Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 67 of 227

“Gaskiya yarda ce kam tun da bata fadawa kowa ba sai ni”

Nimra ta kwantar da kanta jikin Dr zainab.

“Ta ba ni tausayi”

“Darasi ne agareku ku da kuke da iyayen a raye, kuma suka dage suka ba ku gata da tarbiya daidai gwargwado, sai ku bisu da addu'a kuma ku cigaba da yi ma Allah godiya kuna musu biyayya”

Maganar da Dr Zainab ta yi ta soki Nimra, sai ta yi shiru kamar ruwa ya ci tana kallon wani gurin na dabam har sai da Jabir ya fice sannan ta tashi zaune tace.

“Mommy akwai maganar da nake son na yi da ke, amman ba yanzu ba sai mum kebe saboda magana ce mai girma, but ke kadai zaki iya taimako a nan saboda Abiey yana jin maganarki kuma zaki iya tankwara Ummi ta aminta ma”

Dr Zainab ta kalleta da duba da babu wasa a cikinsa.

“Wace magana ce?”

“Akan wani ne, kusan dai zan iya cewa maganar aurena ne, amman dai sai kin kara hutawa zuwa gobe ko jibi zai mu yi maganar, amman for now karki fadawa kowa mun yi maganar wannan sirrinmu ne”

Dr Zainab ta gyada mata kai cike da jindadi daman kullum burinta ta ga sukana dan'uwanta, kusan ta fi kowa damuwa da rashin auren da kowa be yi ba a cikinsu tun daga kan Maleek da be son zancen aure har zuwa Nimra da Namra da suke mata, a take ta ji duk ta matsu goben ta yi fada mata ko minene.

*** *** ***

Waira na tsaye tana kallon barewar dake ta kiwo ita kadai Ummi ta iso gurin rike da tissue ta dafa Waira, sai Waira ta juyo ta kalleta.

“Kin ce kina so na, amman baki taba hira da ni kin fada min damuwarki ba miyasa? Ina yawan tambayar ina iyayenki suke baki fada min ba”

Waira ta sauke ido kasa.

“Waira bata da kowa, Waira bata san Iyayenta ba, Waira bata san waya haife ta ba, Waira bata ga Babanta ba, bata ga Mamanta ba”

Ta fashe da kuka, sai Ummi ta riketa.

“Wani lokacin barin damuwa a cikin rai ba ya maganin komai, ko da yake fitarwa ma bashi magani, sai dai idan ka fada kana jin sanyi, we all have story to tell, kowa yana da damuwa da burin da yake boyewa a zuciyarsa, Waira na miki alkawari, matukar abun da kika fada gaskiya ne, zan rike ki kamar ƴata wata kila saboda haka Allah ya dubi zuciyata ya yafe min son zuciyar da na aikata a baya, ni ma na rasa farinciki kamar dai, ina da damuwa wacce na boyeta a raina na kasa fadawa kowa, sai dai na san hakki ba zai daina bibiyata ba, tarin dukiya da kayan more rayuwa sun yi kadan su manta da ni kuskuren da na aikata a baya, farinciki a zuci yake na rasa nawa”

Hawaye take sosai tana jin kamar ta samu damar fashe ƙurjin da ya nuna yayi mata tuwa a zuciya.

“Wata kila shaidan ne yake ribantata, amman ina jin son ďana a raina, fiye da sauran ina kewarsa sai kace na taba rayuwa mai tsawo da shi, ina son na hada su guri ďaya matsayin yan'uwa, gabar dake tsakaninsa da Maleek ina son ta wuce na rumgume su biyu a lokaci ďaya, ina son kamin na mutu na roki yafiyarsa kamin ranar da Allah zai tsayar da ni ya tambaye miyasa na aikata son zuciya da abun da nake ganin kamar hanya ce mai bullewa, na manta shi ke kashewa ya raya, soyayya ta rufe min ido a wacan lokaci, ni kawai yarinya ce mai wauta da sakarci a wacan lokacin, hakkin Deen da na iyayensa yana kaina, hakkin Ameer yana kai na, ina son na gyara komai kamin ďan lokacin da ya rage min ya kare, ina son na kyautatawa ďana na fada masa irin kaunar da uwarsa take masa, na roki yafiyarsa, so nake na yi masa gata kamin na mutu amman taya.....?”

Ta rumgume Waira tana kuka, Waira ma kukan take duk kuwa da kasancewar bata fahimta takamaiman dalilin daya saka Ummi take kuka sosai haka ba, kuma take kalaman da bata gane manufarsu ba. Rumtse ido ta yi ta dafa hannun Ummi a kokarinta na fahimta abun da Ummi take fada. Duk abun da suke Maleek na tsaye jikin gilashin windows din ďakinsa yana hangesu, sai dai ko za'a kashe shi ba zai iya fadar abun da suke cewa ba, ko kadam be jidadin hango mahaifiyarsa tana kuka sosai ba, wata kila labarin Waira ne ya taba ta, daman ya san ta da rauni, shi ma da yake dakakken ya ji tausayinta balle kuma ita. Ya cire hannunsa ďaya dake cikin aljihu ya saki curtains din.

©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: 28

Ta saki Ummi da sauri ta daga kai ta kalleta, a take ta mance da kalar nata damuwar, tausayin Ummi ya kamata, tsoro da mamaki suka bayyana a fuskarta. Ummi ta yi kasa ta zauna tana kukan data kasa controlling din kanta, Waira ta bita suka zauna a gurin sai dai ita ba kuka take a yanzu ba, mamaki ne ya kusan kasheta da kuma tausayi. Ganin dukansu jiran mutuwa suke yi. Ummi da ta zo da tissue da sunan ta sharewa Waira shawaye sai gashi  Waira ta dauko tissue tana sharewa Ummi hawayenta. Cikin karfin hali Ummi ta yi murmushi ta karbi tissue ta share hawayenta, sannan ta mike tsaye Waira ma ta tashi tana kallon Ummi da wani irin kallo da take jin kamar ace yana iko da damar yaye mata damuwarta ta kawar mata da komai, domin ta rike ta kamar yarta bata taba nuna mata kyama ko hantara a iya zamanta a gidan ba, tana ganinta a ciki yanayi na damuwa sai dai ba ko yaushe ba, domin tana kokarin boyewa saboda yayanta da mijinta, hakan ya saka bata taba kokarin netso ta shiga duniyar tunaninta ta hango rayuwar da take boyewa a cikin ranta ba.

“Ummi... Waira tana tana son Ummi”

Ta fada tana kallonta, wani sabon babin kallon tausayi ta budewa Ummi da zarar ta kalleta sai ta hango abun da ta gani daga rayuwarta. Ummi ta rike fuskarta tana dariya.

“Ummi ma tana son Waira, amman ba haka ake cewa ba, kin kasa iya hausa daidai har yanzu, saboda baki bude baki ki yi magana idan ana hira, cewa zaki yi Ummi ina sonki fadi na ji”

“Ummi ina sonki...”

“Yauwa Yata yar albarka”

Ummi ta rumgume ta tana murmushin da kusan ya zame mata a dole a kowa ne wuni da dare, domin mutane suna ganin zahirinta ne baďininta kuma ita kadai ta san abun da take ciki. Sun dade a haka sannan ta riko hannunta suka dawo cikin falon. Yammaci ranar har dare Waira kusa da Ummi ta rayu kamar yadda ta saba wai dai wannan ya kusanci ya fi na baya, ko ina Ummi ta motsa idon Waira na kanta. Dr Zainab suka tattauna maganar yadda Ummi take ganin ya dace da Waira sai dai bata yanke hukunci ba har sai ta ji daga bakin mijinta. Bayan Sallah Isha'i aka sake gabatar musu da abincin da Hanne ta girka, Ummi kuma ta damawa Waira madara da kankara kamar yadda ta saba mata a kowane dare. Tana gama sha ta kwanta akan doguwar kujerar tare da yin matashin kai da cinyar Ummi, Dr Zainab ce ta sauko sanye da gown marar nauyi sai hula a kanta tana rike da wayarta, Juwairiyyya da Yesmin suna dakin Nimra tare da yar'uwarta suna ta hira, Mahmood kuma ya fita tare da Jabir da dan lukuti wato Umar, Maleek ne kawai a Falon sai Ummi da suke kallon wani documentary da ake a Al Jazeera, Hanne ma ta shige BQ bayan gama aikinta a bangaren Ummi domin babu abun da ta rasa a sashenta sai dai kadaici da take fama da shi wani lokaci, kasancewar bata tare da kowa sai ita kadai kanta, da kuma karamin tv da Abiey ya saka mata da startime ta kama channel din da take so a ko wane lokaci. Ummi da Maleek ne kawai ke kallon sai kuma Gwaggon su Maleek wacce ta sauko a yanzu ta zauna tana latsa waya, Waira kam Ummi ce tv ta, daman can kallo ba burgeta yake ba, farkon fara ganin mutane a tv ya tsorata daga baya ta saba sai dai hakan ba saka ta saki jiki ta dauke shi da muhimmanci ba ko wani abun burgewa ba, har yanzu tana kallon wani abun na rayuwarsu dabam da ya sha banban da nata, akwai abubuwa da yawa da bata waye da su ba a tsawon zamanta a gidan, wasu abubuwan kuma basa burge ta, har gobe tana marmarin rayuwarta ta baya kamar yadda bahaushe ya ce sabo turken wawa. Lokuta da dama Ummi zata shigo falon ta tarar kowa yana zaune yana kallo ko taba waya ita kuma hankalinta yana can wani gurin dabam, ko kuma ta boya a bayan kujera ta kwanta idan bata son zama a cikin mutane, shi ma kuma sai idan Ummi bata kusa kamar idan ta leka bangaren Abiey ko kuma wata fitar ta kama ta, ko kuma tana kitchen tana girki.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.