Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 116 of 227
“Hello”
Ameer ya fada cikin rashin kuzari murya can kasa. Kai tsaye Abdull ya fada masa dalilin kiran.
“Ameer ka ji kanwar Maleek ta rasu”
Jin an fada masa abun da ya sha gaba komai wato mutuwa ya saka shi zabura ya gyara zama da sauri.
“W-w-w what? Wace wace wace please wace?”
“Nimra, ta rasu da daren nan asibiti”
Ameer ya aje wayar akan center table dake kusa da shi ya dora hannunsa saman kai ya gurfana a kasa kamar mai neman gafara.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Allah ya Abdull how? Why?”
“Why? Mutuwa ai bata da magani, ba kai ka fada min an kaita asibiti ba? Maybe ciwon be barta ba”
Ya girgiza kai ya rufe bakinsa yana kuka.
“Na kasheta Abdull ni ne... Ni ne silar mutuwarta.. Na rabata da duniya... Oh my God yanzu ya zan yi da hakkinta?”
“Ameer lafiya kake kasan me kake fada?”
“I break her heart, na yi ne kawai saboda na bakantawa Maleek, and ba son gaskiya nake mata ba, kuma na fada mata and.... Shi ne silar sumanta har aka kaita asibiti now you're telling me ta mutu, Me yasa abubuwan nan za su zo min a yanzu Abdull I'm such bad person i didn't deserve anything good at all, ina zan roki yafiyarta? Yanzu ya zan yi da hakkinta”
Dauke wuta Abdull domin shi dai ya kira ne kawai ya sanar masa kamar yadda abokinsu Dawood ya sanar musu so that su taru su tafi gurin abokinsu domin jajanta masa kuma ayi komai da su, kamar yadda suna gudanar da al'amurransu a can da, duk kuwa da kasancewar babu wanda ya taba rasa rai a cikinsu sai a yanzu da Maleek ya rasa, sai dai duk abun da ya samu suna taruwa su jajanta ma juna, ba dan ma matsalar da Ameer ya samu da Maleek ba da a kullum tare suke rayuwa.
“Ameer... Kasan me kake fada kuwa? Amman Ameer ya sani? All this fadan da kuka yi har abun ya kai su gurin police iyaye suka shiga abun be tsaya iya nan sai da zuciyarka ta raya maka ka aikata ma yarinyar nan wani abu? Yanzu miye amfanin aikatawar da ka yi? Gashi ka zama silar mutuwarta, innocent live, da ma ace kana sonta da gaske sai abun ya zo da sauki amman kasan baka sonta ka aikata hakan saboda kawai ka cutar da ita? Kana da matsalar rayuwa Ameer, idan ka dauki gaba da mutum kai ala dole sai ka ga bayansa, burinka ka wulakanta kowa cikin har da mu da muke abokanka, kuma babu wanda zai fada maka ta ji wannan ba rayuwa ba ce mun sha nuna maka amman baka ji ba, yanzu kana tunanin hakkin yarinyar nan zai barka? Idan iyayenta suka yi kararka ma za a iya kwatar musu hakkin yarsu, bayan haka kuma ka karawa kanka kiyayyar kanka a gurin Maleek da iyayensa.. Sannan.... ”
Yanke wayar yayi fahimtar Abdull ba zai gaba zuba masa kalaman da suke kona masa rai ba.
“Nimra...”
Ya furta yana hawaye, wayarsa ta sake ringing wannan karon Dawoo ne ya kira shi, wata kila shi ma zai sanar masa an yi mutuwar ne, sai ya ki daga wayar sai hawaye kawai yake, wani rauni da nadama suka mamayeshi. Sai a yanzu yake ganin be kyauta ba, be aikata daidai ba, be dace yayi haka ba, me yasa ya cutar da Nimra? Son zuciya ne ya kai shi ga aikata hakan ko kuma rauninta? Wa gari ya waya yanzu? Gashi Ummi ta fada masa kanwarsa ce, that's mean Ummi ta haife ta kenan? If wani ya aikata wa kanwarsa haka ya zai ji balle kuma ace shi da kanss ya aikata? Ya mike tsaye ya fara safa da marwa a falon, dariyarta ce ta fara fado masa a rai yana tuna yadda take nishadi idan ta zo gidan, saboda tana tunanin son gaskiya ya nuna mata, yadda ta rike hannunsa tana rokon ya rike ta amana ya tsaya mata a duk lokacin da za su tsinci kansu a cikin mawuyacin hali, yadda take yawan fada masa tana kaunarsa ga kuma irin marin da Abiey yayi mata a lokacin da suka zo daukarta restaurant ya tsaya masa a rai, kiran da ta yi masa a waya na karshe har ya fada mata cewar shi baya kaunarta ya hana shi sukuni. Sai da ya kai tsakiyar falon ya fadi durkushe ya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, sosai yake kukan da ace gidan ba babban gida ba ne da makota ma za su iya jiyo muryarsa.
“Nimra ki yafe min.... Ki yafe min Nimra.... Na shiga uku, i hurt this innocent girl, i hurt her hakkinki ba zai bar ni ba, me yasa na aikata? Akan me zan dauki dansa akanta? Meyasa na zama wawa? Why ido zai rufe na kasa ganin abun da zai biyo baya?”
Fada yake da kansa kamin ya daga hannunsa ya dauke fuskarsa mari, ya daga hannayensa ya buga kasa, be taba jin ya cutar da wani cutar da ta kai makura ba irin wannan, sam be dorawa Nimra mutuwa a yanzu ba, shi be ma zaton son da take masa ya kai har haka ba.
“I'm such a bad person”
Ya fada yana jin kamar akwai abun da zai iya yi ya dawo da rayuwar Nimra ya roki gafararta. Tunanin yadda take rayuwa da shi a gidan ya dawo masa komai nata gani yake kamar lokacin yake faruwa, dariyarta ta cika kunnensa. Da sauri ya dauki key din motarsa da wayarsa ya fice daga gidan, sai da yayi kamar ya tafi gida kuma ya ji ba gidan yake bukata ba, kai tsaye gidansu Nimra ya nufa sai ya faka nesa da gidan yana kallon gidan, yadda motoci suke shiga da fita ya tabbatar masa da yarinyar da ya cutar ta bar duniya. Sai da dare yayi sosai ya juyo ya dawo gidan, ban da Mommy babu wanda ya san dawowarsa domin ya dawo a wani yanayi kamar ba shi ba. Dakinsa ya kulle ya rasa abun da zai yi, yadda gidansu Nimra ba a runtsa ba shi ma be yi bachin ba har garin Allah ya waye, washe gari yayi wanka ya shirya tun da wuri ya saka mask da bakin tabarau ya fice daga gidan. Gidansu Nimra ya sake komawa ya tsaya nesa da gidan yana kallon motocin dake shiga da fita, yana a gurin har aka fito da gawarta aka wuce da ita zuwa makabarta domin a cikin gidan aka yi mata Sallah sai da motocin suka yi nisa sannan ya bi bayansu har makabarta ya shiga ya tsaya can wani gefe domin ya san be isa ya taka karasa gurin, gawar Nimra ce first gawar da ya taba rakiya zuwa kabari, shi tun da yake a rayuwarsa be taba zuwa makabarta ba, sai dai ya gani a hoto ko video. Be taba sanin dan'adam ba a bakin komai yake ba sai a yau. Bayan kowa ya tafi sannan ya shiga motarsa ya dawo gida, kamar wanda yayi sata aka kamashi haka ya shigo falon jiki ba kwari zuciya a raunace, ido a kumbure baki a bushe.
“Ameer ga abun karyawarka, kuma mahaifinka ya damu da fitar da ka yi da safe baku ga juna ba, gashi baka dawo gida ba jiya sai da dare ya raba sosai”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.