Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 181 of 227
“Munafurci yayi min kenan? Ya ce wani abu na yi miki? So yake ki tsane ni kenan?”
“I already did...”
Ta fara fashewa da kuka, dauke kai yayi ya fice daga dakin sai ya biyo shi ta fito tana kuka, yana yi yana juyowa ya kalleta ganin da gaske kukan take kuma binsa take ya saka shi tsayawa.
“Me kike so wai? Karki tara min mutane nan fa”
“Ba zan iya kwana ni kadai ba, idan na tafi dakinka ba sai ka kwanta saman gado na kwanta kasa ba?”
“Ba zan yi hakan ba, ki koma dakinki”
Ya fada mata cikin tsawa har sai da ta sha jinin jikinta, ya juya ya fara tafiya kenan Ameer ya kira shi sai ya juyo ya aje mata wayar a kasa.
“Gashi nan ya kiraki”
Ta karasa da sauri ta dauki wayar sai dai bata ganin komai sai fuskarta.
“Ni ce ai babu wanda ya kira”
“Ki taba maballi green”
Yana fada yana tafiya, sai ta taba maballin sai ga fuskar Ameer ta fito yana ganin Nuwaira ce sai ya saki fuska yayi murmushi.
“How are you? Me kike yi ma kuka?”
“Na fadawa Ya Maleek ba zan iya kwana ni kadai ba, yace shi ba zai kwana da ni dakinsa ba, na ce ya kira min kai be yi ba kuma ina jin tsoro”
“Babu abun da zai same ki just ki yi addu'a, tafi ki kwanta yanzu”
“Ni kadai?”
“Ba gani ba? Zan jira sai kin yi bachi kamin kin kwanta zan koya miki addu'ar tsari”
“Ya Maleek ya kawo min wani littafi ma na addu'a wai”
“Yayi kyau, kin ga zaki iya kenan”
Haka yayi ta janta ta hira har ta koma dakin, ya tambayeta an kawo mata abinci ta ce an kawo mata na rana da yamma ma an kawo mata haka after Magariba ma an kawo mata. Wayar ya saka ta aje gurin kan gadonta ta rufe dakin yana hira da ita ta shiga bandaki ta yi fitsari ta fito ta hau saman gadon ta kwanta sai ya saka ta dauko littafi ta bude tana nuna masa ya saka ta karanta inda ya ji ta yi ba daidai ba sai ya gyara mata yana karantawa tana binsa har ta karanta addu'ar kwanciya bachi ta kwana tana kallonsa gaba daya ya gama burgeta domin jin take kamar yana kusa da ita ne.
“Karka kashe wayar Ameer ko da na yi bachi”
“Okay zan yi ta kallonki har ki farka hakan yayi miki?”
Ta daga masa kai.
“Ameer i didn't hate you”
Yayi mata murmushi daman ya san bata tsane shi ba, kawai dai bata mishi irin son da yake mata ne.
“I know, ki yi ta addu'ar da na koya miki har bachi ya dauke ki”
“Okay idan na koma can gobe zan yi missing dinku all”
“Ina fatar dai wani abun da zai same ki ba, kuma ba zaki jefar da addininki ba”
Kamin ta bashi amsa har bachi yayi gaba da ita, daman ga gajiyar mota ga kuma na kukan da ta yi ta rusa dazun. Kallonta yake yana murmushi bachi take amman hakan be rage komai daga kyauta ba. Ya fada mata zai yi gadinta kuma yayi sau biyu tana farkawa cikin dare sai ta ganshi idonsa biyu yana kallonta.
“Ba zaka yi bachi ba”
“Indai zan yi gadinki ki yi naki bachin cikin natsuwa da kwanciyar hankali shi ne farinciki ne, zan yi nawa da rana koma ki kwanta yanzu sallah nafila zan yi”
“Minene Sallah nafila kuma?”
Dare amman hakan be hana shi bude mata wani sashe na karatun Nafila da fa'idarta ba, sannan ya tashi ya shiga bandaki yayi alwala a lokacin duk tana kallonsa har ya fara sallah sannan bachi ya sake yin gaba da ita. Can cikin bachi tana ji yana kiran sunanta a hankali sai ta amsa ba tare da ta tashi ba.
“Tashi asuba ta yi”
“Ina jin bachi ai”
“Haka zaki daure ai, haka muke yi muma tashi ki yi sallah zan tafi masallaci yanzu”
Ta tashi zaune tana murza idon, kamin ta kalli wayar shi kuma yana kallonta a system dinsa ganin yake kamar tana kusa da shi ta cika masa System din kuma wannan ne karon farko da ya raya dare yana kallonta har garin Allah ya waye.
“Thank you Ameer”
“You're welcome ki yi addu'ar farkawa bachi mana”
Ta yi saurin janyo littafin ta bude tana dubawa yana karanta mata har ta biya.
“Good Morning”
“How was your night?”
“Fine”
“You can say Alhamdulillah instead of Fine”
“Okay”
“Good zan tafi masallaci”
Yayi mata sallama sannan ya sauka. Shi kansa bachi yana gadinta a yau ya masa rana domin yayi addu'ar kwanciya bachi a kokarinsa na koya mata, daman ya iya kawai dai ba yayi ne saboda shi dan iskan kansa ne duk wani abu na addini ne dame shi ba a baya, ba kamar yanzu ba da yake ta saituwa a hanya.
Time da aka shigo mata da abun karyawa Maleek ya shigo dakinta, a tunaninsa zai same ta cikin damuwa ko kuka ne sai ya same ta wasai not happy not sad.
“Good Morning”
“How was your night”
“Fine no Alhamdulillah”
Ta fada duk da kasancewar bata gama gwarewa a furta kalmomin larabci ba. Ya mika mata hannusa.
“My phone”
Ta nufi inda wayar take ta dauko ta mika masa.
“Ameer ya tsaya min har safiya”
Be ce mata komai ba ya fice. Sai ten na safe suka gama duk wani shiri na su, a nan hankalin Nuwaira ya kara tashi sanin ta kusa rabuwa da su Ameer da Maleek ko da yake Ameer yayi mata bankwana tun a shekaranjiya jiya kuma ta yi bankwana da Shuraim. Ba ma kamar lokacin da wanda ya san hanyar garin ya iso tare da karin wasu police biyu da za su raka su garin, suka kama hanya suna cikin motar da suka shigo ita da Ameer police din biyu dake cikin shiga ta farin kaya suna a motar Maleek biyun da za su kara musu rakiya suna sanye da uniform su kuma suna a cikin wata motar ta dabam tare da wani dan kusa da garin wanda zai nuna musu garin amman ba zai shiga ciki ba.
Hanyar kawai Nuwaira take kallo bata gane komai ba har sai da suka isa bakin kofar garin sannan ta gane garinsu, domin bata taba fita garin ba, ko a lokacin da ta gudu ba ta hanyar gari ta fita ba. Sai dai abun da ya bata mamakin ganin Eid tare da wata tawaga ta mutanen da ta sani da kuma wadanda bata sani ba tsaye a bakin kofar garin suna jiran isowarta. Dukannin mutanen suna sanye da tufafin garinsu, mazan na sanye da walki matan kuma na sanye da rigar saki wasu kuma suna sanye da warkin skirt da rifar ganye kamar yadda suke yi, wasu kuma riga da skirt din suka na fatu ne. Idonta ya cika da hawaye now she know what she missed ta fita motar zata tafi gurinsu Maleek ya dakatar da ita.
“Ya aka yi suka san zaki zo?”
“Suna da tsafin da za su iya kirana na zo, kamar yadda suka yi yanzu, kuma suna da kalar tsafin da za su iya sanin halin da nake ciki”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.