“Ya akai tufafinta sika yage?”

Ya tambaya domin ya san suna bayan curtains din a boye suna lekenta.

“Dazun da Doctor Mu'azu yace a fito da ita ayi mata allura saboda ko an bata maganin ba zata sha ba, shi ne ta yi ta kokawa da mutane har ta barka kayan”

Kamar ance mata kamata za su yi sai ta juya da sauri zata koma kasan gadon hanzarin riketa Dr Shuraim yayi sai ta juyo ta rumgume kam tana kuka jikinta ko'ina rawa yake, ba a taba mata daukar karfe aka soka mata a jiki ba sai wannan karon da ta samu kanta a duniyar da bata san kowa ba kuma kowa be santa ba, yadda ta kamkame shi ko kwakkwaran motsi kasa yi yayi. Hankalinta be kara tashi ba sai da Police din da aka bari ya tsareta ya leko dakin da uniform dinsa wannan karon bakin wando ne da riga sky blue a jikinsa, a nan ta kwala wani irin kara da siririyar muryarta irin karar nan dake shiga cikin kunne ta hana kwakwalwa kwanciyar hankali da sukuni, har sai da Dr Shuraim ya rufe kunnensa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.