Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 226 of 227

“Good morning Fam”

Ta yi dariya, shi ma dariyar yayi ya kai bakinsa ya sumbanci katon cikinta sannan ya mike tsaye ya rumgumeta.

“I love you so much Humairah i love you with all my heart”

“I love you too”

“Me kike son ki ci?”

“Something new, kuma ranar nan da ka yi min miya ya kone na ji dadinshi”

“Stew?”

“Yeah ya min dadi ina son ka sake min ya kone”

“Okay akwai shi a fridge ai, zan dora a wuta ya kone”

Ya buge masa hannu jin yana kokarin aika mata da sakon da bata shirya karba a yanzu da safen nan ba.

“To ai ba ki gaishe ni shiyasa”

Sai ta mike tsaye gaba daya, ya saka hannunsa ya kama fuskarta ya hade bakinsu, wani kalar French kiss yake aikata mata in a soft lips, har sai da ta ga yana kokarin fita hayyacinsa sannan ta cire bakinta. Sai ya hade goshinsu numfashinsu ya gauraya yana kallon saman idonta dake rufe hannayensa kuma suka sauka a cikinta.

“I love you”

Ya furta mata murya can kasa. A tare suka shiga kitchen ta hau sama kusada sink ta zauna tana masa hira yana aiki, idan ya biyo ta kusa da ita sai sun sumbanci juna yake kaucewa haka dai har ya gama, sannan ya rikota suka sauko tana tafiya yana bayanta ya saka hannunsa ya tallafo mata cikin.

“Kenan ba yanzu za ayi ba?”

“Har yanzu ai be fito da wadda yake so ba, Maleek yace min tun tasowarsu Mahmood yana da ruwan ido sosai yanzu ma baki ji bakinsa ba duk zai yi magana cewa yake shi ba zai zauna da mace daya ba, shi ba zai dauki halin Abiey ba yayana da yawa yake son haifowa kamar ni”

Bata san lokacin da ta juyo da karfi ta kalleshi ba har sai da yayi mamaki.

“Kamar kai kamar Yaya?”

Ya rufe mata idon data zuba masa.

“Kamar haka”

Ya janye hannun.

“Kai ma aure aure zaka yi?”

“Nooo Yaya nake nufi ina son haihuwa da yawa na tara yara maza da mata”

“Oh na dauka aure da sai na cire maka cikinka na aje”

Be san lokacin da ya fashe da dariya ba.

“Dan Allah cire ki aje, har kyauta sai na miki, see dis Girl ku dai mata baku son kishiya? Allah yace ayi ba kuma kin sani”

“Zaka ba ni abincin na ci ko bata min rai zaka yi?”

Ya sumbanci hancinta da tsakiyar girarta.

“Lemme feed you Babyn baby”

Kujera yaja mata sai da ta fara zaunawa sannan ya zauna ya fara zuba musu abinci yana dariya, domin ya lura da gaske ta dauki zancen da zafi...

One year later......

Katon Event Center ne dake dauke da manyan mutane, decoration din kawai zaka kalla kasan biki na yayan naira. Manyan mata na sanye da ash lace yan mata kuma na sanye wani material mai kyalli maroon color, wasu kuma sun saka choice dinsu domin ba kowa yake son anko ba, musamman manyan mutane, a tsakiyar kuma Amarya da ango ne sanye da farare kaya, ango farar shadda amaryar kuma na sanye da farin yadi ta sha makeup ta rufe kanta da wani mayafin fari mai kyalle wanda ya sauko mata har kasa. Humairah ce tsaye tsakanin Amarya da ango sai watsa musu kudi tana tana dariya tana takawa. Kamin Ameer ya isa gurin rike da dansa Bashir da aka yi ma alkunya da Areef na tsakanin hannunsa da kafadarsa, ya ciro nasa kudin ya fara zubawa Mahmood da Amaryar Fiyya, fiyya ta karkata ta koma gefen Ameer ita da shi suka yi ta rawa jama'a na taba musu shi kansa Mahmood din sai da ya koma yana musu karin kudi, MC sai wasa yayan Amarya yake, Ummi ma tasowa ta yi ta watsa musu kudi tana murmushi, kusan kowa sai da ya taba musu a gurin.
Duk abun da ake Nuwaira na zaune a table dinsu ita da Maleek sai wasa hakora take. Can kuma ta kalleshi ta dago masa hannunta.

“Dan Allah ka cire min robar nan dan Allah Ya Maleek”

“Na cire miki roba ki shiga ki yi rawa?”

“Kadan zan yi?”

“Au ashe ma zaki yi din da gaske, ana kallonki da ciki dako dako ki shiga ki yi rawa saboda idonki ya zare ko?”

“To ina ruwanka cikin naka ne ko nawa?”

“Toh da naki ne? Cikinki ne?”

Ya mike tsaye sai shi na ya mike domin robar da ya saka mata a hannu ita da shi basa iya yin tazara.

“Wai ina ka siyo wannan shegen roban ne?”

“Saboda bikin nan na siyota daman na san cewa zaki yi sai kin yi rawa ai”

“Wallahi yau sai na maka kuka kala kala, idan mun koma gida”

“Ki fara tun a nan ma”

“Ko har nan da shekara biyu ba zan manta ba sai na ta yi maka kuka”

“Lokacin ai kin kara hankali ba zaki yi ba”

“Ya Maleek dan Allah ka bari na yi rawa”

“Ko baki da ciki ni bana sha'awar wannan rayuwar da mata suke zuwa cikin mutane suna rawa da sunan biki, balle kuma kina da cikin nan”

Ta fara masa kukan tun anan domin ta san kukanta a abun da ya fi tsana a yanzu.

“To ina son na musu liki ai”

“Okay cry cry baby mu tafi”

A tare suka jera suna tafiya ya rike hannunta mai robar ya saka yatsansa a cikin nata amman hakan be hana ta tana tafiya tana dan takawa ba, domin kidan dake tashi ko malam sai dai yace babu kyau ba dai ya ce babu dadi ba. Suna iss gurin ya ciro kudi ya mika mata sannan ya saka hannayensa ya zagaye ta zama tsakanin kirjinsa da hannunsa haka take likin har sai da ta gama, sannan ya ciro nasa ya lika musu, Nuwaira sai taka take ba damar ta zake ta yi rawa Maleek ya hanata wali, dukawa ta yi zata fita tsakankanin hanayensa sai ya riko hannunta, ya kai bakinsa kunnenta ya ce.

“Zaki ji ma kanki ciwo ne wannan robar ba zata bari ki tafi ko'ina ba”

Ta kalli robar baka ce mai kamar abun hannu sai wata yar danja ja dake jikinta, ta saka dayan hannun ta murza ta murza.

“Ba zan sake zuwa da kai biki ba Ya Maleek ko na gidanku ne sai dai ka zauna a gida”

Mahmood yayi dariya domin cikin masifa ta yi maganar kuma a bakin gaskiyarta take ba zata sake zuwa da shi biki ba. A yanzu ta gano dalilin da ya saka yace kar ta tafi tare da sauran yan biki ta bari su tafi tare, kuma tun a mota yayi mata wayo ya saka mata robar da sunan ta masoya ce ashe ba haka ba ne. Tana hango Ummi ta nuna masa ita

“Mu tafi gurin Ummi zan yi magana da ita”

“Mu tafi”

Tare suka isa tana isa ta kai bakinta saitin kunnen Ummi ta kai karar Maleek. Ummi ta kalli robar ta kalleshi.

“Cire mata mana haka kawai ka hanata walwala?”

Namra dake tsaye bayan Ummi tana kokarin gogewa yaronta bakin ta saka dariya.

“Gaskiya Ya Maleek kana da matsala, yau din ma da ake bikin dangi ba zaka barta ta wala ba?”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.