Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 124 of 227

Ido Ameer ya kura masa yana kallonsa shi ma kallonsa yake da damuwa a fuskarsa.

“Ba wani abun nake son daga gareka ba, ni dai ina son ganin farinciki a fuskarka, ina son na ga kun shirya da mahaifiyarka, ina son na ga ka sadu da dangin mahaifinka da na mahaifiyarka a lokacin da nake raye da idona, domin mutuwa zata iya zuwa min anjima ko yanzu”

“Me da me ta fada maka lokacin da ta zo gidan nan?”

“Bata fada min komai ba, but i see the pain in her face, i read it in her eyes, i hear it in her voice, ta rasa yarta three days ago Ameer, but she still care for you, bayan kuma you're the reason behind her daughter's death, idan ba uwa ba wace mace ce zata so ka? Bayan mutuwar yarta? Kasan wani abun da ya ba ni mamaki? Zuwa ganinka da ta yi, babu wanda ya fada mata kana ciwo, sai alakar dake tsakanin uwa da ďa ita ta sanar mata. Ban ce dole ka yafe mata ba, ban ce dole ka sota ba, amman ina son na roki wannan amfanar a gurinka, dan Allah ka saurareta a duk lokacin da zata zo maka da wani uzuri ko da na magana ne, sannan ba ita kadai ba, Ameer na dade ina fada maka ka bude zuciyarka ka rika damuwa da damuwar wasu, idan wani ya shiga matsala ka rika jin kamar kai ne a ciki, wannan shi ne imani da soyayya ta musulunci. Daga karshe ina son na fada maka, iyaye komai suka aikata mana basa yin laifi, kashe ka kawai za su yi su yi laifi a gurin Allah, bayan Allah da Annabinsa, babu na biyu sai iyaye, da ace na wulakanta iyayena da ban samu kaina a halin da nake ciki a yanzu ba, da rayuwata bata yi albarka kamar haka ba, ni dai kam ina matukar alfaharin da iyaye, ko da kuwa za su siyar da ni a kangin bauta...”

Daddy na kaiwa nan ya mike tsaye yaja kujera baya, ya zagayo ta inda Ameer yake zaune ya dafa shi.

“Shin baka marmarin sanin waye mahaifinka? Su waye yan'uwan mahaifinka? Miye mahaifinka ya yi kamin ya rasu? Miye ma silar mutuwarsa? Baka son saduwa da yan'uwa da danginsa? This is right time da zaka kyautatawa iyayenka ka samu aljannarka cikin sauki, duk wanda zai fada maka wani abu bayan wannan ba masoyinka ba ne, ai yanzu ne lokacin da ya kamata ka yi hanzarin kwace muhallin duka yayan da Zahra take da su a zuciyarta, kai da ka zama ďan gata mai gida biyu iyaye hudu? Baya fika Ameer? Ka ci abinci lafiya...”

Daddy ya karasa yana bubbuga kafadarsa tare da murmushi sannan ya fice daga dinning din. Ameer ya juya yana kallon mahaifinsa sai kuma ya juyo ya kurawa abincin da yake ci ido, kalaman Daddy nata masa yawo a madafar tunanin da nazari, har ya fara tace su yana sakawa a babin lura. Kasa cin abincin yayi tun bayan four spoon da yayi a dazun duk kuwa da irin dadin da abincin yayi da kuma kasancewarsa favorite food dinsa. Tashi yayi ya fito daga bangaren Daddy ya fito waje ya tsaya yana kallon yadda Allah ya kawata saman da tausarari masu kyau da gaske.

Ya dauki tsawon lokaci a gurin sannan ya shiga parlour ya zauna for few minutes, ya tashi ya shiga dakinsa. Miss calls ya tarar kusan 9 daga number Ummi, daman kai ko da ta kira wayar na hannunsa ba zai yi picking ba balle kuma har yayi calling back. Shi be ga reason din da zai saka ta dame shi a yanzu ba, bayan ta kasa bashi kulawa a lokacin da ya fi bukata. Daddy was right idan zai bukaci wani abu a yanzu to tahirin mahaifinsa ne, not her or her family, ba zai son jin haka daga bakinta ba sai dai abu ya zame masa cilas shi ne tambayarta a ina yan'uwan mahaifinsa suke, a gurinsu yake son samun labarin komai ba a bakinta ba. Yana kokarin jifa da wayar akan gado wani kiran ya sake shigowa a take ya danna rejected. Kamin ya aje wayar sako ya shigo masa.

“Waira ce take son magana da kai, ta takura tana son ta tambaye ka wani abu”

Ya karanta sakon, kamin yayi decided zai dauka ko ba zai dauka ba, kiran ya sake shigowa, sai da ta kusa yankewa sannan ya daga ya saka wayar a hands-free, kuma yaki yayi magana har sai da Waira ta fara magana.

“Allo Ammir”

A dayan bangaren sai Ummi ta matso kusa ta karbi wayar ta saka hands-free saboda ta ji muryar ďanta.

“Ya aka yi?”

“Ina ta kira baka daga ba”

“Yanzu na daga ai”

“Baka son magana da ni?”

“Me yasa na daga wayar to?”

“Gashi nan kana bata fuska”

Ta fada ba dan ta ganshi ba, sai dan ta karanci hakan a muryarsa da yadda yake amsa mata. Ya nufi boutique dinsa ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa, da gaske fuskarsa a hade take.

“Zan aje waya sai ka yi far'a sai na sake kira”

Ta fada. Jin haka sai ya saka ya sassauta fuskar yayi ya sauke numfashi.

“Wayar tana kusa da ke ko? Ita tace na ki fada min haka?”

Ummi ta yi saurin girgiza ma Waira kai.

“Aa Ummi tana dakinta”

“Ni na sauko ina falo”

Ya jimmm for some seconds sannan ya ce.

“Me mike son ki tambaye ni?”

“Abubuwa da yawa, na ce Ya Maleek ya kawo ni, sai yayi min ihu wai ba za a sake zuwa ba, kuma idan na sake yin maganarka ma sai ya min duka”

“Saboda shi ubanki ne?”

“Aa shi Ya Maleek ne”

“Baki da alaka da shi ai, ba shi da hujja”

“Shi yaron Ummi ne ai”

“Baki da alaka da Ummi baki da alaka da kowa a gidan nan, so babu wanda zai saka ki dole ko hana ki abun da kike so, idan ma akwai wannan to ni ne, domin ni na dauko ki daga daji, ni ne sikar zuwanki garin nan and that stupid house, remember?”

Ta kalli Ummi sannan ta daga masa kai.

“Yes”

“Good so no one has power over you, tambaye ni abun da kike son ki sani”

Ummi ta yi saurin rada mata a kunne.

“Zaka zo sai na tambaye ka?”

“No”

“Please”

“No”

“Abubuwa da yawa ne, ina son na sani zaka zo saboda ni?”

“Aa”

“Baka damuwa da matsalar kowa kai?”

Yayi shiru, ya saka hannunsa ya taba hancinsa ya runtse ido ya bude.

“Dole sai na zo wai?”

“Eh”

“Zaki iya tambayata a waya”

“Bana so a waya, kai baka da tausayi Ameer ko? Shiyasa ka tafi ka bar ni a lokacin da maciji ya cije ni a daji, ban manta ba i will hate you more”

“Zan zo”

Ya amsa ba tare da shiri ba.

“Yanzu?”

“No”

“Gobe ina zuwa school da safe”

“Zan same ki school din”

“Kasan ina ne?”

“Ki turo min address a waya”

“Okay zan aje waya”

“Good night”

“Good Night”

“Yeah Good Night”

Sai ta sake fada.

“Good night”

“Okay sai da safe”

Sai da ta yanke kiran sannan ya fito daga dakin ya jefar da wayar akan bed, shi yana da alot of questions da zai mata, sai dai hakan ba yana nufi ko da ya tafi ya shiga gidan ba sai dai ya tsaya daga wani gurin ta zo ta same shi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.